← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 22

Sashe 19

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali naji kamar an buÉ—e min baki, sai dai ba abinda naso furtawa ne ya fito a baki na ba, "Ni matsalata dashi shine faÉ—a, abu kaÉ—an in nayi sai ya min faÉ—a, bayan nan kuma baya son canja gajeran wandon shi sai ya yi dauÉ—a, kuma baya gyara jikin sa ko ya yi wanka kamar bai yi ba, Wallahi har amai nake yi."
Na ƙarasa cikin kuka.

Wata ajiyar zuciya Al'amen ya sauke a fili, jin abinda Rahamah tace, har ya shiga tsoron kar ta tona masa asiri, amma tunda har ta fara iya faÉ—ar haka tabbas nan gaba zata tona asirin.
Ya zama dole ya É—auki mataki, musamman Zainab É—in nan dake son shigar masa rayuwa.

Gaba ɗaya suka yi shiru, suna nazarin maganganu na, Aunty Fati dai ta ɓangaren ta abin kunya ya bata.

Ita kuwa Aunty Zainab a hankali take nazartar fuskata, abin da take gani kamar bashi ne a zuciyata ba.
Dan haka ta ƙara tambaya ta, ƙara tabbatar mata da cewa shine kawai, ina jin wani irin zafi a zuciyata kamar zata faso ƙirjina.

Haka ta samu gaba ta mana nasiha, babu kunya ta faɗawa Al'amen gaskiya, kai tsaye tace masa in ita ce bama zata ɗauki ƙazantar sa ba.

Ya ji haushin yadda ta dizga shi babu kunya, bare kuma ayi batun mutumtawar da jama'a ke masa, haka dai suka lallashe ni tare da ban haƙuri suka tafi.

Bai min magana ba, ya tashi ya fice daga farlon.
Ko da dare ban ganshi ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya min ba, ranar nayi barcina cikin kwanciyar hankali da lumana.

Tun daga ranar sai ya canja, harda su fesa turare ya ke yanzu.
Haka in zamu kwanta yana ƙoƙarin yin wanka.
Ya daina zama da jallabiya guda, wanke baki ne dai sai a hankali.
Sai yafi sati bai wanke ba, wannan bai dame ni ba dan ko kusa da bakina bana bari ya kawo nashi.

Haka rayuwar mu ta cigaba da tafiya, yau daÉ—i gobe akasin ta.

A haka cikina ya shiga wata na shida, gaba É—aya na wani irin kumbura jikina ya buÉ—e.
Kwatsam yau na tashi naga ya shigo da masu kayan gado, ana auna É—akin da Anisa ke kwana.
Har na share ban tambaye shi ba, zatona ita zai sawa tunda a katifa take kwana.

Sai dai ganin ba kayan ɗaki kaɗai ba, harda akwatuna ake shigowa dasu yasa na sawa raina zan tambaye shi in ya dawo, dan akwatunan ba sabbi bane kamar dai irin za muyi baƙi ɗin nan.
Ni a gani na ko baƙi ne, ai akwai part har uku da ba kowa a ciki, banda na shi, dan haka sai na zuba ido ina jiran shigowar shi.

*_🥰 MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*
[1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG.

*BAƘAR ZUCIYA!.*

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*

*PAGE 1️⃣0️⃣*

*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET DOCUMENT, GA DUK ME BUƘATA TAMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*

*AL'AMEN*

Zaune suke shi da Malam Mustapha a bakin babban shagon da ya ke saida shaddoji da atamfofi da sauran su,
Inda bashi ke kula da wajen ba, ya É—ora yaran aiki ne dake kula da wajen, shi sai dai ya zo ya duba in an kwana biyu.

Bayan nan yana da shaguna a kasuwanni daban-daban, banda kowanne da abubuwan da yake zuwa ya É—ora yaran aiki, wani kayan masarufi wani kayan gini wasu katifu kai gasunan dai, shi É—in komai da ruwan kane.

