← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 46

Sashe 9

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dare ne ya tsala sosai ban da kukan tsuntsaye da na ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, cikin sanɗa da ɓadda-bami take tafiya a hankali tana waige don kar wani ya ganta har ya fahimci abin da yake tafe da ita. Kamar yadda ta saba a duk daren da take neman biyan buƙatarta haka ta tunkari tsaunin Boka Mai zamani, kamar yadda ya ga zuwanta a cikin ƙoramar sihirinsa haka ya ji takunta zuwa kogon dutsensa. Tun daga bakin ƙofa Boka Mai zamani ya rungume ta a yunƙurinsa na son su fara aikata masha'arsu kamar yadda suka saba duk lokacin da ta ziyarce shi, a hankali ta zame shi daga jikinta tana faɗin, "Sha kundum ta ci gaba da rufa mana asiri dangane da ɓarnar da muke aikatawa Sarki Damina." Boka mai zamani ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya furta, "Wane mutum In ji mutuwa shalelena? Asirinmu ba zai taɓa tonuwa ba don ba na jin wancan sakaran zai iya kusanto da Sha kundum cikin wannan Daular, hasalima rashinta tare da mu shi ne mafi alheri domin na tabbata idan tana yankin nan asirinmu ya gama tonuwa. Yanzu dai ya kamata a baiwa kura ajiyarta." Takawa ta fara yi a hankali tana zame ganyen da ke jikinta daga wanda ya rufe al'aurarta har zuwa na ƙirjinta sannan ta furta, "Ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai ya ke ba mudubina. Indai wannan ne ai ta kwana gidan sauƙi jariri a ɗakin mayya. Amma abin da yake tafe da ni bai wuce kan maganar wancan sakaran Yariman ba, shin maganar da na ji Sarki ya faɗa gaskiya ne zai iya warkewa? Saboda ina ɗagawa Sarki Damina ƙafa ne don na san a halin da yarima yake ba zai iya mulkar Daular nan ba." Boka mai zamani ya ƙarasa wurinta yana yawo da hannunsa a sassan jikinta sannan ya furta, "Tabbas a bincikena matuƙar Sha kundum ta bayyana a Daular nan zai iya warke wa amma da sharaɗin sai an bankaɗo sirrin da ba kowa ne ya sani ba kuma ba kowa ne zai gan shi ba. Mai wannan ikon yanzu haka ta bar duniya, Mai babbar Turaka ita ce ta san da wannan ɓoyayyan sirrin wanda ko da Sha kundum ba ta dawo daular nan ba matuƙar aka bankaɗo shi Yarima zai warke, yanzu haka gawar Mai babbar turaka na ɗakin yarima na kashe ta ne a lokacin da take ƙoƙarin sanarwa da Yarima sirrin ɓoyen da bankaɗe shi ba alheri ba ne a game da ke, ni kuma duk abin da zai muzanta shi zan iya kawar da shi. Sarki Damina yana kallonki a matsayin mahaifiyar Yarima alhalin Hasana ita ce Mahaifiyarsa kece Usainarta, Ko kin san har gobe Mahaifiyar Yarima tana raye a faɗin duniyar nan? Ko kin san Yarima ba shi kaɗai ne Ɗan da Sarki Damina ya mallaka ba? Ko kin san ƴaƴan Sarki Damina Uku ne a faɗin duniya? Idan bacci kike ki farka domin a duk lokacin da Damina ya gano kece kika nemi salwantar da rayuwar yarima da mahaifiyarsa na tabbata kashinki ya bushe. Ki yi duk abin da za ki yi ki nemo tagwayen jarirai ki kawo min domin na cika miki wani aiki da su idan ba haka ba komai zai iya faruwa, kuma ki tabbata jariran sun fito daga cikin jinin Maharba domin har gobe jininsu na tasiri akanmu tun da sune suka yi galaba a kan mu a lokacin da mummunan al'amari ya faru da Sarauniya Shakundum." Jakadiya da tun shigar Mai ɗakin Sarkin Damuna take laɓe a ƙofa ta riƙe bakin cikin mamaki, a hankali ta furta, "Tabbas Usaina ta cika tattaciyar marar imani amma na yi rantsuwa da Sarauniya Sha kundum da mulkinta sai kwaɓarta ta yi ruwa, a kullin fata da burina bai wuce Sarki Damina ya auri Jummai don na tabbata ko da tsiya da azziki sai Jummai ta haihu a gidansa. Jakadiya bata ƙarasa wannan tunanin ba ta hango harshen wutar itace kafin ta yi wani yunƙuri Bayin Sarki Damina suka haske ta da shi, a tsawace babban bawansa ya furta, "Jakadiya Lami me kike yi a wurin Boka mai zamani a talatainin tsohon daren nan duba da kin san haramun ne matuƙar ba a sanar da Sarki Damina wannan ziyarar ba?" Daga cikin kogon dutsen cikin Boka mai zamani da Usaina mai ɗakinsa ne ya kaɗa, nan take zufa ta fara keto musu cikin faɗuwar gaba ta furta, "Halaka ta zo mini matuƙar Sarki Damina ya san da ni a kogon dutsen nan." Kafin boka mai zamani ya yi magana daga cikin rijiyar da gunkin Sarauniya Sha kundum take suka ji wata irin tsawa wacce ta haddasa razanar Jakadiya ta faɗo cikin kogon dutse a hargitse. Ganin haka ya sa Sarki Damina da Fadawansa suka rufa mata baya, don ya kawo ziyarar cikin dare ne sakamakon mummunan mafarkin da ya yi akan Yarima da wata matashiyar buduwa mai ɗauke da kwari da baka a hannunwanta."

