← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 46

Sashe 7

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gab da shiga ɗakin, Mai babbar turaka ta dubi Nalami dogari cikin karayar zuci ta furta, "Ka taimaka ka bar ni ko na taƙi kaɗan ne zan bar musu wasiyyar da ba na son ku buɗe ta har sai bayan babu rayuwata. Jikinsu ne ya yi sanyi duk da kasancewar ba sa daga cikin masu tausayi, ganin tausayi na neman tasiri a zuciyarsu ya sa suka fisge ta da ƙarfin tsiya. Kamar mayunwacin zaki haka Yarima ya kurma wata uwar ƙara haɗe da janyo Mai babbar turaka da ƙarfin tsiya, ganyan da ke maƙale a ƙugunta da ƙirjinta ne ya faɗi gefe Yarima ya haɗe ta da jikinta tare da sauke buƙatarsa a haukaca akanta. Cikin fitar hayyaci ta riƙa ambatar sunan Damina tana tsine masa da aibanta shi da miyagun kalamai marasa daɗin saurare, sai da Yarima ya dawo cikin hayyacinsa ya fahimci Mai babbar turaka ta galabaita. A wahalce ta dubi Yarima yana faɗin, "Yarima mahaifinka ya yi min abin da ba zai taɓa albarka ba, akwai laƙanin da nake son taimakon wannan daular da shi amma yana cikin turakata..." Da sauri Yarima ya tallafo kanta yana faɗin, "Laƙanin me ye kar ki tafi ba ki gaya min ba." Cikin kakari ta furta, "Ka tabbatar da ka yi tozali da sabuwar sarauniyarmu kuma ita ce za ta ɗauko..." Daga haka harshenta ya sarƙe idanunta suka ƙafe ta faɗi matacciya.

Zuwanmu tsibirin keda wuya muka samu dubbannin jama'ar yankinmu sun yi dafifi akan tsiribirin, da yake duk ranar talata da daddare muna taruwa akan tsibirin domin miƙa buƙatunmu ga abar bauta. Mun yi amanna akan duk wanda ya faɗi buƙatarsa a kan tsibirin tabbas buƙatarsa za ta biya. Kasancewar sun lura da halin da nake ciki ya sa suka buɗe min hanya muka wuce don isa ga abar bauta saboda akwai ƙudurin da nake son sanar da ita duba da rikitattun al'amuran da suke baƙuntar rayuwata. Muna gab da ƙarasawa muka riski sautin wakiliyar Abar bauta, ba mu sake tsinkewa daga lamarin ba sai da muka yi tozali da ita ta fito matsayar da ko a tarihin rayuwa ban taɓa jin ta fito harabar wurin ba. Kamar ɗaukewar ruwa sama haka wurin ya yi tsit kowanne ya baje majiyar sauti da maganansa, ko a mafariki ban taɓa tozali da siffar wakiliyar Abar bauta ba sai dai labarin da magaba suke ba mu akan samuwarta da tasirinta ga rayuwarmu.Tun bayan kafuwar yakinmu a tarihin da muka taɓa fuskanta, abar bautar wancen yankin bata taɓa fito wa ba sai a ranar da wani mummunan al'amari ya faru da su wanda sanadin haka ya sa aka kafa tarihi har muka mayar da ranar Talata a matsayin ranar karɓar addu'a kuma ranar biyan buƙata, domin a cikinta ne al'ummar Maharba suka samu ƙarfin iko da nasara akan Baƙar Daular da ke gaba da yankinmu. Sannan mahaifina ya tabbatar min a bisa al'ada duk lokacin da Abar bauta ta bayyana akwai wani mummunan al'amari da zai faru wanda zai hargitsa al'ummarmu. Ban gama dawo wa daga duniyar tunani ba na riski sautinta tana faɗin, "Ya waɗannan al'aumma yau na bayyana kaina ne domin na shaida muku mummunan al'amarin da yake tunkaro mu kwatankwacin mummunar ƙaddarar da ta faru a baya. Kogon bincike ya ƙone ƙurmus! Hasken wutar abar bauta ta ɗauke. Buzun zakin abar bauta ya miƙe yanzu haka yana cen yana fidda aman wuta.

