Sashe 4
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Koda na juya zan tafi, haka ya zaro kuɗi, damin ƴan dubu guda, wato dubu ɗari kenan, ya miƙo min wai na amsa.
Zagaye shi nayi na tafi abina, ko juyowa banyi ba duk irin kiran da ya ke min, a zuciyata ina cewa _Haka kawai ya wani bani kuÉ—i, ko ance masa kuÉ—i nake so._
Koda na koma cikin farin ciki, Aunty Fati ta shiga bani labari akan shi.
Wai ɗan maƙocin su ne, mahaifin sa mai kuɗi ne, yana da mata huɗu ɗaya ce kawai bahaushiya sauran duk yarabawa ne.
Mahaifiyar Al'amen ita ce babba, shine É—an ta na biyu.
Suna da arziƙi sosai dan shi Al'amen ma ana zaton ya gado mahaifin sa ne a dukiya, dan duk yafi sauran kuɗi waye-waye, duk dai ta dinga koɗa shi.
Harda cewa yana da kirki, ga kyauta kowacce rana cikin rabawa mabuƙata kuɗi da abinci ya ke, yana da mu'amala me kyau tsakanin sa da mutane.
Kowa na yaba kyawawan halayen sa, aure ne dai bai yi ba har yanzu, sakamakon duk yarinyar da ya nema sai an ci kuÉ—in sa, daga baya a hana shi auren ta.
Ya daÉ—e yana neman matar aure, har addu'a ake masa a masallatan unguwar akan Allah ya bashi mace ta gari, saboda yadda ya ke kai taimako makarantu da masallatai.
Duk maganganun ta, iya inda tace yana taimakon
Mabuƙata ne kawai ya burgeni, har ma na ɗan ji tausayin sa akan rashin auren da aka ce ba'a bashi.
Tashi nayi na nufi É—akin dake farlon, wanda anan na sauka nace "Allah ya bashi mace ta gari Aunty."
Sallamar Sani me gadi dana ji yana faɗin "Ga saƙo ance a bawa Rahamah, ita ta dakatar dani daga shiga ɗakin.
Na juya na kalli Aunty Fati wadda idanun ta ke kallon ƙofar farlon.
Kuɗin dai dana ƙi amsa, shine ya bawa sani ya biyo ni da shi.
Ita kanta Aunty Fati na fahimci bata so ya aiko kuÉ—in ba, dan haka na cewa Malam Sani ya maida yace an gode.
Kafin ma ya dawo na rufe ƙofar farlon, dan bana son damuwa, dama mijin Aunty Fati baya gari, yaranta kuma sun je gidan ƙanin mijinta hutu.
Washe gari sai ga shi ya zo, ƙiri-ƙiri naƙi fita.
Aunty Fati ganin bana son lamari, dole ta haƙura da tilasta min ɗin da take akan fitar.
Kwana biyu tsakani na shirya na koma Kaduna gida, dan dama sati biyu nayi niyar yi mata kuma nayi.
Komawata gida da sati ɗaya, wata ranar juma'a ina zaune ina wa Mama Hajara tsifa, naga ana kirana da baƙuwar number.
Ina É—agawa na gane Muryar me maganar, dan yana da irin saurin maganar nan.
Mutumin dai da na baro a Lagos ne, sai da nayi dana sanin É—aga kiran.
Wallahi dana san shine ba zan É—auka ba.
Ce min ya yi zai shigo Kaduna satin nan, yana son zuwa Kano sarin wasu kaya, in na bashi dama zai zo ya ganni ya gaida su Abbannmu.
Kai tsaye nace bana so, ya riƙe gaisuwar shi Nagode sosai.
Mama Hajara da taji abinda nace ne, bayan na yanke wayar. Ta shiga tambayata waye ya kira yace zai zo nace Ban yarda ba? Dan sun san halina na ƙin kula samari duk da na wuce ace ina hakan.
Ƙarya ba halina bace, dan haka na bata labarin komai. Cikin sanyin ta tace "Ki bari ya zo ku gaisa mana, gaisuwa ai ba komai bace Rahamah.
Me son ka shi ne kaÉ—ai zai damu da kai, har ya so ganin ka haka."
Bamu gama magana ba, sai ga wani kiran nashi ya shigo. Bisa dole na É—auki kiran, maganar ce dai ta zai zo wai akwai wani kaya da ya ke so ya siya a Kano, in yana zuwa zai sauka a Kaduna mu gaisa sai ya wuce, da dai sauran surutun sa.
Gudun Mama Hajara ta yi fushi nace Allah ya kawo shi lafiya.
Wallahi na manta da munyi magana da shi, bayan kwana biyu sai ga kira a wayata wai in faÉ—a masa sunan unguwar mu, gashi yana cikin garin Kaduna.
Kuma in sanarwa da su Abba zai zo ya gaida su, sosai na kaÉ—u da jin batun sa.
Taya zan cewa su Abba zan yi baƙi zasu gaida shi, bayan ƙa'idar gidan mu yarinya bata tsayawa sa saurayi sai da izinin mahaifanmu.
Kuma Ni ba son shi nake ba, bare nace wai ko zai zo ne saboda ni É—in.
Dan haka sai nace masa, ba sai ya gaida su Abba ba ni zan fito mu gaisa, duk da nasan hakan laifi ne a gidan mu .
Amma a ganina gwara hakan, in yaso faÉ—a kawai za'a min Shikenan an wuce wajen.
Cewa ya yi shikenan, na kwatanta masa unguwar tamu kawai.
Haka na faɗa masa sunan, na shirya na nufi gidan Aunty Baraka matar Yayan ƙawata Binta, dan akwai wata walima da zamu je da yamma, ina son na kai mata Hijabina ta goge min tunda mu wutar gidanmu ta samu matsala.
