Sashe 1
Bakar Zuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*BAƘAR ZUCIYA!.*
*_True life story_*
*_🥰MAMAN ÆŠAN ALBARKA CE 🥰âœï¸âœï¸_*
*_LITTAFIN KOWA YAƘI JI YA KAMMALA COMPLETE, GA DUK ME BUKATA TA TAMIN MAGANA TA WANNAN NUMBER 09014644247_*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.*
*Allah yadda ka bani ikon fara rubutu nan lafiya, ya Allah na roƙe ka ka bani bani ikon kammala shi cikin aminci. Ya Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar musulmai.*
*Wannan labarin ya faru a gaske, labarine ya wanda ya faru akan wata baiwar Allah. Ban fara rubuta shi ba har sai da ta bani izinin rubuta shi. Saboda haka duk wani abu da kuka ga ya zo ciki tabbas abu ne ɗaya faru a gaske. Sai ɗan abin da baza'a rasa ba, wanda na ƙara saboda yanayin labari dan ya tafi yadda ake so, sai canjin suna da gari da sunaye. Ban amince a juya shi ta kowacce siga ba sai da izinina.*
*PAGE1ï¸âƒ£*
Hayaniya ce take tashi ta ko'ina, a cikin É—an matsakaicin tsakar gidan, yanayin mutanen dake kai kawo kawai zaka kalla kasan akwai wata hidima da ake gudanar wa, dan mata ne cike da gidan, kowacce sanye cikin kayan anko taci kwalliya ta dai-dai iyawar ta.
Wata mace ce tsaye bakin ɗan madaidaicin banɗakin dake gefen zauren gidan in ka shigo, wadda a ƙalla ba zata haura shekara talatin da biyar ba zuwa da shida.
Ita ma sanye take cikin kayan ankon, tasa hannayen ta biyu a cikin aljihun doguwar rigar dake jikin ta. Sai da ta kalli tsakar gidan ta kuma kallon banɗakin tare da jan dogon tsaki. Ta matsa jikin banɗakin tare da kara bakin ta a ƙofar tace "Wai Rahamah me kike tun ɗazu baki fito ba, kowa ya kammala shiri ke kin wani shige ban ɗaki sai kin ja mana faɗa wajen Baba. Gashi waje ba kusa ba, salon rana ta yi."
Wata mata ce ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakuna ukun dake jere, tana ƙoƙarin sa takalmin ta take kallon matar dake tsaye bakin banɗakin tace "Wai Jamila kina nufin har yanzu yarinyar nan bata fito ba, sai kace me shirin canja fata, wanne irin wanka take haka wajen awa guda."
Ta ƙarasa maganar dai-dai lokacin data ƙaraso wajen Aunty jamilar.
"Ke ma dai kya faɗa Aunty Zulai, ki zo dai ki mata magana da kanki ko zata ji taki, Wallahi na fi minti goma ina magana yarinyar nan ta yi biris ta ƙyale ni, Kuma banji alamun wanka take ba, tunda banji motsin ruwa ba."
Cewar Aunty Jamila kenan, tare da matsawa Aunty Zulai ta ƙarasa bakin banɗakin.
Ni kam ina jin su duk maganganun da suke, kuka na nake sha kawai.
Asalima tunda na shiga toilet ɗin, ban cire ko zanin jikina ba bare na kai ga wankan, ina tsaye ina sharɓar kukana, zuciyata cike da fargabar da tsoron rabuwa da iyayena.
Yanzu Shikenan ina wankan nan, in na fito na shirya zasu ɗauke ni su kaini can wata uwa duniya, Shikenan sun raba ni da ƴan uwana, sun raba ni da Abbanmu da Amminmu masu sona da ƙauna ta.
Sun rabani da Aunty Zulai ɗina me gudun ɓacin raina, sun raba ni da Aunty Kairat wadda duk wuya duk daɗi muna tare muyi faɗa mu shirya.