A yau na tsaya a gabanku domin na tabbatar muku da bala'in da yake tunkaro rayuwarku, ga taron rundunar baƙar inuwa tana tunkaro mu don haka ya zama wajibi mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu sake tserartar da yakinmu domin gujewa abin da ya faru ɗaruruwan shekarun da suka gabata, a zahiri dukkan alamun da suka bayyana a baya sune suke sake bayyana a wannan lokacin domin yanzu haka tazarar da ke tsakaninmu da wannan baƙin yaƙin bai fi taƙi kaɗan ba. Ina jin tsoron kada farmakin Baƙar Daula ya wanzu a gare mu duk da muna da tsarin da ko tsuntsu ba za su iya gani da idanunsu ba matuƙar ya kasance ɗaya daga cikin ahalinmu na Maharba." Ras! Na ji gabana ya faɗi musamman da na tuna Kandala bata daga cikin zuri'ar Maharba, hasalima tsarinmu ya katange da ita." Ina tsoron kar wani mummunan al'amari ya faru da ita. Hankali a tashe na furta, "Ba zan bari ba Kandala! Ba zan taɓa bari a cutar da ke ba tun da kaina na ɗauki alƙawarin kulawa da rayuwarki. Zalincin baƙar Daula ba zai taɓa ɗarsuwa a kanki ba koda zan rasa rayuwata tun da ni ce sillar salwantar iyayen da suka haifo ki don haka zan bada jini da ruhina akan ki.

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*

©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

4

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

Gudun kada Abar bauta ta fahimci abin da nake faɗa ya sa Mahaifina ya damƙi hannuna mara ciwon sannan ya yi min raɗa a kunne da cewar, "Ɗaure bakinki ya fi miki alheri akan mummunan fushin da abar bauta za ta yi da ke." Idanuwana na ɗago ina kallonsa, har ƙwayar idona ta ciko da ƙwallah sai na haɗiye abina don na tuna gargaɗin da mahaifina ya yi min akan zubar ƙwallata. Muryata na rawa na furta, "Ina gudun abin da zai faru da Kandala don ka san tsarinmu ba zai taɓa tasiri a tattare da ita ba. Ta kasance bata daga jinin Maharba da mafarauta, idan baka manta ba da bakinka ka gaya min Abar bauta ta tsarkake iya zuri'ar wannan yankin namu ne kawai, ka na ganin idan wani abu ya faru da Kandala zunubi da munanan abubuwa ba za su ƙaru a kaina ba duba da abubuwan da suke faruwa da ni? Na yi sanadiyar mutuwar iyayenta, kuma tun da dokar dajin na lashi aniyar kare haƙƙinta kamar yadda iyayenta za su kula da ita. Don Allah kada ka dakatar da ni saboda ina tausayin rayuwarta, ta rasa iyayenta a yankinmu, ta rasa zuri'arta a yankinmu, ta rasa budurcinta a yankinmu shin wannan kaɗai bai isa ya sa a tausayawa rayuwarta ba?" Jikin mahaifina ne ya yi sanyi tamkar wanda aka zare wa laka, ya dube ni haɗe da sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Shi kenan Kyauta! Abar bauta ta kawar da muguwar rana a kan ki, za ta shiga lamuranki ba za ta da mu kunya ba albarkacin tsafi da farauta." Jin daɗin kalamansa ya sa na sakar masa murmushi a daidai lokacin na ji Abar bauta ta sake cewa, "A daren yau zuwa gobe za a katange yankin nan daga baƙar guguwar da ta taso mana. Ya zama wajibi a zubar da jini ga rauhanai don su sake dafa mana akan sha'anin rayuwarmu, wannan shi ne abin da zan iya sanar da ku don na taimaka muku. Idan kuka bijirewa umarnina zan iya sauya sheƙa daga wannan yankin zuwa wani na kafa daulata, munanan abubuwa za su yi ta faruwa a kan ku haɗe da farmakai daga sauran ƙasashe musamman Baƙar Daular da kullin burinta ta shafe tarihin Maharba a faɗin duniya." Cikin aminta da kalaman abar bauta da ba ta yarda ya sa muka amsa mata da faɗin, "Uwar gijiya abar bauta ta dafa mana ta shafe matsalolinmu, mun dogara da ke don haka ke ce mai yaye mana damuwa da ba mu waraka a kowanne lokaci. Mun ji mun amince za mu yi abin da kika ce domin mu ma su bin umarninki ne, mun dogara da tsafi da sihiri sune madogarar abar bauta ita kuma ita ce madogararmu a koyaushe."
Chapter 7 · 0% Book details