← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 46

Sashe 10

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin da muka nutsa dajin mun yi tafiya mai nisa muna cin karo da manya da ƙananan dabbobi, tun muna tafiya da yawanmu har ta kai ga mun rarrabu kowanne ya yi hanyarsa, sai ya rage daga ni sai Nalami autan kunkuru muka ci gaba da nutsawa cikin ƙasurgumin dajin. Haka kawai na ji kaina na sarawa tsigar jikina na tashi yanayin da bai taɓa riskata ba, ga wani irin jiri da yake ɗaukata lokaci-lokaci. A hankali na dafa wata baƙar bishiya haɗe da jingina kaina a jiki saboda yanayin da nake ji ga wani irin sara da nake ji a duk gaɓɓan jikina, Nalami ne ya ƙaraso wurina cikin ƙarfafa gwiwa ya furta min, "Zuri'ar Maharba bata daga cikin raunana don haka babu namin dajin da zai yi galaba akan ki albarkacin tsafi da Abar bauta." A hankali na yunƙura ina faɗin, "Nalami jikina yana ba ni wannan shi ne dajin Bawaya dajin da za mu yi baƙin artabu da hatsabibin macijin nan." Waige-waige ya fara yi hannunsa riƙe da itace mai ɗauke da harshen wuta ya fara haskawa. Garin ganyen idon rana ya kunto daga ƙugunsa sannan ya fara turarashi, sannu a hankali muka fara ganin wata irin walƙiya haɗe da mummunan gurnani mai tarwatsa zuciyar ƙananan jarumai. Miƙe wa na yi a hankali na ƙara ƙwarara gwiwata sannan na ci gaba da baza kunnuwana don jin daga wurin da macijin zai bayyana. Daga gefen da na tashi na ji abu na motsi nan take muka ƙurawa wurin ido, wani abin tsoro a tunaninmu a jikin bishiya muke ashe girman macijin ne ya yi tamkar wata murgujejiyar bishiyar kuka. Baya muka fara yi sai da muka matsa sosai na hangi wata sarƙar zinare da tagulla a wuyansa, idanunsa na fitar da wani hasken kaɗan-kaɗan. Nalami ne ya kwarara ihu nan take dajin ya amsa, ya zabura a guje da niyyar tunkarar macijin gadan-gadan. Da sauri na riƙe shi muna haɗa ido na furta masa, "Ba a gaggawar gasgata ɗan ɓarawo har sai an jarraba shi. Ba ta haka za mu ɓullo masa ba dole sai mun yi takatsantsan." Gyaɗa min kai ya yi a hankali muka zaro bindigarmu, muka saita shi sai dai wani abin mamaki nan take bindigar ta fara fidda farin hayaƙi. Daga can bayana na fara jiyo ihun wata mace, sosai na kasa kunnena duk da ina gaban baƙin macijin da koyaushe zai iya hallaka mu. A hankali na riƙa ja da baya ina bin hanyar da na ji sautin wannan matar yana tashi, ƙarasawata bakin wani ɗan kogo ya sa na fahimci daga wannan wurin sautin yake fitowa. Leƙa wa na yi ina zura harshen wutar don haska abin da yake ciki, nan take na ci karo da wata mace mai tsoron ciki wacce da alama naƙuda ce ta taso mata gadan-gadan. Kallon tuhuma na bita da shi a lokacin da ta ɗago hannun tana miƙo min alamar na taimaka mata, garin ƙafar rauhanai na ɗauko na turara don na tabbatar da mutum ce ko kuwa iska ce take son cutar da ni. Wannan garin mahaifina ya samu laƙaninsa a wurin Mahaifinsa yana taimakawa wurin farauta a duk lokacin da kake kokwanto kasancewar hallita. Ganin bata ɓace ba ya sa na kutsa kaina ciki na tsugunna a wurinta ina faɗin, "Ga ki jinsin mutum amma meye ya kawo ki wannan baƙin dajin da tsohon cikinki?" Kamar kurma haka ta rikice tana kuka ta rungumo ni jikinta tana shafa ni, ban fahimci abin da take nufi ba don haka na buɗe baki zan yi mata magana na ji ta riƙe ni sosai ban yi aune ba na ji kukan jariri ya ratsa kunnuwana, ajiyar zuciya ta sauke ta ɗago jaririn haɗe da saka wani fiƙaƙƙan itace ta yanke masa cibiya. Ganyen fatar da ke kare da gefen ƙirjina na ciro na miƙa mata ta naɗe jaririn da shi, ta ɗago ta kafe ni da idanunta ganin haka ya sa na yunƙura zan miƙe na ji ta ruƙo hannuna. Sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin, "Albarkacin Sha kundum ki taimaka ki karɓi jaririn nan saboda kin kasance daga cikin masu sa'a, a ƙallah na shafe sama da shekara ashirin da biyar a cikin baƙin dajin nan ban taɓa ganin wani mahaluki ya shigo shi ba. Sha kundum ta yanke mini baƙar wahalar da na jima ina sha ga shi har zuwanki ya zame min waraka, ni kam na san tawa ta ƙare amma ki taimaka ki ɗaukar min alƙawarin kula da jaririn nan kuma ki min alƙawarin za ki sada