Sashe 7
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rige-rigen gyara zama aka shiga, masu neman É—ankwali su É—aura nayi, masu lalubar hijabi nayi dan duk mun haÉ—u harda su Umma Safiya da su Binta muna fira.
Hakan da ya gani bai sa ya juya ya fita ba, sai cewa da ya yi "Ina wunin ku." Idanun sa baki É—aya a kaina, sai wani murmushi ya ke sakar min abin haushi.
Takaici da haushi ne ya kama Aunty Zulai, ganin yadda ya kafe ni da kallo kamar tsohon maye. A ranta tace
_Ikon Allah wannan mutumin anya kuwa?_
Ai bata gama tunani ba ta tsinci Muryar shi "Aunty Dan Allah a É—an bamu waje, ina son magana da Matata ina kiran ta tun É—azu bata É—auka ba."
Dukan su kusan daskarewa suka yi a zaune, basu gama mamaki ba suka ga ya nufi gadon ya zauna a gefen Rahamah.
Babu shiri suka tashi a kunyace suka fita, kowa da abinda ya ke saƙawa a ransa, suna mamakin hali irin na mijin Rahamah kamar me motsi a kai.
Banyi zaton rashin tunanin sa zai sa ya iya aikata haka ba, dana san su Aunty Zulai fita za su yi da na riga su fita.
Ban gama tunani ba naji ya kawo hannun sa ya kama nawa. Ji nayi kamar an watsa min wuta, da sauri na fusge hannuna na miƙe tsaye akan gadon na fara ja baya. Da hannu nake nuna shi ina faɗin "Kar ka matso kusa dani, karka taɓa ni bana so.
Shima biyo ni ya yi yana wani mirgina tumbi kamar randa, yana wani lumshe ido cikin ƙasa da murya yana cewa "Dan Allah Rahamah ki tsaya, babu abinda zan miki ganin ki kawai zan yi.
In kuma bakya so anan ki taho mu je É—akina kawai, kinga nan dama ga su Aunty kar su ga na hana su sakewa."
Kallon shi kawai nake, ina jin zuciyata kamar ta faso k'irjina saboda takaici, ikon Allah ni kam wanne irin miji ne wannan? Wa nake aure ?.
Babu zato naji ya rungumo ni ya wani matse ni a jikin shi.
Iya ƙarfina na shiga ƙoƙarin ture shi, sai dai yadda kasan dutse, ko motsi bai yi ba bare yasan ina yi.
Ai ina ganin ya fara ƙoƙarin kai hannun sa wajen zip ɗin rigata, na taƙarƙare iya ƙarfina na gasa masa lafiyayyen cizo a hannu.
Babu shiri ya sake ni, tare da hankaÉ—a ni kan gadon nayi baya na faÉ—i.
Da sauri na miƙe ina gyara zaman rigata, cikin fitar hayyaci nace "Na rantse da Allah in baka fita a nan ba, zan baka mamaki."
Kallon hannun sa kawai ya ke, ya ɗago ya watsa min idanun sa da suka yi wani irin ja, tare da nuna ni da hannun sa yace "Wallahi sai kin biya bashin da kika ci, zamu haɗu dake ne ai baƙin zasu tafi."
Bai ƙara magana ba ya sauka daga gadon, da ƙyar yana nishi saboda tumbin sa.
Da harara nabi bayan shi da kallo, tare da jan tsaki me ƙarfi nace "Mu zuba Ni da kai aga wanda zai yi nasara."
Har ya kai bakin ƙofa, jin abinda nace yasa ya juyo ya sakar min wani irin murmushi, wanda ban san ma'anar shi ba ya fice a ɗakin.
Da sauri na tashi na gyagygyara kan gadon, gudun kar su Aunty Zulai su yi zaton wani abu, nasan ni zai bari da kunya tunda shi ya yi gaba.
Ina cikin gyaran suka shigo, cikin ikon Allah kuma babu wadda tace komai, suka nemi waje kowa ya kwanta da saƙe-saƙe kala-kala a ransa.