Haka duk zan barsu na tafi da sunan aure, Ya Allah. In har na tuna uwa duniyar da za'a kaini, sai na ji tamkar n fito nace musu na fasa auren baki ɗaya a barni na zauna cikin ƴan uwana, amma babu hali nasan yanzu haka an riga da an ɗaura auren, auren da nake jin sa wani irin banbarakwai, Ni ba farin ciki ba Ni ba baƙin ciki ba.
Gani nan dai kawai za'a ce.
Jin yadda Aunty Zulai ke bugun ƙofar yasa na had'iye kukan nawa, cikin dashshsiyar murya nace "Gani nan Aunty."
Daga can waje taja tsaki ta ƙara buga ƙofar cikin faɗa tace "Na rantse da Allah Rahamah in baki fito ba, da kaina zan shigo banɗakin in yaso na fito dake. Ya ya zaki shanya mutane suna jiran ki kin wani yi zaman ki, bayan kin san abin dake gaban mu."
Na sani sarai zata aikata, tsaf zata shigo banÉ—akin muddin ban fito ba kamar yadda tace. Dan haka sai na tsugunna na fara kaÉ—a ruwan botikin a zuwan na fara wankan, ko zasu tafi dan bana jin zan fito banÉ—akin nan yanzu.
Hakan kaÉ—ai ne nake gani a matsayin mafaka, kafin su tilasta Ni na fito.
Kallon Aunty Jamila aunty Zulai tayi tace "Mu je mu jira ta, kin ga yanzu ta fara wankan tsabar ta raina mu."
Suna shirin juyawa, sai ga wani dajjito Kyakykyawa baƙi wanda a ƙalla ba zai haura shekara sittin ba, ya shigo sai baza babbar rigar shi ya ke tare da amsa gaisuwar matan dake zazzaune a hanya.
Hango su Aunty Zulai da ya yi, ya ratsa tsakiyar matan yana faÉ—in "Ina Rahamah ina fatan dai kun shirya? Dan kun san babu lokaci yanzu angwayen zasu iso."
"Baba za dai mu shirya É—in mu mun gama, amma ita Rahamah tana banÉ—aki tana wankan."
Sai da ya gyara zaman babbar rigar shi, sannan yaja tsaki cikin faÉ—a-faÉ—a yace "Ya kika bari haka ta faru Zulai? Kin fa riga da kin san yanayin tafiya yanzu, hanya babu kyau bana son ku yi shigar dare, nafi son duk abinda za ku yi ku yi kafin mota ta zo, shi yasa na baro wajen É—aurin auren na dawo."
Sauke kai Aunty Zulai tayi, cikin ladabi Muryar ta a ƙasa tace "Ka yi haƙuri Baba in Sha Allahu yanzu zamu gama."
Juyawa ya yi, yana faÉ—in "Kun dai ji abinda nace muku."
Ya fice daga gidan baki É—aya.
Ai tun lokacin dana ji muryar Baba Usman, tuni na fara wankan cikin sauri, dan na riga dana san halin shi sarai, bashi da sauƙi baya son ɓata lokaci akan komai, komai nashi cikin gaggawa ya ke gudanarwa baya son jira da shirme.
Baba Usman wa ne a wajen Abbanmu, uwar su É—aya uban su É—aya, shi ne waliyyin dake É—aura auren yaran gidanmu.
Mutum ne me mutumci da son zumunci, yana da son Ƴan uwan shi Sosai.
Sai dai yana da zafi, baya É—aukar shirme da shashanci ko kaÉ—an.
Allah bai bashi haihuwa da yawa ba, Ƴaƴan shi uku kawai, Aunty Zulai sai Labaran, sai kuma Abdullahi.
Saɓanin gidan mu, Abbannmu me Suna Malam Kabir, yana da mata biyu, Mahaifiyar su Aunty Jamila ita ce babba. Sunan ta Hajara, muna kiran ta da Mama. Ƴaƴan ta biyar, Zainab ita ce babba, sai mai bi mata Yaya Yusuf, sai Yaya Musa, sai Khalid shine Sa'ana, sai autar su ita ce Bilki muna kiran ta da Ummi.
