Sashe 24
Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da Sarki Damina ya tashi daga bacci tuni Boka mai zamani ya gama abin da zai yi ya yi gaba, da tarairaiya ta tarbe shi sannan ta furta, "Na yi mamakin yadda ka iya yin bacci a daren yau." Murmushi ya yi yana shirin magana ta ci gaba da cewa, "Farincikin samun lafiyar Yarima ya fi min komai don haka yau ko kaɗan ban runtsa ba. Idan ban manta ba rabona da farinciki irin wannan tun kafin samun ciwon Yarima yau sama da shekara ashirin da wani abu. Kai gaskiya mun gode wa Shakundum ta dubi roƙon da muke yi na tsawon shakaru."Sarki Damina ya faɗaɗa fara'arsa yana faɗin, "Hasana ban da bacci ɓarawo ne babu abin da zai hana ni kwana idanu biyu, kin ga maganar boka mai zamani ta fito fili da ya ce min Yarimana zai warke. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ya ce min yarinyar da zai kusanta ita ce silar samun lafiyarsa kuma har da albarka Ɗa ko Ƴa a tsakaninsu." Ras! Gaban Usaina ya faɗi, a zabure ta furta wannan saduwar da ya yi da su ko kuma wata nan gaba?" Kai tsaye Sarki Damina ya ce, "Wannan dai kin ga ya zaman wajibi na sa a binciki yarinyar don dole Yarima ya aureta tun da na lura alheri ne tattare da ita kuma ƴar baiwa ce." Usaina ta fara sosa kai wani abu na taso mata mai ɗaci a maƙogaro sai kuma ta wayance da cewar, "To mai zai hana ka sa a tara ƴaƴan nawa a bincike su idan aka gagara ganewa ka ga ba sai ka saka a killace su ba, idan aka killace a wani gidan ana kula da su da sannu za a ga wacce take da juna biyu a cikinsu. Idan kuma haka bai yi ba sai ka saka Boka mai zamani ya yi maka bincike a kansu." Cike da jin daɗin shawararta ya rungumeta yana buga bayanta ya ce, "Shi ya sa nake ƙaunarki Hasana, ke wallahi kin ga dai ƴar uwarki Usaina ta mutu ko amma ko ita da kuka kasance ƴan biyu ba za ta nuna miki kaifin basira da tunani ba domin sam hali da tunaninku ba ɗaya ba." Wani abu ne ta ji ya soki ƙirjinta har sai da fushinta ya baiyyana a fili, ganin haka ya sa Sarki Damina ya yi tsammanin ko don ya faɗi wannan maganar game da ƴar uwarta ne ta ji haushi, cikin lallashi ya furta. "Ki yi haƙura ban faɗa don na ɓata miki ba sai dai yabon gwani ya zama dole." Usaina ta wayance tana murmushi ta furta, "Wannan haka ne. Yanzu dai idan an jima zan leƙa na ga sauƙin jikin Yarima, idan ya so sai ka yi yadda na bada shawarar ina ganin zai fi." Sarki Damina ya amsa mata. Daɗi ne ya kamata don ta san duk shawara ɗaya da ta bayar idan aka ɗauketa dole za ta samu mafitar da za ta hallaka su lokaci ɗaya ba tare da wani ya zarge ta ba.
Shiru na yi lokacin da na ji shela da sanarwar da aka bayar daga wurin Sarki, a tunanina zan iya ɓaddabami na saje da sauran bayin cikin wurin da muka samu a wurin, ina gani wasu daga cikin tsirarun ƴanmatan da aka tafi da mu suka fita wurin mai shelar. Ni da sauran mutum huɗu muka yi shiru kamar ba ma daga cikin waɗanda ake yi wa sanarwar, wani abin mamaki sai ga Dakarun na zaluƙo mu ɗaya bayan ɗaya duk da babu wani abu da za ka kalla wanda ya bambamta mu da waɗancen, idanu ne ya dawo kanmu nan take tsoro da fargaba suka mamaye zuciyata musamman da na tuna irin halin da muka baro yarima a ciki yana wani irin bacci da ban taɓa ganin irin munsharinsa ba. Hawaye ne ya zubo min na fara ayyana irin gashin-ƙumar da za a yi mana domin har lokacin matar da muka samu an farkewa ciki ta gagara ɓace min daga idanuna ba, kuka nake sosai saboda tausayin hukuncin da za mu fuskanta. Ganin haka ya sa ƴan uwana da aka tafi da mu tare suma suka mara min baya kowacce na zubar da ƙwalla, a gaban dubban jama'a aka sake jere mu sarki da muƙarrabansa suna cikin tanti a zaune. Karaf idanuna suka hango min shi a zaune kusa da Mahaifinsa, a wannan karon tsaf na gan shi cikin kyakkayawar shiga duk da ba wata sutura ce a jikinsa face ganye. Amma kana ganinsa za ka bambamce yanayin nutsuwarsa saɓanin jiya da muka same shi a hargitse, a hankali na furta, "Ko kaɗan ba zaci cutarwar da kake min a baya ta kai haka ba, sai ga shi ka raba ni da ƙimata da mutumcina da na jima ina yi wa Goga tanadi..." Maganar da Sarki Damina ya yi ce ta katse min kalamaina, ya miƙe tsaye yana kallon al'ummar da ke wurin yana faɗin, "Ya ku al'ummar cikin wannan Daula, ku yi sani Yarima Ɗana ɗaya jal tilo ya samu lafiya. Ya samu lafiya ne kamar yadda boka ya faɗa min a baya sanadiyar waɗannan ƴanmatan, don haka ya zama wajibi a gare mu; mu killace su domin suna daga cikin masu daraja." Yana rufe baki na ji duka sun ɗauki sowa da tafi cikin farinciki suka shiga raye-raye da bushe-bushe, sai da suka ɗan jima sannan Sarki ya ruƙo hannun Yarima ya fara takowa har gabanmu, tun da na ga haka gabana ya ci gaba da faɗuwa ina tsoron kada ya nuna ya sanni domin na san babu tantama shi ne mutumin da ke fitowa daga cikin tawagar da ke baƙuntar rayuwata. A hankali ya fara nuna masa mu ɗaya bayan ɗaya sannan ya bashi labarin zuwanmu da kai mu wurinsa da aka yi, bai tanka wa mahaifinsa ba illa gyaɗa kai kawai da na ga ya yi sannan suka koma suka zauna. Wurin zama aka nuna mana sannan aka kawo mana kayan ciye-ciye da lashe-lashe. Ina kai loma ɗaya bakina na ji ta min ɗaci sakamakon tuno iyayena da ƴan amanata da na yi, hawaye na goge a fakaice sannan na ci gaba da turawa ba don ina jin daɗinsa ba. An jima ana shagali sannan daga baya aka ɗauke mu daga wurin aka kai mu cikin gidan Sarki Damina, a wani ɗan ƙaramin gida aka sauke mu aka ba mu duk wani kayan buƙata tamkar waɗansu ɓangare daga jinin Sarki Damina.