Firar da bamu yi ba kenan kuma, da asuba suka shirya suka ce zasu tafi, da ya ke akwai direban da aka ware aka ce zai maida su gida dan haka a farfajiyar gidan muka yi sallama.
Nasha kuka harda birgima, haka suka dinga bani Haƙuri, suka kuma ƙara min da nasiha da ban haƙuri.
Harda cewa sai nayi haƙuri da mijin nan nawa, dan sun ga alamun bai da seti da sauran su. A raina nace _Ni zan faɗa muku bai da seti._
Sauƙin abin ma ina da Aunty Fati, suna tafiya na maza na faɗa sashina na kulle ko'ina na bar makullan a jiki dan bana son ganin wannan mugun mutumin ko kaɗan.
*_🥰MAMAN ÆŠAN ALBARKA CE 🥰âœï¸âœï¸_*
[1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG
*BAƘAR ZUCIYA!.*
*_🥰MAMAN ÆŠAN ALBARKA CE 🥰âœðŸ»âœðŸ»_*
*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLET, GA DUK ME BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*
*PAGE 4ï¸âƒ£*
*AL'AMEN*
Tun lokacin da Rahamah ta cije shi, ya sawa ransa zai nuna mata kuskuren ta.
Amma kuma daya tuna amarya ce, sai ya ga bari ya bita a sannu gudun kar ta botse masa baki É—aya.
Allah-Allah ya ke Æ´an Kaduna su tafi, dan shi har ga Allah Aunty Zulai É—in nan ta bashi haushi, ko ledar daya bata, ya bata ne wai ko zata gane nufin shi ta yi kara ta taso Rahamah.
Sai ta amsa ta rufe ƙofar, in da hakan ya bashi haushi sosai, gashi ita ma Rahamah ta ƙi bari ya ganta kwata-kwata.
Shi yasa ya je har ɗakin ya cire kunya dan ya ganta, shine suka ƙare a faɗa a ƙarshe.
Yanzu ma zaune ya ke a tafkeken farlon shi, wanda ke ainahin gidan shi wanda zasu zauna da Rahamah dake unguwar Mile 12.
Ba ƙaramin girma gidan ya ke da shi ba, dan a ƙalla yana ɗauke da part kusan biyar banda na shi, wanda shi harda bene irin me hawa biyun nan.
Shine a matsayin ɓangaren Al'amen ɗin.
Wani mutum ne kusa da kujerar da Al'amen ke zaune. Fari ne sosai mara jiki, daga kallo É—aya zaka gane asalin bafulatani ne babu sirki.
Sanye mutumin ya ke da riga da wando na wani yadi fari, fuskar shi É—auke da dogon gemu da saje daya cika ta.
Sai irin hirami nan baƙi daya yafa a kafaɗar sa. Idanun sa sanye da kwalli ya yi rau.
Shi kuma Al'amen sanye ya ke da jallabiya ruwan ƙasa (Brown color).
KuÉ—i ne gaban Al'amen dami-dami a wata jaka,
a hankali ya raba jikin sa da jikin kujerar ya turawa mutumin kuÉ—in baki É—aya. Mutumin ya ja jakar ya fara zaro kuÉ—in yana dubawa.
Can ya ɗago ya kalli Al'amen yana jinjina kai, cikin murya irin ta malaman nan ƴan ƙaƙale yace "Masha Allah ai na faɗa maka, ribar wannan satin sai ta linka ribar shekara guda daka samu, gashi yanzu kaima ka shaida tun ba'a je ko'ina ba."
Ya rufe jakar ya miƙawa Al'amen.
Al'amen yana murmushin jin daɗi, ya amshi jakar yace "Wallahi nima na gani tabbas, dan in ba ƙarya nayi ba zan iya cewa, ribar nan tama linka ta shekarar data gabata."