Sai ɗakin mu, Majaifiyar mu sunan ta Sa'adiyya, muna kiran ta da Ammi. Mu bakwai ne a ɗakin mu, Babban Yayanmu sunan sa Abubakar, sai Ya Mudassir, sai Aunty Khairat, sai Aunty Fati, Sai Yakubu daga shi sai ni Rahamah, sai kuma ƙaramar ƙanwata Aminatu.
Wani uban bugu da akawa ƙofar banɗakin, shi ya dawo dani daga tunanin dana tafi.
Firgigit na ɗago na kalli ƙofar.
Muryar Umma Safiya ce ta ratsa kunnuwana, ƙanwa ce a wajen mahaifiyar mu, cikin faɗa take faɗin "Wai Rahamah kin raina mutane ne, tun ɗazu ke ake jira fa, ke komai naki sai kin sa shashanci a ciki."
Ai da sauri na É—aga botikin ruwan, na juye a kaina dama na gama wankan tuni.
Ɗaura zani nayi na zura ƙaramin hijabana, na Turo ƙofar na fito.
Yadda na tarda su tsatstsaye a bakin ƙofar, kamar irin masu jiran wani sarki ko me muƙamin nan, sai da abin ya so bani dariya dan dai kawai bana cikin yanayin da zan yi dariyar ne.
Yadda naga kowacce na jefo min harara, yasa ban tsaya ba cikin sauri na sunkuyar da kaina, na ratsa tsakiyar su na wuce na nufi É—akin mu.
Mutanen dake tsakar gidan na ganina, suka fara min kirari irin na amare, musamman abokan wasa.
Da sauri na faÉ—a É—akin Mama Hajara, dan dama anan nake gudanar da komai na, sakamon irin haÉ—in kan da iyayenmu suke da shi, sam basa irin kishinnan na jahilci, suna mutumta juna sosai, haka muma yaran baki É—ayanmu kanmu a haÉ—e ya ke. In ba'a faÉ—a maka ba, ba zaka iya banbance Æ´an É—aki É—aya ba, saboda kusan duk kamannin Abbanmu muka É—auka.
Shi yasa tun da aurena ya taho, ban wani bawa kaina wahalar zuwa wani waje daban ba, a cikin gidanmu na gudanar da komai na, dama walima ce kaÉ—ai na yi tun jiya, bayannan banyi komai ba.
Bakin gado na tarda Mama Hajara, ganin shigowata yasa ta kalle ni, cikin sanyin Muryar ta wadda a haka halittar ta take tace "Yanzu ke dama baki yi wankan ba sai yanzu Rahamah? Me yasa ke komai bakya É—aukar shi da muhimmanci ne?."
Bance komai ba, na wuce wajen akwatin kayana, zuciyata cikin wani irin yanayi me nauyi, gani nake kawai kowa ya gaji da ni ne, gaba É—aya sai faÉ—a suke min akan na shirya na shirya sai kace basa sona dama.
Ita ma Mama Hajara tun maganar ta ta farko, da taga nayi shiru bance komai ba, tasan ba magana zan yi ba kenan.
Shi yasa bata ƙara cewa komai ba, ta tashi ta fita daga ɗakin.
Aunty Jamila da Aunty Zulai ne suka shigo, nan suka tsaya a kaina har sai da na shirya, cikin lafiyayyiyar atamfar Vlisco me laushi, wadda aka wa lafiyayyen É—inkin riga da zani, kayan sun zauna kamar a jikina aka É—inka su.
Aunty Jamila da kanta ta amshi É—an kwalin, ta É—aura min shi irin É—aurin simple É—in nan bai cika hayaniya ba.
Daga nan suka ɗauko lafiyayyun turaruka, bayan sun gama feshe ni sun bani na shafawa dana gogawa duk ko ina ya ɗauki ƙamshi.
Suka É—auko babban mayafina, wanda ya dace da kalar kayan, suka lullu'ba min shi.
Aunty Zulai ta kama hannuna, ta jani zuwa tsakar gidan Aunty Jamila na bin mu a baya tana sakin guÉ—a.