Sashe 18
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin tafiyar za ta yi da gaske, hakan yasa hankalina tashi bana so su Abba su ji wani abu, tunda ba iya faÉ—a zan yi ba ko an tambaye ni.
Da sauri na kama ƙafafun ta na durk'usa, tare da fashewa da kuka nace "Dan girman Allah Aunty karki sanarwa su Abba, bana son hankalin su ya tashi dan Allah."
Juyowa tayi ta kama ni ta miƙar, fuskarta ɗauke da yanayin tausayawa, ta sassauta Muryar ta cikin lallashi tace "Haba Rahamah, ya kike so nayi dake to nace ki faɗa min matsalar ki kin ƙi, gwara ki bari na kira su Abba ya fi ko su za su iya sawa ki faɗa."
Kuka na ƙara fashewa dashi, gaba ɗaya ji nake kamar an rufe min baki na kasa faɗar komai, ga maganar ina son yi amma babu hali.
Duk yadda ta dinga lallashina akan na faɗa, ƙi nayi sai kuka da nake ta yi naƙi bari ta tafi.
Ƙarshe ta fusata ta fincike daga riƙon da na mata, tayi tafiyar ta ta barni tace "Ba zan faɗawa kowa ba, tunda haka ki ka zaɓawa kanki, koma me ne in ya dame ki za ki ne me ni, in kuma iskanci ne yasa kike haka sai dai na miki fatan Allah ya shirye ki."
Ina ji ina gani ta tafi, na zube a wajen ina kuka kamar wadda aka ce uwa da ubanta sun mutu.
***
*AUNTY FATI.*
Rai ɓace ta bar gidan Rahamah, bata taɓa jin ɓacin rai irin na yau ba, ace yarinya sai taurin kai da kafiyar tsiya.
A haka ta na mita ta ƙarasa gidan Aunty Zainab.
Ganin ranta a ɓace yasa Aunty Zainab cewa "Ya ya naga kin fita kina sauri, kin dawo ranki a ɓace haka?."
Tsaki Aunty Fati taja ta zauna kan kujerar dake kusa data Aunty Zainab tace "Daga gidan yarinyar nan nake."
Nan ta kwashe komai ta faÉ—awa Aunty Zainab É—in.
Ta gumi kawai Aunty Zainab ta yi, sai da ta gama jin ta tsaf, ta gyara zaman tare da sauke numfashi tace "Gaskiya Fati kema kin yi kuskure tun farko, ya ya yarinya zata ne me ki akan matsalar ta, amma ki kasa yarda da ita.
Ai tun lokacin da ki ka tarda ta a kwance ba lafiya, miji baya kusa da ita babu kulawa cikin ciwo, kawai dan kin ga ya dawo yana nan-nan da ita sai ki ƙi yarda da ƴar uwar ki, shi ki yarda da shi?."
A hankali Aunty Fati ta fara tunani, tabbas gaskiya Aunty Zainab ta faɗa. Bata taɓa tunanin Al'amen zai iya yin fuska biyu ba, sai yanzu da ta tuna mata duba da yadda bai ji kunyar ta ba wajen cewa ta hana Rahamah shan maltina da ƙwai, ga kuma kalmar shi ta ƙarshe wai ta kula da ita kar ta bari wani abu ya samu cikin.
_Tabbas biri ya yi kama da mutum, in kuwa hakane akwai matsala._
Ta faÉ—i hakan a ranta.
Nan Aunty Zainab ta cigaba da magana "Kin ga Fati, duk mutumin da ki ka ga an fiye yabon halayen sa a waje, ki bincika gidan shi ki duba irin zaman da ya ke da iyalin sa, ba duka bane hakan.
Amma yawanci duk masu hali irin na Al'amen, fuska biyu gare su a waje salahai a gida kuma saɓanin haka."
Sauke ajiyar zuciya Aunty Fati tayi, fuskarta cike da jimami tace "Yanzu ya za'a yi? Kin san na baro ta na kuka ne, harda kama ni tayi na ƙwace na taho."
Tsaki Aunty Zainab taja tace "Wallahi kin bani haushi Fati, har wani ɗan iska ya isa na zaɓe shi akan jinina, kin fa san halin ƴar uwar ki ba baki sani ba."
"Uhm Aunty Zainab, ai ni sai yanzu ne ma duk abubuwan ke dawo min, kin san Allah Rahamah bata da matsala, da wuya a mata abu sau ɗaya ta magantu, tana da wani irin haƙuri me wuyar samu a wajen mace.
Sai yanzu nake mamakin yadda take yawan faÉ—ar laifin mijin ta."
Cewar Aunty Fati kenan.
Miƙewa tsaye Aunty Zainab tayi tace "Bari na sako hijabi mu je gidan Rahamar, tunda dama lokacin islamiyya ya yi, sai mu sauke yaran a makaranta mu wuce.
Kafin na fito dai ki kira shi mijin nata a waya, ki ce zamu je gidan shi ya dawo ya same mu, dan in mun haÉ—a su waje É—aya dole su faÉ—i matsalar su, in ita bata faÉ—a ba dole shi zai yi abinda zai tona asirin sa ko yaya ne.
Kin san ni mutum in har bashi da gaskiya, to sai dai bai tsaya gabana ba, amma yana magana nake fahimta.
Dariya Aunty Fati tayi tace "Dama ku lauyoyi, har sai an nuna muku mara gaskiya, sai dai in kunga dama kun ƙyale shi.
Haka kuwa suka yi, Aunty Fati ta koma gida ta shirya yara, suka sauke su a islamiyya da ya ke a motar Aunty Zainab É—in suka fita.
Tuni ta riga da ta kira Al'amen É—in, yace mata yana zuwa.
