← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 22

Sashe 16

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ban ce mata komai ba, na maida kaina na kwantar kawai.
Ni kaÉ—ai nasan me meke damuna a zuciyata.

Har dare muna tare da Aunty Fati, haka ta dinga nan-nan dani tana kawo min abubuwan ƙwadayi irin na masu ciki.
Kusan har dare tana kitchen, ko da ya zo É—auka ta haka ta cika min kula da dambun zogalen da nace mata ina so.

Tunda na shiga motar ko magana ban masa ba, shima bai ce min komai ba, sai motar da naga ya shigar gidan su.
Har ya buɗe ya fita ban motsa ba, ganin haka yasa ya leƙo fuska a haɗe yace "In kinga dama ki fito mu shiga ki gaida Hajiya."

Kamar kar na fita, tuna inda muke abu kaÉ—an zan yi ya sani a idon mutane.
Hakan yasa na fito ina ɓata rai nabi bayan shi. Farlon Hajiyar su muka nufa, kuma har yau ina mamakin me yasa baya kaini wajen sauran matan Baban shi, ko bai ɗauke su a matsayin iyaye bane ban sani ba.
Dan ko suma ƴan uwan nashi, basa wani damuwa da lamarin shi sai in buƙatar su ta kawo su, wasu daga cikin su kenan waɗan da ƙarfin su bai kai nashi ba.

Sai da muka shiga wajen Hajiyar na ƙara tabbatar da Al'amen baida kunya, dan ba wata damuwa yace mata, ina da cikin sati biyu.
Nayi zaton zata ji nauyi, sai naga ta hau murna tana addu'ar, Allah ya rabamu lafiya.
Ni dai gaba ɗaya a takure nake jina, daga ƙarshe sai ga Anisa ta fito wai zamu tafi tare da ita.
Ashe tunda ya fita da ita wajen Hajiyar ya kawo ta.
Ni sai naga kamar Hajiyar ma na wani harhaÉ—e min rai, dan bata wani sake min yadda ta saba ba.
A raina nace _Ke kika sani, daga ke har É—an ki bakwa gabana._

Haka muka baro wajen ta, yace Anisa ta jira mu a mota muka shiga wajen Dadyn su ance baya jin daÉ—i.

Na tausayawa bawan Allah, ganin halin da ya ke ciki na ciwo.
Yana kwance a farlo akan katifa, an É—aura masa ruwa, ciwon lokaci guda har ya rame.

Har ƙasa na tsugunna na gaida shi, da ƙyar ya amsa na masa addu'a akan Allah ya bashi lafiya.
Al'amen ya gyara masa kwanciya, muka masa sai da safe, ya bimu da addu'ar zaman lafiya muka tafi.

Muna isa gida na riga su fita a motar, kai tsaye wuce É—akina, farkon abinda na fara shine fito da katifar Anisa daga É—akina.
Daidai lokacin dana ɗire katifar ina ƙoƙarin juyawa ya sawo kai farlon.

Ban dakata ba na cigaba da tafiya, ina jin shi yana kiran sunana yana faÉ—in "Lafiya Rahamah ki ka fito mata da katifa?."

Ban kula shi ba, ya biyo Ni har cikin É—akin cikin fushi yace "Wai ba dake nake magana ba?, ya ina tambayar ki zaki share Ni ki yi banza dani."

Ba tare dana kalle shi ba na ƙarasa bakin gado na zauna nace "Na rantse da Allah ka ji na rantse ko? Muddin kace Anisa zata cigaba da kwana a ɗakina, to sai dai ka zaɓi ɗaya. Ko Ni ko ita, dan in har kace ta cigaba da kwana daga yau na haramtawa kaina kwanan ɗakin, in yaso sai ku dinga kwana tare."

Na yi tunanin zai hayayyaƙo min, kamar yadda ya saba in maganar ta haɗa mu.
Cikin mamaki naga ya sassauta murya yace "Ki yi Haƙuri ba za'a yi haka ba, na yarda ta daina kwana a ɗakin, amma yanzu ki taso mu je ki taya ni mu gyara mata ɗakin farlo, tunda ba komai a cikin sa."

Tsaki naja na kauda kaina nace "Babu in da zan je, kai dai da ka É—auko ta kaga zaka iya da hidimar ta ai sai ka je ka gyara mata."

Al'amen gaba É—aya daurewa yake, yana Binta a hankalina ne kawai saboda sharaÉ—in da Malam Mustapha ya bashi, tun sa'ar da ya sanar da shi tana da ciki.
A waya ya kira shi.

Nan ne fa yace ya yi ƙoƙari wajen bin duk abinda take so, ko zasu samu ta saki jiki da shi ta dinga abinda suke so.
Tunda dai yanzu Allah yasa tana da ciki, me ciki na son kulawa ya dinga daurewa.

Wannan shine dalilin da yasa har ya sassauta muryar shi yanzu.

