Sashe 21
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata irin zuciya ce ta É—ebe ni, jin da nayi yace wai kishin shi nake.
Dan haka cike da tsiwa na tashi na kalle shi a wulaƙance na shiga nuna shi da hannu nace "Ka kalle ka fa dan Allah."
Nayi wani irin murrmushi me ciwo nace "In ba ƙaddara ba da rabon wannan cikin, me zai haɗa ni da kai ko a hanya? Wallahi kai da kanka kasan nafi ƙarfin ka na wuce ajin auren ka, ƙaddara ce kawai ta kawo ni cikin gidan ka, kuma a kullum ina addu'a Allah ya warware min auren nan naka, wanda ya zame min dana sani, ya zame min masifa da baƙin cikin rayuwa."
Nan da nan kuka ya ƙwace min, na koma na zauna ina yin shi cikin ƙunar rai.
Tsaki yaja me ƙarfi, ranshi a ɓace ya nuna ni da ɗan yatsan shi yace "Wato ni ne na zama masifa a rayuwar ki ko? To ki tattara ki wuce ki je gidan Aunty Fati ki yi sati biyu, na baki hutu bana ciki da raini.
In yaso in ina da amfani a rayuwar ki zaki sani, karki bari na dawo na same ki a gidannan, wallahi in na dawo na same ki kome na miki ke kika siya."
Yana gama faÉ—in hakan ya juya ya fice, ya barni zaune na cigaba da kukana.
Can kamar wadda aka mintsina na tashi da sauri, tuna kalmar shi da yace ya bani hutu.
To ai ni gaba ta kaini, in sha Allahu in na bar gidannan na barshi kenan har abada.
Da sauri na É—auki wayata na kira Aunty Fati.
Tana É—agawa Bayan mun gaisa nace "Aunty kina gida ne?."
"Eh ina gida lafiya ko?."
Daga can Aunty Fati ta amsa min.
"Babu komai, gani nan zuwa yanzu."
Nace mata tare da katse wayar.
Iya hijabi kawai na ɗora akan kayan jikina, na ɗauki jakata ƴar ƙarama da iya wayata da ƴan canji ne a ciki.
Ina fita kai tsaye titi na fita, in da nasha tafiya kafin na isa dan ban taɓa fita ni kaɗai ba tun da na zo gidan.
Da ƙyar na samu abin hawa, kasancewar titin babu cikowar ababan hawa.
Ana sauke ni ƙofar gidan Aunty Fati na biya me mashin ɗin na shiga.
Bakin famfo na tarda ta tana wankin kayan yara, kujera Ƴar tsugunno dake gefen ta na zauna ina faɗin "Kai nasha wuya wallahi."
ÆŠagowa tayi tana bina da kallo, idanun ta akan fuskata tace "Lafiya naga fuskar ki a kumbure kamar wadda ta kwana tana kuka? Sannan ina mijin naki kika zo ke kaÉ—ai?."
Cire hijabin jikina nayi na miƙe tsaye nace "Cewa ya yi na taho nan na huta, iya abinda yace min kenan ni nagaji bari na je na ɗan kwanta.'"
Ban jira cewar ta ba, na nufi farlo dan da gaske a gajiye nake."
Babu shiri Aunty Fati ta tsame hannun ta a ruwan wankin, ta biyo bayana tana faÉ—in "Wanne irin ki zo ki huta a gidana? Ko dai wani abin ne ya faru tsakanin ku yace ki taho É—in?."
Sai da na zauna akan kujera ina nishi nace "Wallahi babu komai, bayan dai abinda ya haÉ—a mu akan kawo Æ´ar yar Hajiyar su da yace zai yi farlona, nace karya kawo ta ya kaita wani sashin.
Har dai saɓani ya haɗa mu dashi, muka ɗan yi faɗa yace sai ya kawo ta ban isa ba, yanzu ina ɗaki zaune ya same ni da maganar abinci, daga magana kaɗan yace na wuce gidan ki na huta tsahon sati biyu.
Zama Aunty Fati tayi a gefena tana bina da kallo tace "Um um Rahamah, kodai wani abin ne ya faru daban?, dan da wuya yace ki tafi gida haka kawai ba tare da wani laifi ba, iya wannan maganar bata ci ace yace ki taho nan ba."
Ta É—an numfasa da maganar kaÉ—an tace "Kuma da yace ki taho nan a garin mahauka muke ne, ai ba anan ya É—auke ki ba a Kaduna ya aure ki, Nima zaune nake gidan wani da zai ce ki zo wajena ki zauna."
Gyara zamana nayi nace "Wai kina mamaki ko? To ki daina mamaki kaÉ—an daga haukan Al'amen kenan, in ina faÉ—a miki baida seti ai ke ke goya masa baya, gashi yanzu kema kin gani ai."
Girgiza min kai tayi tace "Ko yanzu bawai zan yanke hukunci bane Rahamah, dole a neme shi a ji ta bakin sa shima tunda ba'a yanke hukunci da ɓangare ɗaya, dole sai shima anji ta bakin shi tukun na."
"To shikenan Aunty, ku kira shi ɗin ku ji da kunnen ku, banga amfanin ƙarya da zan muku ba."
Na faÉ—i hakan a sanyaye.
"Ba ƙarya nace kin min ba Rahamah, dan ni tuni na fara dawowa daga rakiyar Jagaba, kawai dai ina son tabbatarwa ne daga shi ɗin."
Daga haka tace zata kira mijin ta, shi zai nemi Al'amen tunda shine namiji.
Haka kuwa aka yi ta kira shi ta faÉ—a masa, sai aka ci Sa'a yace yana kusa da gida ma.
