Sashe 14
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na kalli gadon sai naga babu Al'amen, duk yadda aka yi masallaci ya tafi.
Na ƙarasa kusa da ita ina bin katifar da kallo, da ya ke gari ya waye sosai, a toilet ɗin farlo na yi alwala sai da na idar da Sallah na shigo ɗakin.
Ganin bargon data kwanta a kai nayi a jiƙe Jagab. _Kenan fitsarin kwance take?_
Na tambaya kaina, nasa hannu naja fillon da ta kwanta akai. Ban san sunan ta ba sai na shiga faÉ—in "Ke ke ke tashi gari ya waye."
Zabure ta tashi yarinya ba sai ta fashe da kuka ba.
Tsayawa nayi kawai ina kallon ikon Allah, na shiga tambayar ta "Lafiya me ya same ki?."
Muna cikin haka sai ga Al'amen ya shigo, ganin ta na kuka ya fara tambayar ta a ruÉ—e idanun shi a kaina.
Ni dai naji Anisa da yace kawai, da alama tambayar ta ya ke, dan da yare ya ke maganar.
Cikin kuka na ji ta masa magana da yarabanci, bansan abinda tace masa ba tunda ba jin Yaren nake ba.
Nayi zaton in yaga fitsarin zai mata faÉ—a, dan in dai ba baya jin wari ba yaci ace tun shigowar shi ya ji warin fitsarin a É—akin.
Sai naga ya kamo ta ya miƙar da ita, jikin ta na ɗigar fitsarin ya kama hanyar toilet da ita yana faɗin "Dan kin yi fitsari shine ki ke kuka, wuce mu je ki yi wanka."
Sai kuma ya canja baki zuwa Yaren su, kamar dai lallashin ta ya ke.
Wata sabuwa kenan, abinda ba zan ɗauka ba kenan kwana da me fitsarin kwance ni da ban ko haihu ba, ace ina shaƙar uban warin fitsarin gardiya.
Ina tsaye sai gashi ya fito, ya kalle ni yace "Ki tattara wajen ki kwashe bargon ki kai baya, anjima in me wanki ya zo sai ya wanke."
Yi na yi kamar ba dani ya ke magana ba, nayi banza da shi na fice a É—akin.
Har farlo ya bini yana magana, "Ba dake na ke magana bane wai Rahamah."
Dakatawa na yi na juyo nace "Wallahi ba zan yi aikin fitsarin kowa ba, ita data yi ta tattara ta fitar wajen. Kuma ta gyara min ɗakina tsaf dan ni bana ciki da ƙazanta."
Ƙwafa ya yi ya juya yana faɗin "Duk abinda za ki yi, ki cigaba da yi Rahamah yarinya ce babu in da za ta fitsari kuma larura ce."
Da kanshi ya É—auke bargon, ya fito da katifar ina kallon shi ya kai waje ya shanya a rana.
Babu jimawa ita ma yarinyar ta fito, ta yi wanka ta canja kaya.
Kallo na take tana wani raɓe-raɓe, na ɗauke kaina na yi kamar ban ganta ba. Tashi na yi na shiga kitchen dan naga lokaci ya fara tafiya.
Breakfast me sauƙi na nema mana, ina gamawa na jere komai na wuce ɗaki.
Gyara É—akin na yi da har lokacin nake jin zarnin fitsarin, haka na goge ko ina nasa turaren wuta dana tsinke da room freshener sai lokacin na ji É—akin ya É—an min dama-dama.
Koda na fito na tarda tuni har sun fara karyawa, sun baje a tsakiyar farlon sunwa gun kaca-kaca babu kyan gani.
Cikin mamaki na ke kallon flarsk ɗin shayin babu basu rage min komai ba, sai iya doyar dana soya Dan ita nayi sha'awar ci shi yasa na soyata da ƙwai.
Ita É—in ma duk sun sa hannu a ciki, haka kawai naji zuciyata bata kwanta da naci ba.