Kwata-kwata na manta da wani batun Al'amen tun da naje na samu fira,wayata ma na cikin jakata kuma na sata a silent, munfi awa biyu muna shan firar mu da ita, ita ta rako ni har wajen ƙofar gidan mu sannan ta koma, ina ce mata in na shirya zan kirata a waya.
Sai da na na zo shiga gida, ganin baƙin motoci ya tuna min da maganar Al'amen.
Hannu nasa na É—an dafe kaina ina faÉ—in "Kash nama manta da mutumin nan."
Nasa hannu a jakata tare da ciro wayata, ganin miss call nayi rututu sun fi ashirin, kuma duk shi ya kira ni.
Tsaki naja na tura k'yauren gidan mu na shiga, tun daga bakin zauren na fahimci gidan namu akwai baƙi.
Dan ƙofar farlon Abbanmu takalma ne na maza da yawa.
Zagayawa nayi ta bayan É—akin Abban dan shiga ainahin cikin gidan, dan bana son wucewa ta gaban farlon dan sai an ganni.
Ganin mutanen gidanmu nayi kusan baki É—aya a farlon Mama Hajara, cikin mamaki naga gaba É—aya ni suke kallo.
Na cire hijabina na zauna kusa da Aminatu ƙanwata, ina faɗin "Lafiya naga duk kun taru anan?."
Ummi ce tayi caraf tace "Ba dole ki ganmu anan zaune ba, tunda kin bamu mamaki Aunty Rahamah, Ashe dai tuni ke kin yi miji abinki na nunawa Sa'a."
Da sauri Mama Hajara ta kai hannu ta doke bakin ta, cikin zare mata ido tace "An tambaye ki rasai? Dan ƙaniyar ki tashi ki bawa mutane waje."
Sum-sum ta tashi hannun ta dafe da bakinta, ta fita daga farlon.
Kaina ne ya ɗaure baki ɗaya, dan haka na kasa daurewa na kalli Mama Hajara da ke magana da Ummanmu ƙasa-ƙasa nace "Wai Mama ban gane ba, baƙi muka yi a gidan ne yau?."
Yakubu ne da ya sawo kai ɗakin, ya bani amsa "Ki ji yarinyar nan da rainin hankali, tambaya ki ke baƙi aka yi bayan ke kika turo su?."
Amminmu ce tace "Barta ina ga yanzun ma raina mana hankali za ta yi."
Gaba É—aya sun É—aure min kai da maganganun su. Sai daga baya nake ji wai ashe Al'amen ne ya zo harda wasu manyan mutane, wai Ni na turo su sun zo da shirin komai harda sadaki ya shirya aure na.
Mun riga da mun yi magana da shi tuni.
Sosai na kaÉ—u da jin batun, na rasa me zance musu sai kuka dana fashe da shi, ina rantsuwar wallahi bani na turo shi ba, cewa ya yi kawai zamu gaisa nace ya zo.
Duk irin yadda na so su fahimce ni, sun ƙi fahimta ta.
Bayan tafiyar su Al'amen É—in ne Abba da Baba Usman suka kira ni suma.
Nasha faɗa sosai kafin ma su faɗa min Maƙasudin kiran nawa, nan suka maimaita min abinda su Ammi suka ce min, na Al'amen ya ce mun gama magana tuni. Ni na bashi izinin ya zo ya nemi aurena, in da Baba Usman ya hau faɗa a ina aka taɓa haka, kai tsaye a zo neman aure.
Amma tunda Ni na turo shi da kaina, su sun ce ya basu kwana biyu za su yi bincike akan shi, tunda abin ya zo da sauƙi ance maƙocin su Aunty Fati ne.
In yaso sai su bashi auren nawa, tunda dama sunyi-sunyi dani akan na fito da miji naƙi ina musu yawo da hankali.
Na fuskanci abin ya ɓata ran Abbanmu sosai, na zuwan Al'amen kai tsaye.
Hankalina ya matuƙar tashi da wannan batun, Allah ya sani ban sa a raina zan yi aure kusa ba, ga kuma wannan mutumin me tulelen ciki da ya zo ya haɗa Ni da iyayena.
Kwana nayi kuka zuciyata cike da k'uncin, wayar Aunty Fati ce ta tashe ni daga barci.
Cikin magagin barci na É—aga. Nan ta hauni da faÉ—a akan na munafunce ta ashe ina son Al'amen har mun gama shirya komai, gashi har ya zo Kaduna neman aurena, shine ko na faÉ—a mata tsabar gulma na nuna bana son shi. Su Abba ne suka kira ta da mijin ta jiya da dare, suka ce a musu bincike akan halayen Al'amen da yadda ya ke gudanar da mu'amalar sa da jama'a, da duk wani bincike da ya kamata ayi kafin a bada aure.
Sosai maganar ta bugeni, ya tabbata dai mutumin nan ya É—aure ni da jijiyoyin jikina, ta ko'ina ya gama sawa sun yarda Ni na tura shi neman aurena.
Duk yadda naso nawa Aunty Fati bayani, ƙin yarda ta yi da batuna.
Ga shi shegen duk kiran da nake masa yaƙi ɗauka kwata-kwata, ina son tambayar shi yaushe muka yi haka da shi ne kawai, sannan na roƙe shi ya janye maganar aurena ni bana son shi.
Sai da aka shafe kwana uku a gidan mu, ina ƙoƙarin wajen ganin na fahimtar da su bani na turo shi ba. Amma kowa cewa ya ke na sani, tunda Aunty Fati ta bada shaidar na san shi, kuma ita bata san yadda aka muka shirya junan mu ba.