Tare suka zo da Malam Mustapha, akan zai yi wata ajiya a shagon, saboda kasuwancin sa yanzu gaba ɗaya ya fara ƙasa, shi yasa ya zo suka duba wannan, da ya ke sun zo da maganin sai ya cewa yaran shagon su bashi waje.
Bayan sun aje maganin can ta bayan kantar shagon inda baza'a gani bane, sai suka zauna a bakin shagon daga gefe yadda ba za'a ji su ba suna tattaunawa, akan yadda zasu sauran shagunan su gudanar da ayyukan su ba tare da wani cikas ba.

_Allah ya kyauta, wasu mutanen suna yin_ _kuskure a rayuwar su. In da wasu basu ɗauke shi a bakin komai ba, wai sai an bada maganin kasuwa sannan za'a yi ciniki, shin akwai maganin kasuwar da ya wuce ka riƙe Allah ko ki riƙe Allah, ba wai ina kushe hakan bane kai tsaye, Ni a tawa fahimtar da kuma sani na babu wani maganin kasuwa da ya isa yasa ka samu kasuwa, muddin ba Allah ne ya dafa maka ba, in kuma kaga ance yi kaza dan farin jinin kasuwanci ko yi kaza dan ka samu kasuwa, tofa tabbas sai an kauce hanya ko yayane, yaku ƴan uwa ku sani ba'a wa Allah wayo, duk wata hanya da zaka a ɗora ka wadda zata kawo cigaba, muddin ba dabarun kasuwancin ko kasuwancin za'a koyar da kai ba, ko baka jari ko ace ka tashi ka roƙi ubangijinmu ba, to tabbas mu guji hanyar nan wata damfara ce wata kuma shirka ce aka mata kwaskwarima, Wallahi mu guji hakan mu tsaya tsayin daka akan gaskiya da riƙon amana a kasuwancin mu, mu tsaida sallah mu tashi mu roƙa wajen me kowa me komai, shi ɗin mawadaci ne shi kaɗai ne zai bamu ya ƙara ba tare da ya gajiya ba, in kuma ya bamu mu gode masa in mun rasa mu gode masa, Wallahi ba zamu taɓe ba, cigaba kuma zamu ganshi a rayuwar mu da albarka._

*_ALLAH YA MANA TSARI DA SHIRKA DA DUK WATA HANYA DA ZATA KAIMU GARE TA KO MAI KANKANTAR TA ALLAH KAR YA BAMU IKON BIN TA._*

Bayan sun gama suka tashi suka shiga mota dan zuwa gaba, a hanya ne Al'amen ya kalli Malam Mustapha yace "Kana ganin ba yarinyar nan bace ta jawo min asara? Duba da bata bada haÉ—in kai yadda ya kamata, sannnan kaga bar wasu abubuwa da kake sani saboda masifar ta."

Cikin nazari Mustapha ya kalle shi yace "Kuma fa kayi magana anan, amma ai nace kayi ƙoƙari ka dawo da yarinyar nan gidan ka, kaga sai ta kula da Anisa sannan kuma duk wasu ayyuka da Rahamah taƙi maka, sai ka bata ta maka ina ga kamar hakan shine mafita."

Girgiza kai Al'amen ya yi yace "Yanzu haka ana can ana gyara ɗakin, amma kasan ni ba wani son shiga harkar yara nake ba, ita kuma yarinyar nan na dawo da ita ne dan itama ta samu ta ƙarasa karatun ta, tunda ga Anisa a gidan koba komai Anisa zata rage zaman kaɗai ci, kuma ko wani abu Rahamah tayi bana nan ina so ta dinga sanar min.
Amma in batun ayyuka ne, gwara mu nemi wata hanya kawai bana son yarinyar ta san sirri na tunda tana min kallon wanda taƙi a baya."

