← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 22

Sashe 6

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta juya tana ƙoƙarin rufe ƙofar.
Ganin hakan da ya yi yace "Am Aunty ga wannan a bata dan Allah ."

Ya miƙo ledojin dake riƙe a hannun sa, amsa Aunty Zulai tayi zuciyarta cike da mamakin Halin Al'amen.
A haka kamar me hankali, amma abinda ya yi ya bata mamaki, sai kace an ce masa ba zasu tafi ba zama za su yi.

A haka tana mita ta koma É—akin, har barci ya fara É—auka ta.
Jin yadda take ɓaɓatu akan shirmen Al'amen, yasa na buɗe idona na yunƙura na tashi zaune.
Ta kalle ni tace "Ke fa angon ki ya zo wai na kira ki, ku je ku kwanta dan tsabar wauta."

Dariya ce ta so kamani, ganin yadda ta ke maganar, sai kace irin wanda ya aikata wani gagarumin zunubi É—in nan.
Na fuskanci abin ya mata wani daban, shi yasa take ta maimaita maganar.
Ina shirin komawa na kwanta nace "To ai ni ya fara kira a waya, wai na fito yana waje mu tafi.
Shine fa na kashe wayar, shine ya kira ki kenan."
Na ƙarasa faɗar ina kwantawa cikin dariya.

Ƙoƙarin saka hular dake riƙe a hannun ta take, bayan ta gama sa kaya ta kalle ni taja tsaki tace "Waya sani ko su haka suke abin su, Ni kunga ma ya bani leda wai na kawo miki, bari na buɗe na ga me ye a ciki.

Ta tsugunna ta shiga fito da abubuwan dake cikin ledar. Wasu irin dank'wala-dank'walan kaji ne masu rai da motsi, sun ji gashi sai tururi suke.
Maida kaina nayi na kwantar, ko sha'awa basu bani ba.

"Kunga mutumin nan ko Jamila, wato mu suka haÉ—a da naman kasuwa shi muka iya ci shi yasa aka haÉ—a mu dasu, duk kuÉ—in sa ba zai iya yanka mana ka ji a soya a tarbe mu da su ba. Amma da ya ke yana son cin amarci ai kinga ya siyowa Rahamah."

Dariya Aunty Jamila ta yi tace "Kai aunty Zulai baki da dama Wallahi, to mene dan ya siyowa matar shi, muma ai an sa mana nama a miya munci."

Sai da ta gutsuri naman kazar tasa a baki tace "Ai ba cewa nayi laifi bane Jamila, duk da muma Alhamdulillahi ba wai yunwar naman muke a gidajen mu ba. Amma ga mutum mai arziƙi irin Al'amen ya kamata mu samu tarbar data ɗara wadda aka mana."

"To ina ga su haka suke abin su fa, shi yasa bakya ganin ba Yaren mu É—aya ba."
Cewar Aunty Jamila kenan.

"Dallah rufe min baki, ke baki san me ke tafiya a duniya bane tunda kullum kina gida bakya zagawa, ai ko lokacin da muka zauna a ilori da Dadyn Fadila Wallahi yarabawa suna da mutumci da kara, basa abin ƙaranta komai nasu cikin wadata suke yin sa.
Ko biki ne suke kai bare ma sai ka ci kasha komai a Wadace."

Ni dai ido ne nawa, haka suka dinga tattaunawa akan maganar.
Ƙarshe Aunty Zulai tace na taso muci naman, Allah ne ya tsaga da rabon su shi yasa.

Cewa na yi na ƙoshi na maida kaina na kwantar, nan da nan barci ya ɗauke ni.
Da asuba Umma Safiya ta ƙwank'waso mana ƙofa, muka tashi muka yi sallah.
Bayan idar da sallar mu, sai na koma na zan kwanta.

