← Book details Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 22

Sashe 2

Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba É—aya hankalin mutanen dake tsakar gidan ya dawo kanmu, aka min caaa ana hayaniya irin ta gidan biki.
Kaina sunkuye ya ke, ta cikin mayafin nake kallon kyawawan ƙafafuna waɗanda suka sha zanen jan lalle, a hankali nake taka tsakar gidan mu dasu.
Zuciyata cike da wata irin fargaba, ji nake duk taku ɗaya in na ƙara, tamkar ina sake nesantar ƴan uwana ne.

Kai tsaye ɗakin Ammimu suka nufa dani, cikin hayaniyar mutanen dake binmu a baya, muka sa ƙafa a ɗan madaidaicin farlon Amminmu wanda ke cike da baƙin ƴan biki.

Zuciyata na wata Iriyar rawa lokacin da Aunty Zulai ta zaunar dani a tsakiyar mutanen, Amminmu na gefe a zaune cikin shigar atamfa riga da zani, irin shiga dai da iyayen amarya ke yi tamu ta gargajiya.

Da ɗai-ɗai suka shiga min nasiha akan haƙuri da zaman aure, da biyayya da ga mijina da yadda zan rungumi kowa nashi tamkar dangina.
Kar na sake na nuna banbanci ko wani abu da zai sosa masa rai, ga ƴan uwan shi ko wani wanda ya raɓe shi.
Sosai aka min nasiha, har ban san lokacin da wani k'akk'arfan kuka ya ƙwace min ba.

So nake Naji Ummanmu ta tofa albarkacin bakin ta, amma sai na ji tace wadda suka min ma ta isa, in sha Allahu tana fatan na É—auka na kuma yi amfani da ita.
Ita bata da abin cewa, fatan ta Allah ya bamu zaman lafiya, ya kaÉ—e fitina, ya bamu zuri'a É—ayyaba, ya bani ikon yiwa mijina biyayya.

Dai-dai lokacin da suke shirin tashi tsaye dani mu fita naji hayaniyar angwaye, ga kuma an turo wai Abbanmu ya dawo yana farlon sa yana jiran mu.
Ai ina ganin mun miƙe, na fusge a guje nayi kan Ammimu, na faɗa jikinta tare da fashewa da wani irin kuka mai taɓa zuciya.

Ita ma rungume ni tayi kawai, ta kasa magana sai É—an bubbuga bayana da take a hankali.
Gaba É—aya sai muka bawa Kowa dake É—akin tausayi.
Kowa sai jikin sa ya yi sanyi, haƙiƙa rabuwa da iyaye ba abune me sauƙi ba, musamman mahaifiya, babu wanda zai san hakan sai wadda suka shaƙu matuƙa da mahaifiyar ta.
Irin shaƙuwar da muka yi da Amminmu, kai ko da baki shaƙu da mahaifiyar ki ba, rabuwa ba wasa bace.
Wata irin shaƙuwa ce me matuƙar shiga rai tsakanina da Amminah, duk wanda ya ganni ni da Amminah, sai mun bashi sha'awa saboda yadda bata iya ɓoye soyayyar ta gare ni, haka nima bana iya ɓoye tata soyayyar.
Ba alfahari ba duk gidanmu suna ji dani, daga kan mazan har matan kowa ya samu abu sai dai ka ji yace Rahamah. Allah ya min baiwa ta saurin shiga rai.
Ban sani ba kodan ni É—in banda damuwa da komai, ban raina kowa cikin yayuna ba kamar yadda ya ke tarbiyyar gidan mu, haka duk abinda na samu to ba zai rufe min ido har na hana É—an uwana ba, Æ´aÆ´an yayuna kullum cikin hidimta musu nake.
Ina zaman lafiya sosai da kowa, shi yasa aurena ya zama daban a cikin gidanmu, duk da ba'a kaina aka fara auren nesa ba, dan Aunty Fatin mu ita ma Lagos É—in take aure, a dalilin zuwa ziyara wajen tane ma Allah ya haÉ—a ni da mijin da ya aure ni me suna Al'amen.
Kuma unguwar mu da tasu babu wani nisa, dan haka kowa kewa Aunty Fati murnar ta samu Æ´ar uwa kusa tunda da ita kaÉ—ai ce.