"To shikenan ka bari na je gida yanzu, zan yi bincike sakamakon da bincikena ya bani da mafitar zan faÉ—a maka."
Cewar Malam Mustapha kenan.

Da wannan suka rufe firar, haka suka wuni ranar suna yawo kasuwanni, duk wani shagon dake amsa sunan na Al'amen sai da suka je suka sa maganin kasuwa.
Ban da sadakar da Malam yace ya raba, ya yi ɓarnar kuɗi ranar kamar bai san ciwon su ba.

A gajiye ya shigo gidan, gaba ɗaya babu abinda ya ke buƙata bayan ya kwanta ya huta, dan haka ko sashin Rahamah bai je ba ya wuce nashi.

A farlon ƙasa ya baje kan carpet yana numfarfashi, madadin ya fara wanka ko gajiyar zata ragu.
_Al'amen kenan, namu na gargajiya akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin shi da zama da warin rana😂_

***

*RAHAMAH.*

Tun ina zuba idon ganin shi, lokaci da naji shigowar motar shi, sai naji shiru babu shi ba labarin shi gashi har sun gama gyaran su tafi.

Fitowa farlo nayi, cikin Sa'a na tarda Anisa zaune tana kallo. Har wata ƴar ƙiba yarinyar ta ƙara da haske, alamar ta samu jin daɗi, to Ni dai ba ruwana da ita iya kaci na dafa taci, gaisuwa ma sai taga dama take min jifa-jifa yawanci sai Al'amen na nan.

Takawa nayi na ƙarasa kujerar dake gefen ta, a hankali na zauna saboda nauyin da cikina ya fara.
Na kalle ta cikin harshen turanci nace "Anisa in tambaye ki mana?."

Cikin mamaki naga tace "Ina jin ki."

Zaro ido nayi waje nace "Dama kina jin Hausa.?"

Jinjina min kai tayi, cikin haÉ—iye mamakina nace "Wai waye zai dawo É—akin ki, naga sai gyara ake an sa sabbin kaya?"

Ɗan rage volume ɗin tvn tayi tace "Aunty Shukhra ce zata dawo, Aunty na ce Baba yace tare zamu zauna da ita, wai itama ta ƙarasa karatun ta tunda banda me kulawa da ni."

A zuciyata nake faÉ—in _Wace Aunty Shukhra kuma?."_
Ashe wata zai sa a ɗakin, shine ni banda darajar da zai faɗa min ni da ɓangaren, in zai kawo mutanen shi ai ba hana shi zan yi ba, amma wannan sashin nawa ne ba nashi ba.
Dan dai in ji kan maganar, sai na shiga tambayar yarinyar cikin dubara.

Nan ta faɗa min komai, wai yarinyar yayar Hajiyar Al'amen ce, kuma da yaƙi aure an so a haɗa su tace bata son shi, to yanzu ta samu gurbi karatu ne anan garin tunda dama ƴar ilori ce, shine ta zaɓi gidannan tace anan zata zauna.

Sosai maganar ta bige ni, wa Al'amen ya ke shirin kawo min? Tsohuwar budurwar shi fa kenan? Cab aikuwa da sake ba ruwana da kishin sa tunda ba son shi nake ba, amma ya zama dole ya canja mata waje ba a cikin farlo na ba, ya kaita wani ɓangaren su je can su ƙarata ko auren ta ma ya yi, amma ba dai waje na ba.

Ganin yaƙi shigowa har wajen la'asar, hakan yasa na kasa daurewa na nufi sashin sa, rana ta farko kenan da zan taka ɓangaren nasa.
Dan ina jin gwara koma meye, muyi maganin shi kafin saukar baƙuwar.

Yadda na same shi ya wani baje kamar kayan wankin, sai da raina ya ɓaci ganin yadda ya tuɓe daga shi sai gajeren wandon sa na gado, ga uban kayan tumbin da ya wani baje shi a kan carpet ɗin, tumbin daban shi ma daban.
Chapter 19 · 0% Book details