Ina jin shi ya fita yana kiciniyar sharar É—akin, har ya gama ya dawo lokacin tuni nayi wanka na kwanta.

Ganin yana shirin hawa gadon ba tare daya yi wanka ba, nayi sauran tashi na zauna ina kallon shi nace "Kamar yaya zaka kwanta ba wanka?gaskiya in har ba kayi wanka ba, bana tunanin zan kwana a É—akin nan sai na koma farlo abuna."

Ban yi zaton zai sauka ba, sai naga ya sauka tare da jan dogon tsaki ya nufi toilet.
Babu jimawa sai gashi ya fito ɗaure da zanina a ƙugun shi.

Cikin takaici na kalle shi, ban ma san yaushe ya buÉ—e Wardrobe ya É—auki zanina ba, haka kuma ya nufo gadon jikin shi duk ruwa da niyar kwantawa.

Ƙara tashi nayi na dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu nace "Kaga dan Allah ka fara goge jikin ka, kuma ni karka ƙara ɗaura min zani na haka kawai akwai towel a toilet ba babu ba."

Bai ce min komai ba ya nufi wadrobe, cire zanin nayi ganin zai maida wadrobe nace "Karka sa dan Allah, baka ga ruwa a jikin ka ba.

Rataye zanin ya yi a kan katakon jakunkuna na, ya É—auki gajeren wandon ya saka ya hawo gadon yana ta jan tsaki.
To ranar dai dama-dama zance, sunan ya yi wanka ne amma har lokacin jikin shi bai daina tashi ba.
Yau cikin Sa'a sai banyi amai ba.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin ikon Allah na cigaba da rainon cikina, inda a halin yanzu har ya kai wata uku, kuma duk abinda nace Al'amen ya min yana ƙoƙarin yi sosai,
ba tare da musu ko cewa ba zai yi ba.

A hankali ƙaunar cikin jikina ta fara shiga raina, koba komai nima jinina ne kuma bashi da laifin komai a gare ni, tunda bai min komai ba.
Bai san me ke tafiya a duniya ba, addu'ar da nake kawai shine, Allah ya bani nagari ya tsare shi kar ya gado mahaifin sa ko karta gano mahaifinta.

Yau ina kitchen da rana, sai ga shi ya shigo hannun sa riƙe da wata leda.
Ajiye wa ya yi yace "Ga wannan ki yi min Farfesu, kan rago ne bana so a haɗa da harshen amma, ki cire shi daban tun daga tushiyar sa har ƙarshe.
Bayan nan ki dafa min faten wake, ina son raba sadakar su ne."

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*

[1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG

*BAƘAR ZUCIYA!.*

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*

*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET DOCUMENT, GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*

*PAGE 9️⃣*

Kallon ledar nayi na ɗago na kalle shi, sai ya shiga washe baki yana faɗin "Dan Allah Rahamah ki yi yadda nace, iya harshen kaɗai za ki cire bari na je na amso wani saƙo, tare nake so na haɗa na raba."

Ganin yana ƙoƙarin tafiya, na cire hannuna a ruwan da nake wanke shinkafa nace "Kaga dakata. Dawo ka ɗauki wannan abin daka kawo min, ba zan dafa ba dan babu ni a cikin shirka,
Wacce irin jarabace wannan fisabilillahi ace kan rago za'a dafa ayi sadaka kuma bayan an cire harshe, wannan ba sadaka bace Wallahi sai dai in wani salon tsubbu ne."
Na ƙarasa faɗar tare da shure ledar da ƙafata, aikuwa sai ga kan rago ya fito gudan shi, da alama ma yanzu aka yanka dan ga jini nan kaca-kaca.

Da sauri na É—auke kaina naja baya tare da sa hannu na toshe hancina.
Aikuwa ya dawo da sauri ya tsugunna ya É—auke kan ragon, ina kallon shi yasa a leda nayi zaton zai ce wani abu.
Sai naga ya juya ya fita a kitchen É—in kawai, tsaki naja ina Allah wadai da halin shi duk zatona da naji kwana biyu baya cewa ayi sadaka, nayi zaton ya daina ne ashe yana nan yana sha'anin sa.
Addu'ata kullum ita ce Allah ya tsare ni daga sharrin sa, dan gaba É—aya yanzu ya dawo min da tsohon tsoron shi a raina.

Babu jimawa kuma sai gashi ya dawo kitchen ɗin, hannun shi riƙe da wata roba duk jini ya ɓata ta, da sauri nasa hannu na toshe hancina ina faɗin "Dan Allah ka fitar da wannan abin daga nan bana so."

Wani kallo ya watsa min yace "Ni da gidana zaki hanani abinda nake so, Wallahi Rahamah duk iskancin da kike kina cin wata alfarma ne kawai.
Karki bari nayi fatali da hakan, duk ranar da ki ka kaini ƙarshe zan shayar dake ruwan mamaki."
Chapter 16 · 0% Book details