Murmushi mutumin ya yi tare da gyara zaman hiramin shi, ya yi gyara murya yace "To ka gani, Fatana zaka dage sosai akan aikin nan.
In har ka dage zaka ga cigaban daya zarce wannan, amma fa ina mai baka shawara da ka bi a sannu, tunda dai yanzu ne aka fara."
"Ai ba sai ka faÉ—a ba, in sha Allahu duk wani mataki, da sharaÉ—in da ka ce zan bi su kaga ga lada da addu'o'i da zan samu, ga kuma cigaban da nima zan samu."
Cewar Al'amen kenan.
Miƙewa mutumin ya yi yana ƙara gyara zaman hiramin shi, ya kalli Al'amen ɗin yace "Ni zan tafi, duk yadda za ka yi karka ƙara bari a samu matsala, a daren nan komai ya wakana.
Zuwa sati na gaba da kanka zaka zo ka tarda ni gida, ka bani labari akan cigaban da aka ƙara samu."
Yunƙurawa Al'amen ya yi, da taimakon hannun kujerar daya dafa ya miƙe. Ya kalli mutumin tare da nuna masa jakar kuɗin yace "Ka ɗibi abinda zai ishe ka, kafin ka tafi dan anan nake son cire wanda za'a kai masallacin juma'ar nan."
Tsugunnawa mutumin ya yi, ya É—auki dami biyu yana murmushi yace "Wannan ma ya isa, sauran in ka kai masallaci sai ka shigar dasu cikin kasuwanci."
Sai da ya rakashi har bakin motar shi, suka yi sallama yaja motar ne gadi ya buÉ—e masa ya fita.
Cikin hanzari da ɗan gudu-gudu Al'amen ya juya ya nufi sashin nasa. Yasan yanzu baƙin sun tafi, dan sun yi waya da Habu direba, yace sun shirya ɗazu dan dama shi tuni ya riga daya sallame su. Ya bawa Hajiyar sa dubu goma-goma yace a bawa baƙi da zasu tafi su sha ruwa a hanya.
Kuma ya bawa Habu kuÉ—i har dubu talatin ya sai musu abinci a hanyar su ta komawa.
Yana da tabbacin zasu ji daɗin kyautar nan, har ma su ƙara ganin mutumcin sa.
Yana shiga farlon, kai tsaye saman bene ya nufa, yana haurawa ya tura ƙofar ɗakin dake farko dan dama ƙofa biyu ce a saman.
Wani haÉ—aÉ—É—en farlo ne ya bayyana, ya fara takawa cikin hanzari ya nufi bedroom.
Wasu irin haÉ—aÉ—É—un kayan gado ne a ciki, masu shegiyar tsada daga gani ba Æ´an nan bane na waje ne.
Kan tamfatsetsen gadon ya nufa, ya É—auki wayar shi da wasu makullaye.
Har ya juya zai fita a ɗakin, ya tuna wani abu da sauri ya koma ya nufi wata loka, yana buɗewa ya ɗauko wata leda baƙa dake ƙulle. Ya zura ta a aljihun sa, sannan ya jawo ƙofar ya fita ya nufi ƙasa. Kai tsaye daya fito wata haɗaɗɗiyar mota ya shiga ya jata da nufin barin gidan.
A bakin get me gadi na hango shi, ya miƙe a guje ya buɗe ƙofar yana ɗaga masa hannu cikin kirari yana faɗin "Sai Jagaba Jagaban mu maganin kukan mu, na gaida uban gidana maganin kukana, Barka da fitowa Jagaban talakawa."
Yana zuwa daidai inda me gadin ya ke, a hankali ya zuge glas ɗin motar, yana sakin murmushin jin daɗi ya leƙo da kanshi yace "A'a Malam Iliya Barka da safiya, fatan ka tashi lafiya."
Da sauri mai gadin ya ƙara matsawa kusa da motar, yana wani irin washe baki yace "Lafiya lau Jagaban mu, ya kwanan amaryar da baƙi."