← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 22

Sashe 13

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aje Kamal na yi muka rungume juna, cikin dariyar farin ciki nace "Gamu kam Aunty Fati."
Taja hannuna muka zauna bakin gado, ta fita ta dawo hannun ta É—auke da filet da ruwa da lemo me sanyi.

Bayan nasha ruwan na cire É—ankwalina ina gyara zama na kan gadon ta, ina bin É—akin nata da kallo nace "Wai Aunty kayan É—aki ki ka canja?."

Tana dariya tace "Wallahi kam ai tun kafin bikin ki, Abban Kamal ya canja min baki kula da kujerun farlon ba kenan?."

Girgiza kai na yi ina jin daɗi a raina, haƙiƙa Aunty Fati ta yi sa'ar mijin aure. Yana matuƙar son ta yana kyautata mata sosai, baya barin ta ta yi kuka akan komai, duk wani abu na jin daɗin rayuwa yana ƙoƙari wajen ganin ya wadata su da shi.
Koda ina budurwa ina sha'awar rayuwar su, gwanin burgewa ba zaka taɓa jin kan su ba.
Sai na ji dama nima haka na yi sa'ar miji kamar ta, ai da na more bani ba kuka.

Cikin farin ciki nace "Allah ya sanya alkhairi, wallahi kuma naga farlon ya canja min fa, Allah dai bai bani ikon in lura da kujerun ba."

Tashi muka yi muka nufi farlon, na dudduba tsadaddun kujerun har Tvn bango Ya canja babba ce yanzu, na musu addu'ar Allah ƙara masa buɗi na alkhairi.
Ta amsa da Amen.

Sallamar me gadin ta ita tasa muka juya, sai lokacin na tuna da Al'amen nake tare.
Cewa ya yi wai Al'amen yace ya na neman iso.

Salati Aunty Fati ta fara tana tafa hannu idanun ta a kaina tace "Ke yanzu dama tare ku ke? Ki ka shanya bawan Allah a waje baki ce na shirya ya shigo ba."

Turo baki na yi gaba murya a shagwaɓe nace "Ni fa murnar ganin ki ce tasa na manta da shi."

Dungure min kai ta yi ta nufi É—aki tana faÉ—in "Ina kin ga dama ki je ki shigo da shi."

Ina ɓata rai ina komai na fita, a bakin ƙofar farlo na tsaya na ɗaga muryata da ya ke ina hango su nace "Wai ka shigo."
Na juya na koma ciki abina, Aunty Fati ce ta fito sanye da hijabi.

Sai gashi shima ya shigo da sallama, hannun sa cikin na Kamal Yana wani sunne kai kamar na Allah.

Zama ya yi kan kujerar, ya gaida Aunty Fati harda yin ƙasa da kai a zuwan girmamawa, yana wasa da Kamal daya haye cinyar sa.
Shiru muka yi duka, Aunty Fati ta kalle ni ta banka min harara tace "Tashi ki kawo masa ruwa da lemo."

Ba dan bana so ta gane wani abu tsakanina da shi ba, da cewa zan yi ba zan kawo ba.
Haka na tashi na shiga kitchen na buÉ—e frij na É—auko ruwa da lemon na kawo.
Haka ta maida ni na ɗauko kofi, sai da na zuba masa tukun ta ƙyale ni.

Ruwan yasha kawai, ana jimawa ya miƙe yace "Zamu tafi."

Kallon shi na yi nace "Ka je ni ma zan dawo."

Girgiza kai ya yi ba kunya yace "Kin san akwai shirin kayan da za ki yi, ki taso mu wuce tunda kun ga juna."

Mamaki ma nake ganin bai ji kunyar Aunty Fati ba, ina ƙoƙarin yin magana Aunty Fati tace "Ka je ka ɗan jira ta tana zuwa."

Kafin ya fita, ya zaro kuÉ—i dubu É—ai-É—ai ya bawa su Islam.
Ɗaki ta jani ta hauni da faɗan bata Sanni da halin musu ba, ya nake son ɓata wayona abinda bana yi shi zan nawa mijina.
Ganin ranta ya ɓaci na bata Haƙuri, nace mata yau zamu koma gidanmu tunda dama ban faɗa mata ba.

Addu'a ta bini da ita, tare da ƙara bani shawarwari.
Ta haÉ—o min kayan mata da su turaruka da abubuwan da baza'a rasa ba, tace ita ma zata shigo anjima kafin mu tafi.

Har waje ta rako mu, muka tura get muka shiga ina jin zuciyata duk ba daÉ—i.

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_*

[1/18, 07:15] Ummu Sultan Ceh3: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJJOOxsRu8dKh9gocmSFuG

*BAƘAR ZUCIYA!.*

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_*

*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLETE, GA MAI BUƘATA TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*

*PAGE7️⃣*

Bamu tafi ba sai da daddare, na samu rakiyar wasu daga cikin mutanen gidan, sai Aunty Fati daga nawa ɓangaren.

Bata bar gidan ba sai da ta tabbatar ta É—an gyara min wasu abubuwan, duk da ba wani aiki bane tunda an gama jere tuni. Sauran tace da safe Ni ma na gyara.

Ni kaɗai na tsaya ina ƙarewa ɗakina kallo, haƙiƙa ba ƙaramin ƙoƙari iyayena suka yi ba, wajen narka dukiyar su suka sai min kayan ɗaki na gani na faɗa.
Addu'a nayi musu akan Allah ƙara buɗi, ya basu ikon yiwa sauran ƴan baya fiye da haka.

