Sashe 14
Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Girma da siffar Badakaren ne suka sake hargitse lissafin rayuwata, a hankali na sake ja da baya ya yin da yake sake tunkaro mu gadan-gadan hannunsa É—auke da wani mummunan Æ™arfe wanda aka naÉ—e jikinsa da manyan Æ™usoshi, a zafafe ya É—aga da niyyar buga min a tsakar ka cikin shammata mahaifina ya kai masa duka a wuyansa. Take suka fara kokawa ganin haka ya sa mahaifina ya yi mini alama da mugudu ni da Kandala, gudu muke kamar ranmu zai fita don na gama tsorota da yanayin azzaluman mutanen da suka fito daga baÆ™ar daula. A yadda na bar mahaifina da Badakaren ina jimamin halin da mahaifina yake ciki don na tabbata zai yi wuya idan bai yi wa mahaifina taron dangi sun hallaka shi ba, sai da muka yi tafiya mai nisan gaske sannan muka raÉ“a cikin wata bishiyar É—orawa mai duhu muka zauna muna hutawa, waige-waige nake yi don ganin hanyar da zan samu ruwan da zan É—ebo mana musha saboda zafin ranar da ya busar da maÆ™ogaronmu. A wahalce Kandala ta kalle ni idonta na zubda Æ™wallah tana faÉ—in, "Kyauta Æ™ishirwa za ta kashe ni maÆ™oshina ya bushe." Jijjiga jaririn nake saboda kukan da yake ta tsalawa wanda na tabbata kukan wahala ne sannan na furta mata, "RiÆ™e min shi ki kula da kyau zan duba mana ko da Æ™orama a kusa idan muka sha sai na duba ko zan samu wani naman dawan na gasa mana." KarÉ“arsa Kandala ta yi na miÆ™a cikin dajin ina duba hagu da dama ko zan samu Æ™aramar Æ™oramar da zan É—ebo mana ruwan, ko kaÉ—an ban yi tunanin wurin da zan É—ebi ruwan ba babban burina bai wuce mu samu ruwa kowanne iri ba ne. Daga can nesa na hango wani bafulatani yana tafe da shanunsa wanda hakan ne ya tabbatar min da kiwo yake, gudu-gudu sauri-sauri haka na rinÆ™a tafiya don na Æ™arasa na cimma masa koda zai sa ya taimaka min, yana ganina ya fara bina da kallon tuhuma don ko bai faÉ—a ba na san suturar jikina yake kallo wacce ta bambamta da irin ta shi, kallon kaina na yi daga ni sai guntuwar fatar da ta rufe min Æ™irjina da wacce na suturta al'aurata, sannan na É—ago na kalle shi yana sanye da farar rigar saÆ™i ta kala-kalan zarurruka, sandar hannunsa ya É—aga na ji yana yin yaren da nake tsammanin fullaci ne sannan ya yo kaina da sauri zai sauke min ita. A razane na ja da baya cikin hakki ina faÉ—in, "Abar bauta bata wanzar da zalinci a doron Æ™asa ba don haka kada ka cutar da ni." Sauke sandar ya yi Æ™asa sannan ya furta, "Hai meye abar bauta kuma? Ke kam aljani ne ko mutum?" Dafe kaina na yi saboda matsanancin ciwon da yake min sannan na furta, "Ni mutum ce tare nake da Æ™anwata ka taimaka mana ka ba mu ruwa mu sha." Kallon da yake min ne na tabbatar min da har lokacin bai gama aminta da ni ba, don haka na ga ya runtse ido yana ci gaba da fulatanci sannan ya kara sandar hannunsa a saitin kaina. Ya É—an jima a haka sannan ya buÉ—e idonsa ya ce, "Zan taimaka maka ina Æ™anwar taka?" Hanyar da na baro su Kandala na nuna masa, ya Æ™urawa wurin idanu sannan