Sai na wuce kitchen Dan na nemi wani abin, dan har ga Allah shi kanshi Al'amen É—in, k'yank'yamin shi nake ji bana jin zan iya cin abin hannun shi.
***
*BAYAN WASU KWANAKI*
A haka rayuwar mu ta cigaba da gudana. kullum Al'amen ƙara fito min da sabbin halayen sa ya ke, waɗan da suke girgiza tunani na.
A hankali na gama karantar shi, duk wasu abubuwan shirka da tsubbace-tsubbace ya iya su, sadaka kala-kala yasha shigowa da jar dawa ya Juye a ƙwarya ya sa kuɗi a kai da goro ya fita da su, wai sadaka zai bada saboda ƙarin haɓakar arziƙin sa.
Yama daina ɓoye min komai yanzu, kai tsaye yake nuna min komai zai iya yi dan neman arziƙin sa.
Duk da lamarin na damuna sosai, amma yadda kuka san wadda ka rufe wa baki nasha yunƙurin faɗawa Aunty Fati, sai na ji na kasa faɗa mata.
Ga matsalar da muke yawan fuskanta a duk sa'ar daya kusance ni, aman nan sai na yi shi ga warin fitsarin Anisa da kullum sai ta tabka shi.
Bisa dole na fara guduwa farlo duk da uban sanyin farlon, daga naga ya yi barci nake guduwa, kuma har yau babu ruwan shi in ya zo yana warin shi yana komai zai kusance ni, bana tantance komai sai wahalar da nake sha.
A hankali na fara rama a tsaitsaye, kullum dare ya yi ina fargabar Al'amen ya matso kusa dani, ga fargabar warin fitsari banda takaicin yadda ya ke gudanar da wasu abubuwan nashi waÉ—anda ke birkita tunani kullum.
Yau gaba ɗaya na tashi jikina babu daɗi, wata irin kasala nake ji haka kawai zuciyata ta dinga tashi. Ko abinci ban iya ɗorawa yau ba, har wajen ƙarfe takwas na safe ina kwance a farlo.
Haka ya dawo masallaci ya tarda ni kwance, ganin ban É—ora komai ba, ba tare da ya tambaye ni lafiya ba? Ya hauni da faÉ—an iskanci ne ya hana na yi musu abincin karyawa.
Na bar marainiya da yunwa waye-waye, maganganun dai kala-kala, Ni dai ina kwance ko É—aga kaina na kasa yi saboda yadda nake jin wata irin hajijiya.
Ina kwance ya fita ya dawo hannun shi ɗauke da ledoji, alamar abinci ya siyo musu dan harda tambarin gidan abincin a ledar. Ba tare da ya damu da ni me zanci na suka zauna suka ci suka ƙoshi, ya ja hannun Anisa suka fita.
Kusan wuni guda na yi a farlon kwance, iya Sallah ce kaÉ—ai ke tada ni na kasa sa komai a bakina.
Ko ruwa nasha haka nake dawo dashi, gaba É—aya na gama galabaita.
Dana ji wuya sai na yanke shawarar kiran Aunty Fati, sai dai na kira yafi sau biyar bata ɗauka ba. Haƙura na yi da kiran na koma na kwanta idanuna na zubar da hawaye.
Wajen ƙarfe huɗu na yamma sai gashi ya dawo, ban ga Anisa ba ko ba tare ya dawo da ita ba.
Duk da ya ganni a yadda ya barni ya same ni, hakan bai sa ya nuna tausayawa ba ko kuma ya tambaya ni me ke damuna ba.
Abincin sa kawai ya tambaya, da ƙyar na iya ɗagowa na kalle shi ganin yadda ya tsaya a kaina kamar me shirin yaƙi, ya wani turo tumbin gaba fuskar shi a haɗe kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa.