Ganin kukan nawa ba mai ƙarewa bane, gashi har angwayen sun nemi izinin shigowa.
Hakan yasa Aunty Zulai dake share hawayen tausayi, tsugunnawa kusa dani a hankali cikin lallashi ta ɗago ni, ta shiga bani haƙuri tare da cewa Amminmu "Ku yi haƙuri Ammih, zamu tafi addu'ar ku kawai mu ke buƙata."
Da ya ke ita ma Ammih take kiran Amminmu.

Ita kanta Amminmu dauriya kawai take, a hankali tasa hannu ta share hawayen da ya ciko idanun ta.
Ta jinjina kai tare da zare hannunta cikin nawa, ina ƙoƙarin ƙara kamata Aunty Jamila ta ƙaraso ta kama ni, Ina kuka ina komai suka fito dani daga ɗakin Ammin, suka nufi ɗakin Mama Hajara dani.

Kamar yadda aka kaini wajen Amminmu, haka aka kaini farlon Mama Hajara. Cikin sanyin ta ta shiga min nasiha me ratsa zuciya, daga ƙarshe muka rungume juna ita harda kukan ta, dan ita macace da kuka baya mata wahala, gata da kirki da mutumci bata taɓa nuna mana banbanci tsakanin mu da ƴaƴan ta ba.

Cikin kukan suka kama ni, muka nufi farlon Abbanmu dake hanyar zaure, kamar yadda kuka sani ana yi in an fito da amarya, bayan mu zugar yara ce Æ´an biki, har ma da wasu daga cikin manyan, sai da zamu shiga aka dakatar da su.

A hankali na zauna kusa da ƙafar Abbanmu dake kan kujera, idanuna kan lallausan carpet ɗin dake malale a tsakiyar farlon, Allah shi kaɗai yasan me ke zuciyata.
Sai yau nake tambayar kaina, ashe dama haka ake ji in za'a rabu da iyaye? Ba zan manta ba lokacin da za'a kai Aunty Fati Lagos, har da Ni a masu mata tsiya ganin irin kukan da take, duk da nima nasha kukan dana ga za'a tafi da ita É—in da gaske.
Amma da farko kallon wasa nawa abin, ashe ita tasan me taji.

A hankali naji sallamar Yayuna suna shigowa, da É—ai-É—ai da É—ai-É—ai.
Dukanmu yaran gidan, manya da yara mun hallara.

Sunana da Abbanmu ya kira, shi yasa na É—an daidaita muryata, cikin sanyin da dashewar da ta yi na amsa da "Na'am Abba."

A hankali ya yi gyaran murya yace " To Rahamah yau cikin hukuncin Ubangiji an É—aura auren ki. Alhamdulillahi ina godiya ga Allah daya nuna min ranar dana aurar dake lafiya, duk da ba a kanki na fara aurar da Æ´aÆ´ana ba.
Amma ina jin farin ciki bisa ga rabuwar da zamu yi lafiya cikin aminci!.
Haƙiƙa bana jin ki Rahamah, ina miki Kyakykyawan zato bisa ga tarbiyyar da muka baki, da kuma kyawawan halayen ki da kowa ya san ki dasu.
Ina fatan zaki ƙara akan yadda na sanki, ki linka haƙurin ki ya fi nada, nutsuwar dana sanki da ita ki linka ta, ladabin ki da biyayyar ki da rashin ɗaukar komai ba komai ba, duk ina fatan zaki linka su sufi nada.
Saboda wannan zaman da zaki je, ba kamar zaman da ki ke a gidannan bane, zama ne na ibada, wanda baya yiwuwa sai da haƙuri da ladabi da biyayya."

Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, ya cigaba da magana "Rahamah a matsayina na mahaifin ki, ina umartar ki da kiwa mijin ki biyayya, matuƙar hakan bai saɓawa Addini ba, ki mutumta shi ki girmama shi, ki sani aljannar ki na ƙarƙashin ƙafar sa, sai kin kyautata masa kin masa biyayya sannan zaki samu aljanna.
Kada ki kasance me jayayya da shi, ko yawan ƙorafi da mita, ki zama me ɗauke kai akan komai ki maida komai ba komai ba.
Kar ki zama me É—aga murya gare shi, Allah baya son hakan, duk matar da ke É—aga murya sama data mijin ta, hakan babban zunubi ne Rahamah.
Ki zauna lafiya da shi, dan ace shima mutumin kirki ne, bashi da matsala da kowa kowa ya shaida shi, dan Allah karki bari na ji matsala ta fito daga ɓangaren ki.
Ina roƙon Allah ya baku zaman lafiya, ya kauda shaiɗan a tsakanin ku, ya baku zuri'a ɗayyaba me albarka."
Yasa hannu ya dafa kaina, ya jima yana min addu'o'i Sannan ya É—auke hannun sa.

Sosai nake kuka harda shashsheka, babu wanda ya hana ni yi, sai ma wasu daga cikin su dake share hawaye.
Haka Yayan Abbanmu shima ya shiga ta shi nasihar, a ƙarshe ya kira sunan Aunty Fatin mu yace ta matso kusa.

Tasowa ta yi ta ƙaraso kusa dani kamar yadda ya umarce ta, da kanshi ya taso ya kama hannuna ina kuka ina komai, ya kama hannun Aunty Fati ya haɗa.
Nan ya shiga mana nasiha tare, akan mu riƙe junanmu, mu zauna lafiya da junanmu in girmama ta, in ɗauke ta tamkar uwa gare ni.
Duk wata damuwa ko shawara da zan nema, kar na sake na tunkari wata ko wani, na nemi Ƴar uwata na faɗa mata, zata bani shawara.
Har ya min misali da ita akan shekarar ta goma sha a gidan miji, amma mijin ta bai taɓa kawo ƙarar ta ba, haka ita ma bata taɓa kawo ƙarar sa ba, yana alfahari da Aunty Fati duk cikin ƴaƴan gidanmu ta fita zakkah tanan.
Nima yana so nayi koyi da ita, na zama mace ta gari ga mijina.

A ƙarshe ita ma yace amana ta na hannun ta, ta riƙe ni tamkar ƴar data haifa, ta nuna min kuskurena in nayi, in wani abu ya taso ta tsaya min tamkar yadda su zasu tsaya min in suna kusa dani.
Ƙarshe aka rufe da nasiha akan zumunci, aka yi addu'a a gurguje sakamakon cewar da aka yi angwaye sun fara shigowa.

Haka kowa ya tashi jiki a sanyaye, saboda yadda hayaniyar tayi yawa, sai ta ƙofar baya suka bi dani muka koma ɗakin mu na ƴammata.

Nan na tarda ƙawaye na zazzaune, mutum biyu ne kaɗai zasu bini a cikin su.
Amira sai Binta. Binta ita ce babbar ƙawata kuma Aminiyata tun yarinta, mun yi wata Iriyar shaƙuwa da ita wadda har ta kai watarana tana kwana gidanmu, kasancewar ita Allah yawa Mahaifiyar ta rasuwa, a hannun matar yayanta take da zama.
Ba wani wahala take sha ba, aiki ne kawai take mata.

Ganina duk sai suka miƙe tsaye cikin hayaniya irin ta ƙawaye, Aunty Zulai da basu san tana bayana ba, tana shigowa ɗakin ya yi tsit kowacce ta fara magana ƙasa-ƙasa.
Sun riga da sun san halin ta, bata son raini da shirme kwata kwata bata shiri da Binta ƙawata.
Dan in da son ranta ne, ba zan yi abota da Binta ba, a cewar ta yarinyar bata da tarbiyya ta cika rawar kai da feleƙe da iyayin tsiya.

Basu gama tunani ba kuwa, aikwa ta daka musu tsawa tace "Duk ku fice ku bamu guri Muna son magana."
Chapter 2 · 0% Book details