← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ture shi na shiga yi ina faÉ—in "Dan Allah sake ni, wai me ma ya kawo ka É—akina, ta ina ka shigo min ma?."

Kunna fitilar gefen gadon ya yi, ina iya ganin shi shima yana gani na.
Ya wani kafe ni da ido cikin wata irin murya yace "Ke ki ke da gidan Da za ki na tambayar yadda na shigo?."

Ya ƙara yowa wajena da nufin kama ni, kaucewa na yi da sauri dan gaba ɗaya wani irin wari ya ke min, kuma ba warin komai bane sai warin zufa. Irin mutum ya wuni a ranar nan ya sha aikin wahala ya yi zufa ɗin nan.
Ga bakin shi da in ya yi magana kusa dani, da nake jin yana tashi.
Har ga Allah har wani amai-amai nake ji. Saboda a rayuwata na tsani wari, haka hancina yana da saurin jin wari ko ƙamshi ko ya ya ne kuwa.

Ina ja baya ina komai, haka ya haÉ—e ni da fuskar gadon.
Yau ma abinda ya min jiya ya maimaita, sai dai yau cikin hayyacina nake. Nasha azaba ba kaɗan ba. Yana komawa gefe na tashi da ƙyar na nufi toilet na fara sheƙa amai kamar zan amayar da ƴaƴan hanjina.
Saboda uban warin da na shaƙa a jikin shi, gaba ɗaya cikina ya hautsine.

Ban fito daga toilet É—in ba, sai da nayi wanka na haÉ—a da wankan tsarki na É—auro alwala, ina bin bango na fito na sa kaya na tada Sallah.
Raka'a biyu nayi na daɗe a sujjadar ƙarshe ina kaiwa Allah kukana.
Na zauna tare da yin addu'o'i na, akan neman mafita wajen Allah akan wannan auren nawa.
Anan barci ya kwashe ni.

Jin motsin mutum kusa da ni yasa na buɗe idanuna dake cike da barci, cikin mamaki na ƙara ware idona akan shi.

Al'amen ne tsaye yana Sallah a gefe na, cikin shigar jallabiya.
Cikin nutsuwa ya ke sallar tashi, kuma gabas ya kalla saɓanin jiya.
Kallona na kai ga agogon ɗakin, sai naga ƙarfe ukun dare 3:0am.
A zuciyata nace _Ikon Allah shima nafila ya ke yi kenan?_ gaba É—aya na rasa in da ya kamata na aje Al'amen.
Dan abubuwan da ya ke ƙara sani cikin ruɗani suke baki ɗaya.

Yana idar wa naga ya É—auki Alqur'ani, ya shiga karatu kamar yadda ya yi a safiyar yau.
Tun ina kallon shi har barci ya ƙara ɗauka ta.

Da safe koda na farka ban ganshi a É—akin ba.
Dan haka na tashi na tattara É—akin na gyara, na fita farlon shima na gyare shi tsaf rana ta farko dana ji sha'awar in sa turaren wuta a gidan.
Dan haka na koma É—akin, cikin kayana da suka rage anan, saboda duk sauran dama ba'a kawo su nan ba, kai tsaye wancan gidan da yace zamu zauna aka kai har kayan gadona da komai an gama min jere na. Zuwa kaÉ—ai ya rage.
Nan iya abubuwan da zan yi amfani dasu ne kawai.

Ina cikin zuba turaren sai ga sallamar shi ya shigo, sanye dai ya ke da jallabiyar da zan iya cewa ta gado ce. Dan tunda nazo ita naga yana sawa. Hannun shi riƙe da carbi alamar daga masallaci ya ke.

Tunda na kalle shi sau ɗaya na ɗauke kaina, sai ya ƙaraso kusa dani yana ƙoƙarin riƙo hannu na na kauce.