Cikin dauriya na buÉ—e baki nace "Banda lafiya ban iya girka komai ba."
Ai kamar wanda na watsawa wuta, haka ya hauni da faÉ—a ta inda ya shiga ba tanan ya ke fita ba.
Wai tsabar rainin hankali ne da wulaƙanci yasa naƙi yin abinci, waye-waye maganganu marasa daɗi ba tare da nuna tausayin halin da nake ciki ba ko kaɗan.
Ƙarshe yace na tashi na shiga kitchen na girka masa abinci, dan shi ba zai yi aure ba ya ƙare a siyan abinci a waje ba da mutumcin sa. Ko da bai yi aure ba bai yi wannan ba, Hajiyar su na masa lafiyayyen abinci ba ma irin kwaɓar mu ta hausawa dana saba masa ba.
Gaba É—aya surutun sa ya ishe ni, nan da nan naji kaina ya fara amsawa, ga shi dama tsayawar da ya yi kusa dani duka warin jikin sa ya addabeni .
Kafin kace meye wannan na fara kelaya amai, tamkar zan amayar da hanjin cikina.
A zato na zai nuna min tausaya, ganin halin da nake ciki. Sai naga yaja tsaki ya juya ya fita ya cigaba da mitar shi.
Gaba É—aya na fara fita hayyacina, sakamakon dama babu komai a cikin nawa iya ruwa kawai nake amayarwa.
Da kaina na lallaɓa na gyara wajen ina kuka.
Na koma kan kujerar na kwanta, nan da nan wani sanyi ya kamani.
Ina jin wayata na ringing, amma na kasa É—auka.
Ƙarshe jin kiran ya yi yawa, na miƙa hannu da ƙyar na ɗauka.
Ganin wadda ke kiran jikina na rawa na amsa.
Ko magana banbari tayi ba, na fashe mata da kuka.
Daga can Aunty Fati tace "Haba Rahamah me ke faruwa ki ke kuka haka? Yanzu na dawo daga unguwa na manta waya a gida, na tarda kiran ki har biyar.
Gabana ya faɗi nace ko lafiya? Ina ƙoƙarin biyo kiran, sai ga kiran mijin ki wai ya ce ki masa abinci kin ƙi masa.
Har da su rashin kunya, yace ya kawo yarinyar Yayan shi ki riƙe bakya kula da ita, ko abincin bakya bata sai ya bata ga rashin mutumci kala-kala kwata-kwata bai isa ya saki ki yi abu ba, sai kice ba za ki yi ba."
Cikin kukan da nake, haÉ—e da mamakin rashin kunya irin ta Al'amen.
Na ce "Wallahi Aunty bani da lafiya ne."
Nan na kwashe komai na faÉ—a mata, tun daga kan kawo yarinyar dake min fitsari da kasa zaman É—akin da nake.
Zuwa yau da banda lafiya yace na yi abinci.
Sai dai na rasa me ya hana na faÉ—a mata maganar shirkar da ya ke, da kuma dukan da ya ke yawan kai min.
Dan abu kaÉ—an nayi, baya shakka ko a gaban waye kai min duka ya ke.
Haƙuri ta bani, ita ma tace bai kamata ba ya kawo min yarinya kamar Anisa mu dinga kwana ɗaki ɗaya, koda kuwa bata fitsari bare kuma tana yi tafi kowa sanin halin k'yank'yami na.
Ƙarshe ta lallashe ni, tace gata nan zuwa gidan.
Babu jimawa sai gata.
Lokacin Al'amen baya gida, ganin halin da nake ciki yasa ta kira shi a waya tace ya zo tana son ganin shi.
FaÉ—a sosai ta rufeni da shi, akan me ya hana tun farko ban kira ta ba.
Haƙuri na bata nace na yi zaton zai daina.
Ba'a wani ɗauki lokaci ba, sai gashi ya dawo, tiɓi-tiɓi hannayen shi riƙe da ledoji.