ya ciro kurtunsa ya miÆ™o min. Har na É—aga kai zan sha na tuna halin da na baro su Kandala, da sauri na sauke shi na ce masa. "Ka taimaka ka cika ladanka ka bar ni na kaiwa Æ™annena su sha. Idan ka yi haka abar bauta za ta albarka ci kiwonka." Æata fuska na ga ya yi don haka gabana ya faÉ—i, ina shirin roÆ™onsa na riski muryarsa yana faÉ—in, "Kada ki sake danganta ni da abin bautarku domin Yesi Almasihu zai yi fushi da ni saboda na haÉ—a bautarsa da waninsa." Shiru na yi ina mamakin maganarsa domin a iya sanina bayan abar bauta babu wani abu da ake bauta wa a faÉ—in duniya. Da yake ina cike da son biyan buÆ™atar kaina sai na gyaÉ—a masa kai cike da godiya, har na juya zan nufi hanyar na ji yana faÉ—in, "Ki bar hanyar É“ata ki dawo kan shiriya ko za ki samu gidan daÉ—i wato aljanna domin mu mabiya Yesu Almasihu mun kasance masu karamci da taimakawa saboda Allah." Ko kaÉ—an ban gane abin da yake nufi ba don haka ban amsa masa ba, sai na kawar da maganar cikin amsar da na bashi da cewar, "Zan gaggauta kai wa Æ´an uwana akwai jariri ina tsoron kada ya mutu." A hargitse ya fura, "Jariri kuma?" Na gyaÉ—a masa kai, jin haka ya sa ya kaÉ—o shannunsa ya rufa min baya muka tunkari wurin da su Kandala suke. A galabaice muka same su don haka cikin hanzari na karÉ“i jaririn na fara bashi a lokacin tuni ya gaji da kuka ya sake yin bacci, sai da ya sha ya Æ™oshi sannan na miÆ™a wa Kandala ita ma ta sha ta rage mini. Tausayin Jaririn ne ya kama shi ya dube ni yana faÉ—in, "Idan ba za ki damu ba ko na tatso masa nonon Naggen can ya sha." Ban san lokacin da murmushi ya suÉ“uce min ba na furta masa, "Na gode sosai da taimakonka." Nonon saniyar ya tatsa da É—uminsa ya miÆ™o mini na É—an riÆ™a bashi kaÉ—an-kaÉ—an yana sha. Sai da na lura ya Æ™oshi sannan na miÆ™a wa Kandala ta shanye sauran, miÆ™e wa na yi na yi na yi masa godiya muna shirin tafiya ya furta min, "Yanzu ina za ku tafi ke da kika ce baki da kowa?" Idanuna ne suka ciko da Æ™walla na furta masa, "A da ni Æ´ar gata ce gaba da baya, sai dai a yanzu ba ni da kowa ban san inda za mu tafi ba." Tambaya ya sake jefo min nan take ya bashi labarin abin da ya baro mu daga yankinmu, ya tausaya mana sosai don haka ya yi alÆ™awarin kai mu rugarsu domin ya taimaka mana, duk da ya gargaÉ—e ni a kan na É“oye addinina idan kuwa na bayyana shi a rugarsu za su iya korata daga garin. A yadda ya ba ni labari tun tasowarsu iyaye da kakanni babu wani addini da suka sani face Kiristanci, a kan shi suka kafu Yesu Almasihu suke bautawa don haka ba su yadda akai musu kowanne irin addini saÉ“anin nasu ba. Ba ni da zaÉ“i don a lokacin burina bai wuce mu samu mutsuguni ba duba da É—anyan goyon da muke tare da shi, a yadda na ayyana da ace daga ni sai Kandala ne za mu ci gaba da tafiya har mu nufi wani yankin da ba sa tsauwala wa game da addinin da ni kaina na gaje shi tun iyaye da Kakanni. Jiki babu Æ™wari na sake rungume jaririn muka fara tafiya, ya wuce gaba shi da shannunsa muna biye.