Ya ɗan ɓata rai yace "Gaida ki zan yi tunda naga ke baki iya gaisuwar ba, duk da nasan ba tarbiyyar da aka baki kenan ba kin tsirowa kan ki ne."

Bance masa komai ba, na ƙara ja baya.
Ya kalle ni tare da taɓe baki yace "Ki riƙe jikin ki, Ni yanzu abinda nake son faɗa miki, ki kasance cikin shiri yau zamu koma sabon gidan mu. Saboda haka ki wuce ki fara shiryawa. Sannan ki je wajen Hajiyar mu ku gaisa, dan tace dama bakya zuwa kina gaida kowa a gidan nan tun ranar da aka kawo ki.
Ki kula bana son rashin mutumcin ki ya shafi iyayena, duk abinda za ki yi ki yi ƙoƙarin kaucewa ɓata musu, karki bari a dinga kawo min ƙarar ki."
Yana gama faÉ—in haka, ya juya ya nufi bedroom.

Ganin ya kusa shiga yasa na É—aga murya nace "Babu in da zani na gaida waÉ—an da ba jin Yaren su nake ba, Iya gidan Aunty Fati kawai zan je na mata sallama."

Har ya kama mariƙin ƙofar zai shiga, jin maganata yasa ya fasa ya dawo da baya.
Ya ƙaraso wajena ya nuna ni da hannu cikin kashedi yace "In kin cika mara kunya karki je, in har baki je ba ko gidan Aunty Fati ɗin ba zaki je ba."
Ya juya ya tafi ya barni tsaye.

Tsaki naja na bi bayan shi da kallo, kamar nayi dariya ganin yadda ya ke tafiya a wani barbaje kamar buhun fulawa.
Na kauda kaina na zauna kan kujera ina shawara da zuciyata.

Allah ya sani bawai son shiga cikin gidan ne bana yi ba, kwata-kwata wannan hayaniyar tasu ce bana so. Basu iya komai a hankali ba, sai ihu da hayaniya ka rasa ma me suke cewa duka.
Nasan in ya hana ni zuwa gidan Aunty Fati, ban isa na je ba.
Dan sai me gadi ya buɗe min ƙofar zan fita, na kuma san cewa zai yi kar ya buɗe min.

Dan haka sai kawai na nufi ɗakin, zaune ba tarda shi ya baje a ƙasa babu ko riga a jikin shi.
Daga shi dai gajeren wando wanda ko cinyar shi bai gama rufewa ba.
KuÉ—i ne dami-dami a gaban shi yana ta faman lissafi.

Yana ganina ya wani haɗe rai, na kauda kaina tare da taɓe baki na wuce wadrobe na ɗauki Hijabina har ƙasa nasa, na kalle shi nace "Na tafi wajen Hajiyar."

Bai min magana ba, sai jinjina kai da ya yi ya cigaba da lissafin sa.
A zuciyata nace _Ko ance masa kuÉ—in sa ya dame ni ne? Da ya wani haÉ—e rai dan ya ganni_

Da sallama na shiga farlon, wata mata na gani zaune da alamar Æ´ar aiki ce.
Tana ganina ta miƙe ta shiga gaida ni cikin gurbatacciyar hausar ta.

Amsawa nayi nace "Ina Hajiya?."
Nu ni ta min da saman bene tace "Ya shiga ciki."

Waje na nema na zaune a kan É—aya daga cikin kujerun farlon, na É—aga idanuna ina bin farlon da kallo a hankali.
Gani nayi matar ta doshi saman, alamar zata sanarwa Hajiyar da zuwana kenan.

Babu jimawa ta sakko tace min "Yace ka shiga."

Ba dan na so ba, na tashi na nufi saman ina bin ko'ina da kallo.
Ƙofa ɗaya ce kawai a saman, dan haka na tura na shiga da sallama a bakina.

