← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 46

Sashe 22

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥

Muna da bridal package

Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k

Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)

Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k

Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852

Ba ƙaramin ruɗu da tsananin mamaki ya shiga da faruwar lamarin, a saninsa duk rana kamar wannan matuƙar ya miƙa kuka da buƙatarsa ga Sarauniya Shakundum tana share masa hawaye ta hanyar amsar buƙatunsa. Koda ta daina yin magana amma akwai alamun da yake ji na amsar addu'a da roƙon nashi. Miƙe wa ya yi tsam daga wurin da yake ya fara kai kawo a cikon kogon dutsen cikin mamaki, bakin wani baƙin kasko ya tsugunna ya ɗebo garin sihirtacciyar bishiyar kukar da ya taɓa aika wani ɗan autan aljanu ya ɗebo masa a dajin Buzurul-shusu. Barbaɗawa ya yi da zummar ya ga ainihin abin da yake faruwa da Gunkin Sarauniya Shakundum, kasancewar a ƙa'ida idan har Almuru ya yi babu shi babu ziyartar muhallin Gunkinta. A maimakon komai nata ya bayyanar masa sai gani ya yi wutar ta ɗauke, ya gwada haka ya fi a irga daga haka jikinsa ya ba shi tabbas akwai wani sabon al'amari da yake faruwa. Don haka a gaggauce Boka mai zamani ya ɗauko madubih sihirinsa yana karkatar da shi kusurwar kudu ya fara karanta waɗansu irin ɗalasuman tsafi tun bai ƙarasa ba ya ga jini ya ratsa ta jikin mudubin yana ɗiga. Da sauri a jiye saboda sababbun al'amuran da yake gani masu rikita lissafi, ko tunanin me ya yi sai ya sake ɗauko mudubin yana bincike game sauran al'amuran da ke faruwa a cikin Daular. Tamkar an saka masa hoto a majigi haka ya riƙa ganin duk abin da yake faruwa, yana sake karkata mudubin zuwan binciken Sarauniya Shakundum kamar wancen karon haka ya sake ganin jini na ratsowa ta cikin madubi. Yana nan zaune yana ganin abin da yake faruwa sai ganin wata ƙanƙanuwar wuta ya yi harshenta na ratsowa ta tsakiyar madubin, ruwan tsafinsa da ke ƙoƙon baƙin ƙarfe mai ɗauke da waɗansu irin zanen baƙaƙen aljanu ya ɗauko ya watsa. Amma abin da ya sake tsinka hanjin cikinsa yadda ya ga wutar ta taso masa gadan-gadan har sai da ta fara lasar naman jikinsa. A firgice ya riƙa ɗaukan abubuwa yana jefawa don ya samu wutar ta mutu amma kamar ƙara mata makamashi yake yi, babu shiri ya ƙarasa bakin wani gajeren kabari ya ɗebi ƙasar saman kabarin a tafin hannunsa. Nan take ya fara kiran sunayen aljanu, sai da kira sama da goma sannan ya rufe idonsa yana kiran Aljanu Gagare, ya jima yana abu ɗaya sannan Aljani Gagare ya bayyana tare da faɗin, "Me yake tafe da kai a tsohon daren nan ya kai wannan tsoho mai surkulle kala-kala?" Bakin Boka mai zamani na rawa ya furta, "Ka taimaka min Ubangidana Kogon tsafina ya kama da wuta sha'anin Sarauniya yau ya zo da wani irin salo." Yana rufe baki Aljanin ya bushe da dariya mara daɗin saurare sannan ya ce, "Wannan wajibi ne a gare ta domin matuƙar kiɗa ya canja dole rawa ma ta canza. Sarauniyar da ka sani a baya ta bambamta da ta wannan, don haka ka yi takatsantsan wurin tsaurara bincike a kanta idan ba haka ba watarana za ka nemi rayuwarka ka rasata gabaɗaya." Ganin wutar na sake ruruwa ya sa Boka ya ce, "Na ga alama amma ka taimaka min da abin da zan kashe wutar nan ina cikin tashin hankali." Aljanin na jin haka ya ɗiga masa wani yelon ruwa akan ƙasar kabarin tafin hannunsa yana cewa, "Ka murje ta da ƙasar hannunka sosai sannan ka je ka watsa wa wutar, wannan ruwan da ka gani fitsarin ɗan autana ne na lakuta maka shi da ƙasar kabarin can su za su kashe wutar." Da sauri Boka mai zamani ya ƙarasa wurin da wutar take ci, yana watsawa kamar ɗaukewar ruwan sama haka wutar ta ɗauke sai wani irin hayaƙi mai wari da yake tashi a wurin. Daga can gefe Boka mai zama ya zauna yana sauke ajiyar zuciya ya dubi Aljanin yana faɗin, "Lamarin nan ya matuƙar gigita tunanina." Aljanin ya yi dariya mai kama da haniniyar doki sannan ya ce, "Na gaya maka wannan kaɗan ne ka gani matuƙar za ka tsaurara bincike a kan Sarauniya Shakundum." Yana rufe baki ya ɓace daga wurin. Yadda boka mai zamani ya ga rana haka ya ƙarasa ganin darensa idanunsa biyu yana saƙa da warwarar abin da yake daminsa, yau kaɗai ya sake tabbatar da zarginsa na baya. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyaɗa kai sannan ya saki wani shu'umin murmushi ya ce, "Tabbas sai yanzu na fahimci kuskurena. Da alama Shakundum ta bayyana a cikin daular nan kamar yadda bincikena na baya ya nuna min tana gabda ƙarasowa Daular nan. Yanzu zamana a cikin kogon tsafin ba shi da wani amfani domin wacce nake zaune domin ita ta bayyana har ta bar cikin kogon nan, amma kuma zan zuba ido na ga abin da zai ci gaba da wakana a cikin Daular. Matuƙar na ga manyan alamomin da nake zargi tabbas kashina da na Usaina ya kusa bushewa. A zabure boka mai zamani ya miƙe kamar wanda aka tsirawa allura a cikin ido, gaban ƙoramar sihiri ya koma ya tsugunna ya hau binkice game da abin da ya shafi Sarki Damina da ƴaƴan cikinsa.

Ras! Ya ji gabansa ya yi mummunan faɗuwa bisa abin da idanunsa suka yi masa tozali da su, Sarki Damina ya gani ya bayyana sai waɗansu haske huɗu da ke zagaye da su. Daga bangaren gabas ya hangi wani ƙaton haske wanda ya shafe sauran gabaɗaya, hannu ya saka da niyyar shiga halararsa ya bincika alaƙarsa da Sarki Damina amma sai ya ga duhu ya mamaye wurin, duk iya bakin ƙoƙarinsa ya gagara gane abin da yake son gani. Cike da mamaki ya furta, "Kar dai wannan hasken ma yana daga cikin zuri'ar Damina? Kai an ya kuwa haka ba zai taɓa yiwu ba. Ya zame min wajibi na nemi Usaina mu tattauna domin mu samu mafita."
Chapter 22 · 0% Book details