← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 46

Sashe 15

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ba ƙaramin artabu aka sha tsakanin Badakaren da Mahaifin Kyauta ba, ganin mahaifin Kyauta na yin neman yin galaba a kansa ya sa Badakaren yin fito nan take wasu daga cikin Dakarun suka yi dirar mikiya a wurin, duka suka riƙa kai masa ta ko'ina sannan suka fisgo shi da ƙarfin tsiya suka ɗaure hannunwansa a jikin murtukeken itacen da tuni aka ɗaure mafi yawa daga cikin mutunen garin mazansu da matansu. Ƴaƴayen da aka raunata iyayensu aka ɗaɗɗaure su sai bi suke suna dafe ƙafafuwansu suna kuka, haka waɗanda aka kashe iyayensu suna kwance akan gawarwakinsu suna tashinsu suna ihu gwanin ban tausayi. Mata masu ciki da tsofaffi haɗe da ƴanmatan yankin duk an ɗaure su jikin itacen da aka zura musu shi cikin kafaɗunsu. Duk wannan azabar da ake gana musu garin tsit ya yi sai kukan ƙananan yara saboda duk wanda aka ji ya yi ihu zane shi suke yi da bulalar hannunsu ba za su bar dukansa ba har sai sun kwaile masa fatar jiki. A haka suka tasa ƙeyar mutanen garin gabaɗaya suka tafi da su, har sun yi nisa shugaban Dakarun ya sa wasu daga cikin dakarun suka koma suka tarkato ƙananan yaran, waɗanda aka lura da suna kwance kan gawarwakin iyayensu sune aka tasa ƙeyarsu ya yin da waɗanda suke kuka suna bin iyayensu da aka ɗebi wasu, wasu kuma aka bar su a wurin. Tafiya ce mai nisan gaske ga babu ruwa balle abinci babu hutu balle su samu salamar azabar da ake yi musu, idan suka lura gungun itace ɗaya ba sa sauri gabaɗaya suke haɗa wa su zane su, ilahirin jikinsu a farfashe yake yana tsattsafar da jini ya yin da ƙananan yaran da aka tafi da su saboda wahala wasu suka riƙa faɗuwa suna suma. Duk yaron da ya suma ba sa bi ta kansa sai dai su wuce idan kuma da kogi ko rami a wurin sai dai su wurga shi a ciki. Ƙalilan daga cikin yaran ne suka samu ƙwarim gwiwar ci gaba da tafiya a haka har dare ya riske su, a kan dole suka yada zango a wani baƙin daji. Duk da kasancewar su a wurin babu abin da aka ba su da sunan ci ko sha, kuma a yadda suke a ɗaure haka suka ci gaba da zama. Mutum ko fitsari da kashi yake ji sai dai ya yi a wurin, suna ji suna gani Dakarun suka yo farautar naman dawa suka gasa suka ci amma su ko ruwa ba su samu ba. Wani tsoho daga cikinsu ne ya galabaita da ƙishirwa don haka a wahalce ya roƙe su akan su bashi ruwa ya sha, wani gajere daga cikin dakarun ne ya ɗebo garwashin wuta kai tsaye ya yi kansa gadan-gadan. Ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalinsu ya yi ba, nan take jikinsu ya fara karkarwa. Yana zuwa ya buɗe bakin tsohon ta ƙarfin tsiya ya zuba masa garwashin a ciki. Saboda azaba nan take tsohon ya fara sakin kashi da fitsari cikin fitar hayyaci, Dakarun na ganin haka suka bushe da wata irin mahaukaciyar dariya har da masu kwanciya a cikinsu saboda ƙeta. Sai da suka yi mai isar su sannan suka dube su cike da izgilanci suna faɗin, "Waye zai kuma cewa zai sha ruwa a cikinku?" Wurin ne ya yi tsit ba tare da wani ya furta koda kalma ɗaya ba, sai da tsohon ya gama galabaita sannan suka ɗauko wani wurtu da ɗan ƙanƙanin ruwa a ciki suka ɗaga kansa suka sheƙa masa. Ruwan da ya shiga bakinsa ko cikin tafin hannu ɗaya ba zai cika ba, ya yin da sauran ya wanke masa fuska gabaɗaya. A na cikin haka ɗaya daga cikin masu matan da ke ɗauke da tsohon cikin ta fara naƙura gadan-gadan, a galabaice take yunƙurin tashi saboda yadda take jin kan jaririn na iya ratsowa ta ƙarƙashinta. Duk yadda ta kai ga ganin ta miƙe ta gagara sakamakon yadda hannuwansu yake ɗaure a jikin itacen kuma a ƙallah sun kai su goma sha biyar a jikin kowanne itace ɗaya. Kururuwa take cikin azaba da neman ɗauki, mijinta da ke ɗaure a wani itacen ya gagara haƙuri duk da zuciyarsa na bugu saboda fargaba ya dubi Dakarun yana faɗin, "Ku taimakawa mai cikin can haihuwa za ta yi." Ɗaya daga cikin su ne ya fara takowa yana sakin murmushin mugunta ɗauke da muguwar manufa, sai da ya ƙarasa gabansa sannan ya wurga masa tambaya, "Ko dai matarka?" Ƙara matar tashi ta sake ƙwallawa a hargitse ya kalli wurin idanunsa na fidda ƙwallah. Suna haɗa ido ta fakaici idon Badakaren ta girgizawa mijinta kai alamar kada ya nuna mijinta ne, ganin irin kallon da mutumin yake yi wa ɓangaren matar ya sa Badakaren ya kalli wurin, a hankali ya miƙe ya ƙarasa wurin matar ya ɗora hannunsa akan cikinta yana shafawa har zuwa gabanta, jaririn da ke cikinta ya ji yadda yake mutsu-mutsu ya waiga wurin mutumin sannan ya sake kallonta ya ce, "Amma mijinki yana tausaya miki da alama yana ƙaunarki sosai." Cije baki ta yi saboda azabar da take ji gumi na ci gaba da keto mata, cike da ƙarfin hali ta girgiza kai murya na rawa ta ce, "Ba mijina ba ne."