Bai yi zaton ba ita kaÉ—ai zata zo ba, suna hanya ya bugo mata waya wai ta tsaya a gida ya zo ya É—auke ta.
Nan tace masa su sun kusa ƙarasawa gidan na shi ma.
Aunty Zainab dake tuƙi ta duk tana jin abinda suke cewa, ta juyo ta kalli Aunty Fati tace "Kin ga abinda nake faɗa miki ko? Ki ji tsabar munafurci wai zai zo ɗauke ki, ke da za ki wajen Ƴar uwar ki ya cutar da ita."
Haka suka cigaba da tattauna maganar, har suka kai gidan Rahamah.
A inda Aunty Fati ta bar ni anan suka tarda ni, ganin ta tare da maƙociyar ta Aunty Zainab.
Sai na É—an ji dama-dama, dan matar akwai mutumci da karamci tun ina budurwa, lokaci ina zuwa wajen Aunty Fati muna shiri sosai.
Kama ni ta yi ta miƙar dani tana faɗin "Subhanallahi Rahamah, ya za ki kwanta a ƙasa kina kuka haka? Bayan ba ke kaɗai bace."
FaÉ—awa nayi jikin ta na fashe da kuka, lallashina ta shiga yi taja hannuna muka zauna bakin gado.
A hankali ta shiga jera min tambayoyi cikin lallashi tana shafa kaina, tace min Al'amen É—in shima yace zai zo yanzu.
Jin haka da nayi yasa na É—ago kaina da sauri, cikin kuka nace "In ya zo ku tambaye shi abinda ya min, Ni ba zan iya faÉ—a ba."
Tsawa Aunty Fati ta daka min, ta kalli Aunty Zainab tace "Kin ga abinda ya ke bani haushi da ita ko? Yarinyar nan na da kayan takaici Wallahi."
ÆŠaga mata hannu Aunty Zainab tayi tace "Kin ga Fati, ke matsalar ki sauri fusata, ki kalli yarinyar nan ki duba yadda take cikin damuwa, tabbas akwai abinda ke damun ta faÉ—ar ne ba ta yi ba kawai."
Ta ƙarasa tana bina da kallo cikin nazari.
Babu jimawa sai muka ji ƙarar motar Al'amen, alamar ya dawo kenan. Kiran wayar Aunty Fati ya yi, yace mata ya dawo zai zo yanzu tana ina.
Ce masa ta yi ya zo part É—ina tana nan.
Duka muka fita muka nufi farlona, muna zama babu jimawa sai gashi ya shigo.
Da sauri na sunkuyar da kaina cike da kunya, ganin yanayin shigar dake jikin Al'amen.
Da sauri Aunty Zainab da Aunty Fati suma suka kauda kai, Aunty Zainab da ta kasa shiru tace "Auzubillahi."
Sanye ya ke da gajeren wando, wanda ko cinyar shi bai gama rufewa ba, sai rigar dake hannun shi wadda ya kare iya gaban shi da ita.
Bayan su babu komai a jikin sa, haka ya shigo tiɓi-tiɓi ya nemi kujera ya zauna.
Aunty Zainab da ta kaÉ—u da rashin hankalin daya nuna, kasa daurewa ta yi ta kauda kanta tace "Dan Allah in ba damuwa, ka fara suturta jikin ka kafin mu fara magana.
Dan ko yadda ka shigo nan a haka, ba al'adar mu ta hausawa bace da aka sani da kunya, hakan ba daidai bane ko ba komai mu ma muna da mazaje matan wasu ne."
Ba ƙaramin burgeni na ji Aunty Zainab ta yi ba, haka kawai naji wani daɗi ya kama ni, ko ba komai yau na samu wanda ya iya tsayawa gaban Al'amen ya faɗa masa magana kai tsaye.
"Ku yi haƙuri."
Ita ce kalmar daya iya faÉ—a kenan, ya juya ya fita yana jin haushin Aunty Zainab, dan ya santa, tunda gidan Aunty Fati shi ya raba tsakanin gidan su da nata.
Babbar lauya ce kuma sannaniya, duk faɗin unguwar gidan ta ne kawai basa wani ganin darajar shi daga ita har mijin ta, yaranta kam dama duk basa ƙasar suna Ƙasar waje karatu, dama su biyu ne duka maza.
Haka ya sako riga akan gajeren wandon, ba tare da ya saka dogon wando ba ya zo ya zauna.
Kallon shi Aunty Zainab tayi tace "Al'amen mun zo ne sakamakon kiran da Rahamah ta mana, tace akwai matsala a tsakanin ku, mun tambaye ta bata faÉ—a mana ba, ko kai zaka iya mana bayanin abinda ya haÉ—a ku yau?."
A zabure ya É—ago ya kalle ni, da sauri na É—auke kaina dan ko kallon shi bana son yi yau.
Kame kame ya fara, yana faɗin shi babu abinda ya faru a tsakanin mu, kawai in yace nayi abu ne kai tsaye nake ƙin yi.
Ga rashin kunya da nake masa, bai isa ya min magana ba sai na taso masa.
Ba sai ga mutumin ku ya fara kuka ba, harda su jan majina wai Wallahi shi yana sona, nice dai bana son shi shi yasa har nake masa sharri yana takura min.
Kallon shi kawai nake ina mamakin ganin yadda yake kuka,sai kace ba shine mugun nan ba me duka na.
Ita kanta Aunty Zainab kallon shi take cikin nazari, a nutse ta karance shi tsaf ta gane bai da gaskiya, dole kuma akwai wani abu da ke ɓoye wanda basu sani ba.
Dan haka ta kalle ni a gaban shi tace "Rahamah ina so karki cutar da kanki, in har kin san yana miki wani abu ki fito ki faÉ—a, karki cuci kanki bayan mun tafi ki yi dana sani."