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*

©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

Free page 5

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

Daga wurin Abar bauta kowannenmu gida ya zarce don ɗauko makamai da kayan shiga farauta, sai da muka ƙara tsare kanmu da magunguna sannan muka fita wajen gari a daidai matsayar da Mahaifina ya sanar da jama'a za a haɗu domin ya rarraba wuraren da za a tunkara. Ilahirin mutanen da ke wurin maza ne sai mata biyu daga ni sai Dela wacce ta kasance ƙawa ce a wurina kuma aminiya, ta kasance ƙanwar saurayina Goga kuma duk farautar da muke fita kusan tare muke fita. Goha na ganina ya ƙaraso wurina haɗe da kara gorarsa jikin tawa yana faɗin, "Dawa dai Sarauniyar kyawawa, ko yau ko gobe sai daji ya buɗa miki a lokacin farauta." Cikin so da ƙauna na mayar masa da martanin murmushi haɗe faɗin, "Sa'a dai jarumina Abar bauta ta tsarkake duk wuya duk daɗi sai ka kai labari."

Lokacin da muka gama taruwa a wurin Muzuru uban balbela ne ya fara busa ƙaho nan take wurin ya ɗauka haɗe da bushe-bushen hayaƙin magani. Mahaifina ne ya ɗaga gorarsa sama nan take wurin ya yi tsita kowa yana sauraron abin da zai faɗa. Sai da ya kalle mu ɗaya bayan ɗaya sannan ya furta, "Gaisuwa ga zuri'ar Maharba an buga da ku an bar ku. A daka a kirɓa sai gwaza maza kuke gumbar dutse kowar ja da ku na yarje muku ɗan butar nan ku kai shi ƙasa ko da Ubanai yake yawo, wuya a dajin gudundu wuya a hanyar gwiɓau wuya a artabun baƙin daji wuya a ƙasurgumin dajin farautar gumurzin maciji aradu ko wuya ko daɗi sai mun saro kansa don bin umarnin abar bauta." Yana gama maganar cikin haɗin baki muka furta, "A lafiya mazaje sai kai hayaƙi mai sanya hawaye a idanun jama'a ko maza ko mata, sa'a dai cau cau cau Abar bauta ta buɗa mana." Murmushi ya yi ya karyo ganyen ƙafar shamuwa ya murtsuka a cikin wani ƙaton daro wanda yake cike da ruwa. Sannan ya ciro wata ƙanƙanuwar layar da ke wuyansa ya tsoma ta a ciki ya cire, ya fara karanta waɗansu alƙaluman tsafi sannan ya tofa a ciki. Ɗaya bayan ɗaya haka ya riƙa ba mu muna muka sha sannan ya rarraba mu gabas, yamma, kudu da arewa. Mahaifina ne ya fara kukan kura ya wuce gaba sannan mu da karnukanmu muka rufa masa baya kowa ya bi hanyar da aka ba shi umarni ya bi, take ƙura ta turnuƙe wurin cike da rashin tsoro muka tunkari dajin Bawaya dajin da ko mahaifina ya sha ba ni labarin hatsari da sarƙaƙiyar da ke cikinsa. A tarihin garinmu tun kafuwar dajin ba a taɓa samun mutumin da ya shiga dajin ya dawo da ransa ba, hasali duk irin tasirin farautarmu mahaifina ya ba ni labari sama da shekara talatin kenan babu wanda ya taɓa saka ƙafarsa cikin dajin da sunan farauta saboda Abar bauta ta dakatar da shiga dajin, har sai a wannan ranar da ta bayar da umarni farautar macijin.
Chapter 9 · 0% Book details