Na cire kayana na nufi
toilet na yo wanka, da ya ke Al'amen ya je maida waÉ—an da suka rako ni.
Nasan kuma zai dawo ko ma yaya ne, dan haka ban wahalar da kaina wajen rufe ƙofar ba na barta a buɗe nayi kwanciyata bayan na gama addu'ar barci na shafa.

Ina cikin barci na ji maganar shi, tashi na yi zaune ina murtsuke ido na. Dan na yanke shawarar na daina nuna tsoron shi, tunda dai banda maganin shi sai Allah, gwara na kwantar da hankalina kawai zai fi.

Kallon shi kawai nake, ganin shi da wata yarinya me kimanin shekara sha uku, wai ya kawo min ita ne ta dinga É—ebe min kewa.
Ƴar wajen Ƴayan shi ce, Allah yawa mahaifiyarta rasuwa, yana fatan zan riƙe ta amana, kuma bai kawo ta dan na dinga sata aiki ba, iya karatu kawai za ta yi a hannun mu, yana son ace shi ya aurar da ita da hannun sa sakamakon zumuncin shi da ɗan uwan sa.

Kallon shi kawai nake lokacin da ya ke maganar. Har zan ce ba zan riƙe ta ba, sai kuma nayi tunanin ai ba yarinya bace zata iya yiwa kanta komai, sannan ni ba aiki zan sa ta ba ba komai ba,
to me zai dame ni da har zan ce ba zan riƙe ta ba.

Ce masa na yi shikenan kawai, madadin naga ya kaita É—aya daga cikin É—akunan dake farlo.
Sai naga ya fita ya kinkimo wata katifa Æ´ar madaidaiciya, wadda ban san ina ya samo ta ba, ya aje katifar a tsakiyar É—akin.

Ni dai ina ta kallon ikon Allah, ya kalle ni yace "Rahamah bani zanin gado É—aya na shimfiÉ—awa yarinyar nan."

Tashi na yi na zauna na
kalle shi nace "Wai me kake nufi, ba dai a É—akin nan yarinyar nan zata kwana tare damu ba?."

"A ina ki ke so ta kwanta to? ko so ki ke na barta a can É—akin ta kwana mu muna nan kwance bayan amana ce ita gare mu."
Al'amen yace hakan yana wani zazzaro ido.

Ita kam yarinyar tana tsaye wajen madubi na, tana kallon mu.
Cikin rashin damuwa nace "Amanar ka dai ba tawa ba, dan ni babu ruwana da ita Wallahi, kuma banga ta inda aka taɓa haka ba, yarinya kamar wannan kace ta kwana ɗaki ɗaya damu. To ai wannan ko ƴata ce Wallahi ba zan kwana da ita ɗaki ɗaya ba"

Cikin fusata ya shiga magana "To Wallahi sai dai ki yi duk abinda za ki yi, amma tabbas tare zamu kwana da yarinyar nan."

"To kwa bazan bada zanin gado na a shimfiÉ—a ba, kwana kuwa in ka ga dama ka kwanta kusa da ita ku yi barcin tare, tunda dai ba a gadona zata kwanta ba ai da sau.."

Jin saukar wani gigitaccen mari a fuskata ya hana ni ƙarasa maganar, idanuna cike da hawaye na ɗago ina kallon shi hannu na dafe da kumatuna. Ban san lokacin da ya ƙaraso wajena ba, bare in san sanda ya ɗaga hannun shi, iya marin kawai na ji.

"Ni ki ke faɗawa magana haka Rahamah?." Ya shiga nu na ni da hannu cikin kakkausar murya "Wallahi daga yau duk ranar dana ƙara magana, ki ka tsaya kina musu da ni sai na miki abinda baki taɓa zato ba, mara kunyar banza da wofi. Yarinya kuma anan zata kwanta, ba bu in da za ta je." Yana gama faɗin haka ya juya ya fice a fusace.

Ni dai ina zaune na kasa cire hannuna a fuskata, hawaye ne kawai ke sintiri a kumatuna.
Rabon da a taɓa lafiyar jikina har na manta, sai ga shi yau akan abin da bai kai ya kawo ba, wannan azzalumin ya ɗaga lafcecen hannun shi ya mare ni.
Ina zaune ya dawo hannun shi ɗauke da ƙaton bargo, da alama na shi ne ya ɗauko mata.

Haka ya shinfiɗa ya kamo hannun ta kamar ƙaramar yarinya, yace ta kwanta tayi kwanciyar ta abinta.

Babu jimawa shima ya hawo gadon, lokacin tuni na gaji da zaman na kwanta, har lokacin hawaye basu daina zuba a idanuna ba.
Ni kaÉ—ai nasan halin da zuciyata take ciki.

Ina jin shi ya jawo ni jikin shi ya shiga yin abinda ya saba, ko tari ban yi bare na hana shi yadda kuka san gawa haka na koma. Ina jin shi yana ta faman jan tsaki bayan ya gama abinda zai yi.
Ya koma gefe ya kwanta, sai tashin munsharin sa da naji.

Aman dai dana saba sai da nayi, ban yi barci ba tsahon daren baki É—aya, kuka ne na yi shi har sai da naji idanuna na min zafi.
Wajen ƙarfe huɗu na tashi nayi wanka na ɗauro alwala.
Saboda katifar da ya aje babu inda zan shinfiÉ—a abin sallah, sai kawai na fice na koma farlo na tada Sallah.
Raka'a biyu nayi barci ya ci ƙarfina, sama-sama nayi addu'a na rarrafa kan kujera sai barci.

Ina shiga É—akin naji wani uban zarni ya daki hancina, hannu nasa na toshe hancin na shiga bin É—akin da kallo.
Idanuna na sauke akan yarinyar da har yanzu bata ta shi ba, barcin ta take hankali kwance.
Chapter 13 · 0% Book details