Daga wurin taron kai tsaye Sarki Damina wurin Boka Mai zamani ya wuce, duk abin da yake faruwa ya zayyane masa da neman taimakonsa. Boka mai zamani yana son yin bincike a gaban Sarki mai zamani amma yana gudun kada wani abu ya faru marar daɗi har Damina ya ga gazawarsa. Don haka ya ƙarfafa masa gwiwa akan hukuncin da ya yanke na killace ƴanmatan a wuri ɗaya kafin cikin da ake tsammani ya bayyana. Cike da murna Sarki Damina ya miƙe har zai je bakin ƙofa Boka ya ce, "Damina ina fatan baka manta al'adar Daular nan ba ko?" A hargitse Sarki Damina ya juya yana faɗin, "Ta me fa?" Cikin rashin damuwa Boka ya ce, "Har ka manta sadaukarwar da ka yi wa Babban dodo abin da ka haifa na fari? Sanin kanka ne duk wani Sarki ko mai jiran gado dole ne abin da za a haifa masa na fari a sallama wa Babban dodo, idan kuma ba haka ba ka san abin da ya wakana ga mahaifinka kafin baƙuntarsa lahira." Dariya ya bushe da ita mai ƙarfi sai da ya yi mai isarsa ya kalli Boka ya ce, "A halin nake ciki ko uwarsa ka ce na sallamawa Babban Dodo zan bayar da ita balle abin da za a haifa masa, na yi alƙawarin a lokacin da yarinyar da ke ɗauke da cikin Yarima ta haihu ko mahaifa ba za ta kai ga faɗowa ba Jaririn zai dangana ga Babban dodo. Buri da fatana dama Yarima ya samu lafiya yadda zan samu magaji kuma ya samu ban damu ba, don haka idan ka cire Yarima da ni zan iya fansar da gangar jiki da ruhin kowa." Yana gama maganar ya fice daga kogon dutsen. Jinjina kai Boka mai zamani ya yi ya ce, "Tabbas kuwa ka yi shuka a idon makwarwa waɗannan kalamai naka tamkar a kunnen Usaina ka yi su."
Zamanmu a cikin gidan Sarki Damina babu yabo babu fallasa domin duk wani abin buƙata babu wanda muke nema mu rasa, sai dai tuni kwanciyar hankali ta yi ƙaura a gare saboda kullin tunani ɗaya a wane hali iyayena da ƴan amanata suke. Ga ƙarin takaici ɗan gidan da aka kai mu a ciki muke rayuwa ko soro ba a bari mu je, sa dai kusan kullin Mahaifiyar Yarima takan kawo mana ziyara, a yadda na lura macece mai mutumci da sakin fuska. Kullin cikin jammu a ciki take tana kawo mana hira masu daɗi da kwantar da hankali, don haka ya sa a duk lokacin da ta shigo wurinmu take tambayarmu matsalolin da ke damummu. Kwananmu goma sha biyu a cikin gidan na fara ciwon kai mai zafi ga yawan kasala da tashin zuciya, sautari a duk lokacin da na ci abinci sai dai na fakaici idanun sauran ƴanmatan da muke tare na tafi banɗaki na kyalaya amaina a can, wannan sauyin da na gani ba ƙaramin ɗaga hankalina ya yi ba domin duk wasu alamin ciki ya bayyana a jikina, ranar da mahaifiyarsa ta shigo wurin mu da yamma haka kawai na ji turaren jikinta na tayar min da zuciya. Na tsugunna ina gaishe na ji na gagara daurewa sakamakon aman da nake jin ya taso min, da gudu na nufi bakin rariya na fara amai kamar zan amayo da ƴaƴan cikina. A wahalce na dawo ina shirin zama mahaifiyar Yarima ta ruƙo hannuna tana duba tafin hannuna, tana gama duba hannuna ta gwala idona tana ƙarewa ƙwayar idona kallo. Sunkuyar da kai ƙasa na yi na ji ta ce, "Tun yaushe kika fara yin aman nan?" A hankali na furta, "Yau kwana uku."