Koda ya dawo shi da kanshi ya yi mamakin abinda nace, haka ya dinga tambayata ko dai wani abin ne daban, in akwai wani abu na faÉ—a musu kafin su nemi Al'amen, dan su san irin matakin da zasu É—auka.
Cewa nayi iya wannan ne, ina ji a ƙasan raina kamar zan iya faɗan komai amma na kasa.
Kiran wayar Al'amen Mijin Aunty Fati ya yi yace yana son ganin shi, babu kunya yace shi ba zai zo ba, sai dai in ana son magana da shi a je a same shi.
Da ya ke a hansfree ya saka wayar muna jin komai.
Cikin fushi Aunty Fati tace "Dan Allah ka ƙyale ɗan wulaƙanci, Rahamah tafi ƙarfin wulaƙantawa wallahi, gari na wayewa zata tafi Kaduna, ai ba daga sama ya samo ta ba, tana da gatan ta da komai."
Ɗaga mata hannu mijin Aunty Fati yayi yace "Kar ki ce haka Ammin Islam, shi lamarin aure ba'a masa gaggawa, haka in matsala ta faru tsakanin ma'aurata ba'a shiga barin su ake, kar ki zaƙe da yawa, ku bari na je wajen nashi ni da kaina, in yaso duk yadda muka yi in na dawo zaku ji."
Badan ranmu ya so ba muka amince, haka ya tafi wajen Al'amen É—in.
Fitar shi babu daÉ—e wa, muka ji tsaiwar mota a farfajiyar gidan.
Cike da mamaki nake bin yaran dake shigowa da kallo, hannayen su É—auke da akwatuna na har biyu, sai wata babbar jaka ta ita ma cike da kaya.
Binsu muke da kallo kawai, dan ita Aunty Fati ta kasa komawa ta ƙarasa wankin ma.
Tambayar su muka yi waya aiko su, suka ce Jagaba ne yace su kawo, suka juya suka tafi abin su.
Cike da takaici Aunty Fati ke faɗin "Wallahi na yarda da maganar ki Rahamah, kai amma wannan mutumin ba ƙaramin ɗan iska bane."
Ni dai ina zaune zuciyata cike da baƙin ciki, me hakan ke nufi? Duk da bana son shi amma banyi zaton cin mutumcin zai kai haka ba.
Miƙewa nayi tsaye nace "Wallahi ba zan ƙara kwana ɗaya a garin nan ba, tafiya gida zanyi Aunty ai ina da iyaye ba wai banda su ba."
Ita ma cike da takaici tace "Ai maganar tafiyar ki gida ma ta zama dole, sai dai tausayin ki nake da wannan cikin na jikin ki Rahamah."
Tsaki naja nace "Wallahi ko da cikin nan zai zube sai na bar garin nan, ba zan iya ƙara kwana ɗaya ba ji nake kamar ana hura min wuta a garin nan."
Muna cikin tattaunawa sai ga mijin ta ya dawo, ranshi a matuƙar ɓace ya ke, ko sannu da zuwan da muke masa bai amsa ba, ya kalle mu ya kalli kayan dake gaban mu yace "Kenan kayan sun iso ashe?."
Aunty Fati ce tace "Gasu kana gani ma, wai ya ku
ka yi da shi ma tukunna?."
Zama ya yi yana yi
Faman jan tsaki yace "Ammin Islam wannan mutumin yau na tabbatar baida hankali, ke kin ga haukan da ya dinga min a cikin mutane yana aibata yarinyar nan, Wallahi da ace nasan abinda zai yi kenan ba zan je ba."
Ina ganin haka na fice ina jin zafi a zuciyata, Ni kaɗai nasan halin da nake ciki dan tsabar baƙin ciki.
Kallon shi Aunty Fati tayi cike da lallashi tace "Ka yi haƙuri me ya faɗa maka?."
Kwashe yadda suka yi da shi ya yi ya faÉ—a mata, yace Al'amen yace Rahamah bata jin maganar shi, sannan ko abinci bata dafawa sai taga dama, kuma bata yi masa abinci me daÉ—i kullum sai ya fita ya siyo, kuma in yace tayi irin nasu na yarabawa tace ba zata yi ba.
Ga shi bata bashi haÉ—in kai a wajen kwanciya."
Yana kawowa nan ya dakata cike da takaici yace "Kawai dai abar sauran maganar, Wallahi wasu batutuwan bai kamata ace sun fito daga bakin sa ba, dan ni kallon me hankali nake masa ada."
Tsaki Aunty Fati taja cike da takaici tace "Me yace kuma dan Allah?."
"Babban baƙin cikina shine, yadda ya dinga ɗaga murya a cikin kasuwa, wai harda cewa shi ba daɗin mu'amalar aure ya ke ji da ita ba, kuma da alama ba yau ya fara faɗa ba, dan har wasu daga cikin abokan kasuwancin sa da suka ji muna magana suka taso, harda me ce masa haƙuri ake ai rannan ya bashi shawarar ya sai mata maganin sanyin."
Ya kalli Aunty Fati cike da takaici yace "Ki ji wannan abin kunyar dan Allah."
Gaba ɗaya kan Aunty Fati ya gama kullewa, sabuwar magana take ji wadda bata taɓa zaton ba, lallai Al'amen kura ne da fatar akuya yau ta yarda da Rahamah, dan ita kaɗai tasan me take ji.
Maganar da mijinta ya cigaba yasa ta bashi hankalin ta "Kin san har haƙuri na bashi akan ya maida yarinyar nan, sai ce min yayi Wallahi sai ta yi sati biyun da yace, in da kuma zaki san bai da hankali wai harda bani kuɗi wai na sai mata abinda take so.
Ban amsa ba takaici yasa na baro wajen cike da kunya da ya sani."