Ta faɗi haka ne don ta lura a lokacin da mijin nata ya yi magana ya taso gadan-gadan don aiwatar masa da mugunta, wannan dalilin ya sa ta yi wannan badarar ko mijinta ya kuɓuta daga azabarsu. Jin abin da ta faɗa ya sa Badakaren bushewa da dariya, ajiyar zuciya mijinta ya sauke ya sunkuyar da kai ƙasa sai dai duk abin da yake faruwa yana kallonsu ta gefen idonsa. Cikin shammata Badakaren ya saka hannu ya bigi tsakiyar cikinta da ƙarfin gaske, azaba ce ta ratsa ilahirin jikinta ta saki razananniyar ƙara. Ganin haka ya sa jikin mijinta ya riƙa karkarwa ransa ya yi mummunan ɓaci, yana shirin yunƙurawa don yin magana Mahaifin Kyauta ya zungure shi a fakaice cikin raɗa ta furta masa, "Ka da ka yi wani yunƙuri don komai zai iya faruwa daga kai har mai ɗakinka." Babu yadda ya iya haka ya koma ya yi laƙwas yana yin hawayen zuci saboda ɓacin rai, Badakaren ne ya miƙe ya koma wurin zamansu don irin dukan da ya yi mata a ciki ya tabbata idan mijinta ne zai magantu, ganin mijin nata bai tanka ba kuma bai yi wani yunƙurin dakatarwa ba ya sa ya yadda ba matarsa ba ce. Sabon ciwo ne ya taso mata gadan-gadan ganin haka dabara ta faɗowa sauran mutanen da suke ɗaure a jikin itace ɗaya, yunƙurawa suka yi da ƙyar suka tashi suka tsugunna don sun tabbata idan ba haka suka yi ba babu yadda za a yi ta iya haihuwar abin da yake cikinta lafiya ƙalau. A daidai lokacin da suka tsugunna kan jariri ya taho cikin azaba ta ƙwallah wata gigitaciyyar ƙara sai ga jariri ya faɗo, jaririn ne ya fara wutsul-wutsul a cikin ƙasa da gwiwoyin ƙafarta take yunƙurin ɗaukansa amma ta kasa. Kukan jaririn ne ya cika dokar dajin don haka tausayinsa ya ratsa zuƙatan mutanen wurin, mahaifiyarsa ta kifa kanta a kansa ta rushe da wani irin matsanancin kuka.

Tamkar dirar mikiya haka ta ji maganar babban Badakaren a kanta, tana ɗagowa ta riske shi ya ɗauki jaririnta. Tsugunnawa ya yi ya ciro wata kaifaffiyar aska ya yanke masa cibiya sannan ya saka aka kwanceta. Mamaki ne ya kamata sai kuma take ganin kamar tausayinta ya ji har ya sa aka kwance ta. Jaririn ya miƙa mata sannan ya sa aka ɗaure mata sarƙa a ƙafafuwa biyu, saitin fuskart ya koma suna fuskantar juna sannan ya ce, "Kin samu wannan rangwamen ne domin biyan buƙatar kaina, yau ita ce ta kasance ranar shaƙatawa a Daularmu don haka zan fanshe ranata a kanki." Ƙirjinta ne ya buga sakamakon yadda take jin gabanta yana yi mata wani irin raɗaɗin azaba, uwa-uba ga babu wani gyara da ta samu a matsayinta na mai jego. Kallon jikinta ta yi ta ga yadda jini yake bin ƙafarta kace-kace, kasa tanka masa komai ta yi sai hawaye da ke bin idanunta. Tana ji tana gani haka Badakaren ya sa aka rirrriƙeta ya fara biyan buƙatarsa da ita a gaban mutane, saboda azabar da take ji sai da ta yi suma biyu sannan ta farfaɗo ta dawo hayyacinta. Jikin sauran mutayen wurin ba ƙaramin sanyi ya yi ba, mijinta ban da huci babu abin da yake yi. Fatar da ta rufe ƙirjinta ta ciro ta naɗe jaririnta a ciki ta rungume, tana haɗa ido da mijinta ya sunkuyar da kai cike da tausayawa. Yadda suka ga rana haka suka ƙarasa ganin daren, gari na yin haske Dakarun suka tashe su suka ci gaba da tafiya, a galabaice suka ci gaba da cira ƙafafuwansu suka ƙara ɗaukan hanya da yin tafiya mai nisa. Sai da suka shafe wuri guda sannan suka ƙarasa babbar ƙofar da za ta sada su da Daular. Dakarun bakin ƙofar ne suka fara yi musu barka da zuwa, domin su ne tawaga ta biyu a cikin Dakarun da sarki ya tura fataucin bayi waɗanda suka dawo. Saura tawaga biyu da ake saka ran ganin ta hanyar da za su ɓullo.
Chapter 15 · 0% Book details