Cikin tsawa Aunty Zulai tace "Yau naga ikon Allah Rahamah barci za ki yi? Kina amarya ace kin kwanta ba tare da kin yi wanka ba."
Ina ji ina gani ta hanani barcin, sai da nayi wanka ta zaɓo min kayan cikin kayan da Abbannmu ya ɗin ka min daban, dan tace Duk cikin kayan da ke akwatina bata ga wani babba da zan sa na fitar kunya ba, dan ba wani laifen ku zo mu gani ya min na duk kuɗin sa.
Les É—in da na sa ma kyauta ce wadda Abbanmu ke bawa Kowacce daga cikin Æ´aÆ´an sa in za ta yi aure.

Ba ƙaramin kyau nayi ba, kasancewar Les ɗin fari ne irin fari tas ɗin nan, sai ratsin golden da duwatsu farare.
Ɗinkin doguwar riga ne sai akai mata aikin wuta tun daga sama har ƙasa.
Da kaina na É—aura É—ankwalin, kasancewar nima gwana ce ta wannan fannin, na iya kafa É—auri kala-kala.

A hankali nake bin kaina da kallo yadda nayi wani irin sihirtaccen kyau na musamman, kyakkyawar fuskata nake bi da kallo, wadda take a cike daidai gwargwado, inada hanci É—an madaidaici Masha Allah wanda ya yi daidai ya zauna a fuskata.
Sai ɗan madaidaicin bakina wanda ke ɗauke da fararen haƙorana wanda suke jere gwanin sha'awa da wushiryata yar daidai a tsakiyar su.
Yayin da in nayi dariya duka kumatuna ke lotsawa Dimple ɗina na bayyana, wanda ke ƙara min kyau na musamman.
Ina da cikar gashin gira dana ido, wanda bai sani ba zai ce ina sa Eyelashes ne.
Babu laifi, ina da ƴar ƙiba amma ba irin sosai ɗin nan ba, ko'ina na jikina a cike ya ke bani da rama ko kaɗan.
Dan haka kayan suka wani irin zama a jikina.

Turaruka na musamman na faffesa a jikina, su kansu su Aunty Zulai sai da suka dinga tsokana ta akan nayi kyau.

Babu jimawa sai ga Æ´an aike wasu mata biyu, É—auke da manyan fulasai, da kuloli sun kawo abincin karyawa.
Bayan mun gaggaisa suka ce mana in mun gama, a kaini na gaida uwar ango da uban ango suna farlon Dady.

Aunty Jamila ce tace basu san ina ne ba, shine suka ce in mun gama za su zo su raka mu.
Ni dai kasa shan shayin nayi, dan ko alamar citta babu bare ayi batun sauran kayan ƙamshi, da alama iya ruwan zafin ne aka tafasa da Lipton.
Sai gwangwanin madara da milo da sugar da aka haÉ—o da su.
Sai kuma soyayyen ƙwai da dankalin turawa shima soyayye.
Shikenan abin karyawar.

Su Binta ne kawai suka iya ci, Nan da nan Aunty Zulai ta kira Aunty Fati a waya tace ta aiko mana abinci, babu jimawa sai ga Aunty Fati ta zo.

Shi muka ci abinmu, babu jimawa wannan matar da tace zata taka mu gaida Maman Al'amen ta zo.

Sai yau na samu damar ƙarewa gidan kallo, Babban gida ne mai ɗauke da sashi daban-daban, kuma duka iri ɗaya ne.
Ban dai san guda nawa bane dan ta can baya ma ina hango wasu gine ginen.
Sashin da aka ce na mahaifiyar Al'amen ne muka shiga da sallama.
Wasu mata dake zazzaune suka amsa mana a tare, kaina a ƙasa ban iya banbance abubuwan dake farlon ba.
Sai dai idanuna dake kallon lafiyayyen carpet É—in dake malale a tsakiyar farlon.

