← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 46

Sashe 1

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*

©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

1

A duk lokacin da Allah (S.W.A) ya ƙaddara wanzuwar hallitar Ɗan adam a doran ƙasa, ko ya ƙi ko ya so akwai waɗansu abubuwa da suke yin jerin gwano a gangar jiki da ruhinsa. Inuwa! Wata aba ce da Ubangiji ya ke ƙaddara wanzuwarta manne a jikin kowanne abu, walau mai rai ko akasin haka. A kodayaushe tana bibiye da su matuƙar bawa zai zuba maganansa zai lura da haka. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko kishiyarta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake wa ƙaddararsa, sanin haka ya sa na fahimci karin maganar Malam bahaushe ta: 'Tun ran gini tun ran zane." ta zauna ɗaram kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbinta.

10/06/1022
Shekara Dubu ÆŠaya baya.

Hankalinsa ya fi na kowanne lokaci kai wa matuƙar ƙolokuwar tashi, yana tafe yana taku da sandarsa Waziri da sauran muƙarraban cikin daular suna take masa baya. Tamkar waɗanda saƙon mutuwa ya dirar wa haka fuskokinsu suka fasalta saƙon da ke ƙunshe cikin birnin zuciyoyinsu. Sarki Damina yana kai ɗora ƙafarsa kan jan dutsen da ke a matsayin matattakalar benen hawa tsauni tsidik! Wani gajiyayyan talakansan ya dira a gabansa cikin firgice da tashin hankali, kuka yake tamkar hawayen idanunsa za su ƙare. Ya ruƙo ƙafafuwan Sarki Damina a ɗimauce yana faɗin, "Ya kai babban Sarki, Sarkin sarkunan duniya bakiɗaya sarkin da yake share mana hawaye. Ka taimaka ka roƙar mana afuwa wurin Sarauniya Sha-kundum, yanzu haka ɗana Rabo yana can yana aman jini ta hanci ta baki don mai ɗakina naƙuda take jini ya ɓalle mata tana gangarar..." Tun bai rufe baki ba Sarki Damina ya daka masa razananniyar ƙarar da sai da hantar cikinsa ta kaɗa, yana shirin sake magana Sarki ya fisgi takobin da ke maƙale a kafaɗar Waziri kafin Bawan ya yi wani yunƙuri tuni ya sauke kansa ƙasa. Da sauri wasu ƙaratan Dogarai suka ƙarasa wurin suka zube suna yi wa Sarki godiya, "Godiya muke Sarki Damina mai masoya da yawa, Sarauniya Sha-kunduma ta yi ruƙo da hannayenka. Haushin zuciyarta ya gushe domin ta faɗa mana hanyar maganin samun lafiyar Yarima, idan wannan bai wadatar da kai ba ka yi mana umarni mu kawo maka wani ko da a cikin mu ne ka sake datse rayuwarsa matuƙar zai sanyaya zuciyarka" Bai tanka musu ba ya miƙa wa Waziri takobin da ke ɗigar da jini, har sun cicciɓi gawar bawan da kansa tuni ta samu mutsuguni a gefen wata bishiya, Sarki ya dube su yana cewa. "A gaggauta ƙone gangar jikinsa tare da yaron nasa da ba shi da lafiya. Ita kuma mai ɗakinsa a zaro jaririn cikinta a kai wa babban dodo sannan a salwantar da gangar jikinta" Yana gama magana ya haye kan tsibirin maƙarrabansa suna biye da shi a baya.

Kamar yadda yake farillah a wurinsu duk lokacin da za su shiga cikin kogon dutsen a yanzu ma sai da suka aiwatar, sai da kowannensu ya saka ƙanƙanuwar aska ya yanki gefen ɗan yatsan hannunsa suka yarfar da jinin a jikin wani sassaƙaƙƙaen gunki, hannun gunki ɗauke yake da kwari da baka daga bayansa an jingina masa takobi a jiki. Kansa a sunkuye yake alamar ƙasƙantar da kai ga wani dungulmin kan mace da suka ɗora masa a gadon bayansa. Sarki Damina ne ya fara yin gaba sannan su Waziri suka rufa masa baya, daga bakin shiga dutsen suka tsaitsaya don sun san ko karan hauka ne ya cije su ba za su taɓa haure bakin ƙofar dutsen ba. Kai tsaye Sarki Damina ya kutsa ciki sandarsa ta zame masa abokiyar tafiya. Daga tsakiyar kogon dutsen ya hangi Boka Mai zamani zaune da wasu ƙanana tukwane a gabansa, daga shi sai ganyen ayaba wanda ya yi makari don rufe al'aurarsa.