Ɗan ƙaramin farlo ne, me ɗauke da setin kujeru ɗaya, da tv dake manne a bangon dake kallon ƙofa, sai wani ɗan tebur ƙarami dake tsakiyar farlon remote ne akan shi da wani ɗan kofi alamar Abu aka sha a ciki.

Daga ciki na ji ance "Ki shigo ina ciki."

Nufar ƙofar da na ji maganar na yi, na yi sallama aka amsa na shiga.
Tana zaune a bakin gado, gaban ta wasu takardu ne tana duddubawa idanun ta sanye da gilashi irin na ƙara ƙarfin gani ɗin nan.

A ƙasan carpet ɗin nake ƙoƙarin zama, ta ɗago ta nuna min gefen ta tace "Dawo nan ki zauna, ya za ki zauna a ƙasa."

Zama na yi nace "Ki barshi Hajiya nan ma ya isa, dan ina ganin yau dai ba zan iya zama kusa da ita ba, dan haka baya cikin kunyar da aka sanmu da ita ga surukai mu Hausawa kenan.

Ganin na riga dana zauna, sai bata ce komai ba ta aje takardun ta fuskance ni tana murrmushi.
Na gaida ta ta amsa, tare da tambayar lafiya ta, harda cewa fatan ina kula mata da yaron ta yadda ya kamata.
A bakinta ma nake ji, ashe Al'amen yana da yayu maza biyu da mata uku, sai ƙaramar ƙanwar shi tace tana aure a ibadan. Kuma tace gidan Yayan Al'amen ɗayan ma yana jikin gidan mu, matan sa biyu da yaran sa.

Ni dai jinta kawai nake, a raina nace _Sai kace na tambaye ta._
Ta daÉ—e tana bani labarin su, tare da min nasiha akan dai na kula mata da É—an ta.
Ni kam nace _ÆŠan ki kaÉ—ai ki ka sani, ba ruwan ki da Æ´ar mutane da halin da take ciki._

Ban wani É—auki lokaci ba nace mata zan tafi, nan ta tashi ta biyo bayana.
Kitchen ta shiga ta haÉ—o min wasu abubuwa a leda, tace "Gashi na É—an yi aiki da su kwana biyu, Al'amen na son su shi yasa.
Ba tare dana san meye ba, na amsa na tafi.

Koda na koma na tarda ya fito a É—akin, anyi Sa'a ya yi wanka ya canja kayan jikin sa.
Ko zama ban yi ba na aje ledar.

Nace masa zan je wajen Aunty Fati.
Miƙewa naga ya yi yace "Mu je na raka ki, dama ai ban je na mata ya gajiyar biki ba."

Kallon mamaki na shiga bin shi da shi nace "Ba sai ka bi ni ba, ina zaton ai in zaka gaisheta zaka iya zuwa daban ko?."

"To ni tare nake so mu je, in ba haka ba sai dai ki fasa tafiyar."

Bisa dole ina ji ina gani haka muka jera, duk da muna fita muka shiga gidan Aunty Fati É—in, amma sai na tsinci kaina da jin kunyar yadda na jera da shi abu Ruguzaza haka.

Wajen me gadin Aunty Fati ya zauna, na wuce ciki na tarda yara ne kaÉ—ai a farlon.
Suna ganina suka taso a guje suna min Oyoyo.
Iya Kamal kaÉ—ai na É—auka, na dungurewa Islam kai nace "Ke ba ruwana da ke, dan baki da kirki matsa ki bani waje dan Allah, wannan shi ne É—ana."

Matsawa ta yi tana ɓata rai, ban bi ta kanta ba na wuce bedroom ɗin Aunty Fati kai tsaye dan Kamal yace tana ciki.

Linkin kaya na tarar tana yi. Tana gani na ta fara fara'a tana kallona cikin murna tace "A'a Amarsusu ta angon ta mai abin mamaki, ku ne tafe kenan?."
Ta ƙarasa faɗar tare da miƙewa tsaye ta nufo ni.
Chapter 12 · 0% Book details