Gaban matan aka tsugunnar dani, hannuna cikin na Aunty Zulai Dan ita kaÉ—ai ce ta biyo mu.
Haka na dinga gaida su, ta ƙarshen ce naji ta riƙe ni ta miƙar dani tare da fashewa da kuka.
Cikin mamakin meye abin kuka, na É—an buÉ—e mayafin fuskata dan ganin wace.
Babbar mace ce irin masu jikin nan sosai, kamar su ɗaya da Al'amen kamar an tsaga ƙara babu abinda ya raba su.
Cikin kukan da take, ta shiga samin albarka.
Wai na kyauta mata na share musu hawayen da suka daÉ—e suna zubarwa, na auri É—an ta ba tare dana guje shi ba.
Maganganu dai kala-kala tana ta sharɓa kuku, haushi duk ya ishe Ni da ta taimaka ta sake Ni ma da yafi Wallahi.
A zuciyata kam cewa nake _Ni ma baki san fin ƙarfi na aka yi ba, har na auri ɗan naki. Ƙaddara ita ta kaini in ba ita ba da baki ganni ba._

Bata sake ni ba, sai da ta gama kukanta san ranta, sannan ta sake ni ta wani jani kusa da ita ta zaunar.
Allah ya sani nayi danasanin zuwa gaisuwar nan, dan ina ji ina gani ban fita a wajen ta ba, ƙarshe Aunty Zulai tafiya tayi ta barni tace zata dawo.
Haka nayi tsuru-tsuru cikin su, bana jin abinda suke cewa sai surutu suke zubawa cikin yare.

Nafi awa É—aya sannan tace a kaini wajen Dady wato mahaifin Al'amen.
Shi da ya ke bahaushe ne, cikin ladabi na gaida shi ya dinga jero mana addu'o'i, daga ƙarshe ya sa mana albarka muka taso muka nufi sashin da aka sauke mu.

Aunty Zulai kamar zata ari baki saboda faɗa, cewa take an ƙi bari mu huta mu da muka sha uwar tafiya, babu in da zata ƙara bari na fita ya isa haka.

Haka da rana gidan ya cika da jama'a, muna jin su suna kid'en-kid'en su da raye-raye, duk cikin mu babu wanda ya fita sai Binta da Ummi, dan Binta cewa tayi sai ta je ta gano.

Naji daÉ—in yadda Aunty Zulai ta tsaya tsayin daka ta hana a shigo ko É—akin da nake, dan kowa ya zo cewa take bana jin daÉ—i a barni na huta.
A zuciyata nace _Mutum me faÉ—a ma yana da ranar sa._

Kwana ɗaya su Aunty Zulai suka ce zasu ƙara, gobe zasu tafi. Duk yadda na dinga roƙon su akan su ƙara kwana biyu, cewa suka yi garin ya ishe su, kuma ba hauka bane abin daga kawo amarya su zauna suƙi tafiya, sun fahimci ango kanshi a matse ya ke su tafi gwara su tafi abinsu.

Gaba ɗaya jikina a sanyaye ya ke, har na fara fargabar tafiyar su in suka tafi ya zamu ƙare da wannan mutumin?.
Da daddare Muna cikin fira dan nace yau ba zan yi barci ba, gwara mu yi firar bankwana.
Ina ganin wayata na kawo haske, saboda na sata a silent gudun kar mutumin nan ya dame ni, Dan tun da rana ya ke kirana wai na fito yana wajen parking É—in motoci, so ya ke ya ganni kawai.
Naƙi fita na daina ɗaga kiran shi baki ɗaya.

Shine yanzu ya ke ƙara kirana, ina sane naƙi ɗauka muka cigaba da firar mu da su Aunty.
Can muka ji ana gyaran murya a bakin ƙofa, cikin mamaki aunty Zulai tace "Waye?."

Gani muka yi ya sawo kai É—akin kai tsaye da uban tumbin sa a gaba, yana faÉ—in "Ni ne Aunty."
Chapter 6 · 0% Book details