"Yau ba ranar zuwan ka ba ce kamar yadda yake a bisa al'ada, me yake tafe da kai don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Boka mai zamani ya faɗa yana karkatar da hankalinsa wurin Sarki Damina. Duk tsananin izza da taƙama irinta Sarki yau ya sauke ta a gefe ya fusakanci Boka yana mai bayyana damuwarsa, Sarki Damina ya zube gwiwowinsa kamar wanda ya aikata wani mummunan zunubin da yake neman gafara. Murya ɗauke da damuwa ya furta, "Ya kai Boka Mai zamani lamarin halin da talakawanmu suke ciki tabbas tura ta fara kai bango. A yau mun wayi gari da samun ɓillar annobar haɓo a cikin gari fiye da tsammani, babban abin da ya ɗugunzuma hankalina abin bai tsaya iya waje ba hatta ahalina na fuskantar wannan barazanar, a taimaka a roki Sarauniya Sha-kundum ta yafe mana tun da laifin wani ba ya taɓa shafar wani." Boka mai zamani ya miƙa masa busasshen hannunsa mai ɗauke da zaƙwa-zaƙwan farata, taurin hannunsa tamkar busasshen katako sannan ya ce, "Ina tukwicin ziyarar Sarauniya Gunki Sha-kundum kafin na san abin yi? Domin sanin kanka ne tuni bakin alƙami ya riga da ya bushe." Sai a lokacin Sarki Damina ya tuna da ƙoƙon tukwicin ziyara, cikin sake ƙanƙan da kai ya furta. "Sha-kundum ta dafa aikinka ta shiga lamuranka boka mai dogon zamani. Ka ga taka ka ga ta kakanninmu, iyayenmu duka sun wuce sun barka. Ya kai wannan boka mai dauwamamman ruhi da dogon zamani a yi mini afuwa bisa mantuwar da na yi, amma duk wani hukunci da Sha-kundum za ta yanke ni mai biyayya ne." Boka na gama jin haka ya miƙe ya tunkari bakin wata rijiya wacce faɗinta ya fi girman ƙaramin ɗakin, yana zuwa ya fara taka matattakalar da ke cikinta ya shige. Shigarsa ke da wuya bakin rijiyar ya shafe tamkar ba a taɓa wanzar da komai a wurin ba. Yana shiga kai tsaye ya tunkari gunkin wata mace da ke tsaye da tulelen tsohon ciki a jikinta, hannunta ɗaya tallafe da tsohon cikin ɗayan kuma yana riƙe da garkuwa alamun ta kare kanta da shi. Sai da ya sunkuya ya miƙa gaisuwa sannan ya furta, "Ya ke Sarauniya sha-kundum! Ya ke mammallakiyar wannan Daular a yau ma na sake dawowa da neman yafiyar al'ummarki.Na tabbata kina saurarena kamar yadda kika daɗe kina jina. Haƙiƙa talakawanki sun dawo da wata buƙata domin a yau sun wayi gari da samun annobar haɓo shin wane taimako za ki yi musu?" Hawayen ne ya ziraro daga cikin idanun gunkin, boka ya ƙarasa ya kanga kunnensa a jikin ƙirjinta. Ya jima a haka sannan ya ɗago cike da girmamawa ya ce, "Tabbas zan isar musu kamar yadda kika buƙata, ki ƙara haƙuri nan ba da jimawa ba za ki dawo cikin ainihin hallitarki ta zahiri. Za ki ci gaba da mulkar al'ummarki kamar yadda kika mulke su a ɗaruruwan shekarun da suka gabata. Komai ya zo ƙarshe tun da ke kika tabbatar min da haka, sarauta da izzar mulki na baibaye da rayuwarki. Taɓewa da hallaka tana ga Maharba da Mafarauta har ƙarshen rayuwarsa." Yana gama maganar ya juya jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri, yana taka matattakalar bene ɗaya rijiyar ta fara dawowa kamar yadda take da farko a wurin.

Kan shimfiɗarsa ta farko ya koma ya zauna ya dubi Sarki Balarabe yana faɗin, "Ta faru ta ƙare..." Da sauri Sarki ya katse shi da cewar, "Allah sa ba laifinmu ne ya sake hauhawa ba."
Chapter 1 · 0% Book details