shi da wata Daula mai cike da sarƙaƙiya da rikitattun al'amura. Ki yi min alƙawarin duk daren daɗewa za ki sada shi da mahaifinsa idan har yana raye, duk wani ƙarin haske zan baki dange da waye mahaifinsa domin kafin zuwana nan mahaifinsa shi yake mulkar Daular bakiɗaya. Kamar yadda ƴar uwata ta gaya min ga shi yau ya tabbata, ta saka boka ya aiko rauhanai sun kawo ni nan ne domin biyan buƙatar kanta. An kawo ni nan an tsaface ni ta yadda ba zan taɓa haifar abin cikina ba har sai ranar da wani jinsin bil'adam ya kawo ziyara wurin nan. Ta alƙarwarta min za ta auri mijin kuma za ta salwantar da rayuwar yarima, don ta gaya min koda wani ya shigo wurin nan ba zai taɓa ɗauka ni mutum ba ce duba da dajin nan yana da kamanceceniya da dajin ƙare kukanka. Sai ga shi yau na haife cikin da ya shafe shekara sama da ashirin da biyar a jiki, tabbas wuya bata kisa kuma na amince Maharba na da farar zuciya domin da mutanen yankina ne sai dai su kashe ni su zari abin da yake cikina."Jikina ne ya yi sanyi da jin kalamanta, na dube ta cike da tausayawa na furta, "Ki taso ki biyo ni na yi alƙawari zan taimaka miki. Amma ba zan tafi da jaririnki ba domin ni ma wani aiki ne a gabana na sarar kan macijin da ke cikin dajin nan." A madadin ta amsa mini na sai na ga ta saki murmushi tana faɗin, "Sara da makami ba zai taɓa baki nasarar kashe macijin can ba, ki ɗebi ciyawar tukunyar maƙiya ki murje a hannunki da shi, sannan ki shafe duka jikinki sai ki saka ƙwara uku a baki ki tauna ki tunkare shi cikin jarumta ki tabbatar da kin kai kansa doron ƙasa, domin wannan ne kaɗai makarin ruhinsa shi kenan za ki yi nasara akansa." Da mamaki na dube ta na furta, "Ya aka kika san haka?" Ta rungume jaririnta haɗe da bashi mama ya kama yana sha sannan ta furta, "Shekara ashirin da biyar a dokar dajin nan ba wata ashirin da biyar ko makwanni ashirin da biyar ba ne. Ki yarda da ni ba zan cutar da ke ba kuma ki yi min alƙawarin za ki kula min da yarona har ki kai min shi mahaifarsa." Tana rufe bakinta na ji ihun Nalami don haka a gaggauce na amsa mata da na amince na fice daga cikin kogon, a kwance na same shi shame-shame cikin azaba. Yana jin na taɓa shi ya furta, "Kar ki wahalar da kan ki a kaina mutuwa zan yi Kyauta, maza hanzarta ki kare kan ki kada a yi biyu babu." Magungunan saran macijin da ke ɗaure a ƙuguna na kunto ina saka masa amma babu wanda ya yi aiki, ina shirin kun ce wani na ji ya riƙe hannuna yana faɗin, "Wannan ba kamar sauran macizan da kika sani ba ne, ki bar wahalar da kan ki tawa ta zo ƙarshe. Sa'a ta kai miki abar bauta ta baki nasara akan wannan macijin cau cau cau mai gayya mai aiki." Hawaye ne ya zubo min a hankali na furta, "Jarumi uban yaɗiya ya amshi ziyararka, dawa ba daɗi a dajin Bawaya." Ina ji ina gami numfashin Nalami ya ɗauke, gurnanin macijin ne ya sake ankarar da ni don haka na miƙe da sauri na fara lalubar ciyawar da matar nan ta faɗa min, dama na santa a ido sai dai ban san laƙanin da ta sanar da ni ba. Na jima ina abu ɗaya har muka fara wasan ɓuya da macijin yana watso min dafinsa ina kaucewa. Har na fara fidda rai sannan na hangi ciyawar a saman wani shuri, da sauri na dira a kan shurin nan take ya rushe na tsinki ciyawar na murjeta na fara shafe jikina.

Kai tsaye na tunkari macijin ya fara ja da baya ganin yana shirin guduwa ya sa na tafi da gudu na damƙi jikinsa, laushi ya fara yi da sauri na ɗare samansa ya tura kansa a doron ƙasa nan take ya faɗi matacce. Takobin da ke rataye da ni na zaro ba a ɗauki lokaci ba na datse kansa, na sakala takobina ta cikin ƙwayar idonsa na fara jan kan da karfi don nauyin kansa ya kusa girmana a a tsaye. Bakin kogon na ƙarasa sai dai wani abin mamaki na nemi matar sama ko ƙasa na rasa sai jaririnta da ke gefe yana mutsu-mutsu ga wata azurfa a kan cikinsa da wata ƙaramar aska. Daga wurin ƙafafuwansa wani ƙaton ganye ne da aka zuba wasu abubuwa da ban san na meye ba. A hankali na ƙarasa na ɗauki jaririn na rungume tare da kwaso kayan da ta ajiye masa, na fara jan kan macijin a wahale sannan na ɗauki hanyar da za ta sada ni da yankinmu.

Daular Sarki Damina.
Chapter 10 · 0% Book details