← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 46

Sashe 17

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rukunin bayi suka rinƙa wucewa kala-kala, kowanne wuri suka wuce da irin kallon da suke yi musu wanda hakan ba ƙaramin sanyaya jikinsu ya yi ba. Ɓangare-ɓangare ne a cikin gidan masarautar wanda ya haɗa da ɓangaren bayi masu aikin wahala kala-kala. Ganin irin baƙar wahalar da bayin suke yi ne ya sake sanyaya jikinsu wasu daga cikinsu har suka fara zubda ƙwallah tun kafin a sama musu gurbin zama, a wani katafaren fili aka tsayar da su mutane sai kallonsu suke ƙananan maganganu suna tashi a wurin. Kamar saukar ungula ba su yi aune ba haka suka hangi wani gabjejen mutum zaune akan kujera mai siffar mutum wanda ya duƙar da kai ga kwari da baka saƙale a wuyansa kamar yadda kujerar ta zame masa mazauninsa kodayaushe. A razane suka dube shi ganin a kan abin da yake zaune, da sauri Dogaransa suka ƙaraso suka fara kafa masa tanti tare da sauron fadawansa. Ransu ba ƙaramin ɓaci ya yi ba sakamakon ganin kamar cin zarafi ne ake yi wa al'ummarsu ta maharba, suna girmama duk wani abu da ya shafi maharba da faruta. Don haka kusan lokaci ɗaya suka sunkuyar da kai ƙasa zuciyoyinsu babu daɗi. Cike da izza, ɗagawa da taƙama Sarki Damina ya dube su a wulaƙance yana faɗin, "Ya ku wannan ƙasƙantacciyar al'umma taɓaɓɓu ababen taɓewa. Ku sani ba tun yau ba ina cike da ƙishirwar samunku don haka sai na shayar da ku ruwan azaba mai raɗaɗi, duk wani mummunan al'amari da yake faruwa da Daular nan ku ne sila don haka za ku ɗanɗana kuɗarku." Ya gama magana ya dubi ɓangarensa na hagu, wani ƙosasshen ƙato ne mai siffar samudawa a tsaye yana jiran umarninsa. Nuna wurin da su Mahaifin Kyauta suke tsaye ya yi sannan ya nuna wani matashin saurayi yana cewa, "A ɗauko min wancen ƙasƙantaccen karen." Dogarin na jin haka ya ƙarasa bakin wani daro ya ciro baƙar sarƙar sasari ya ƙarasa gabansu ya zargo wuyan matashin da sarki Damina ya nuna. Da yake har lokacin a ɗaure suke nan take gabaɗaya suka kife a ƙasa, a wahalce suka fara ihu saboda azabar buguwar da suka yi wasu daga ciki kansu har fashe wa ya yi. Sai da ya tusugunna ya kunto saurayin sannan ya sake zargo wuyansa yana jansa a ƙasa har gaban Sarki Damina, da ƙarfi ya sa ƙafa ya take kan saurayin cikin ƙasa yana sake murza fuskarta a ƙasa. Lokaci ɗaya ya bushe da wata dariya mara daɗin saurare, matashin saboda azaba ban da wutsul-wutsul babu abin da ƙafafuwansa suke yi. A gadarance ya dubi dubbanin al'ummar da ke wurin yana faɗin, "Daga wannan rana da muke ciki wannan ƙasƙantaccan bawan zai kasance haka a kodayaushe a tare da ni, kullin zai kasance yana cin ƙasa daga yau ita ce abincinsa" Cikin haɗin baki gabaɗaya suka furta, "Sarauniya Sha kundum ta ci gaba da jan ragamar mulkinka ya kai wannan adalin sarki mai cikakken iko. Mun fansar da kanmu gare ka duk yadda ka ga dama ka yi da mu, mu masu biyayya ne a gare ka." Kan Sarki Damina ne ya sake fashewa saboda jin daɗin kambabawar da suka yi masa, ya dubi wani dogari da ke gefensa sannan ya sake cewa. "Yau ranar farinciki ce a gare mu don haka a je a fito da Yarima a kai shi ga ƙasƙantattun can da suka fito daga la'ananniyar zuri'a." Mahaifin Kyauta ne ya sunkuyar da kai ƙasa cike da takaici don irin cin zarafin da Sarki Damina yake yi musu tun da suka zo duniya ba su taɓa ganin irinsa ba. Kasancewar sun san yanayim ciwon yarima ya sa Dogarawa huɗu suka tafi don taho da shi, ba a ɗauki lokaci ba suka dawo da shi a rirriƙe yana wawure-wawure alamun yana son ya yago naman ɗaya daga cikinsu. Zuwan da aka yi da Yarima wannan wurin ba ƙaramin sake ɗugunzuwama hankulansu ya yi ba, jikinsu ban da karkarwa babu abin da yake yi. Mahaifiyar Kyauta cikin kuka ta dubi Mahaifin Kyauta da ke ɗaure a wani itacen daban, ta yi ƙasa da murya hawaye na zuba tana faɗin. "Sa'a dai mazaje uban Kyauta amanar shamuwa. Yanzu haka za mu ƙare rayuwarmu cikin wannan ƙasƙancin da azabtarwa? Babu wani taimako da Abar bauta za ta yi mana ta kawo mana mafita."

Jin tambayarta ya sake raunata zuƙatan sauran matan da ke wurin, lokaci ɗaya hawaye ya wanke fuskokinsu suna kallon Mahaifin Kyauta don jin abin da zai faɗa. Muryarsa na rawa dube su ɗaya bayan ɗaya ya ga yadda duk suna lalace lokaci ɗaya suka fita hayyacinsu sannan ya mayar musu da martani, "Dawa da buɗa mana abar bauta ta shiga lamuranmu. Tabbas shigowata wannan Daular ya farkar da ni daga dogon baccin da muke yi, a wannan Daular da muke ciki ƙarfi da ƙarfin sihiri ba zai fusshe mu ba face mu zuba na mujiya mu ga yadda rayuwarmu za ta kasance. Shigowata Daular nan ya tunasar da ni labaran da magabatanmu suka sanar da ni akan mummunan lamarin da ya faru a ɗaruruwan shekarun da suka gabata tsakanin wannan Daular da yankinmu wato al'ummar Maharba." Cikin kuka wani magidanci ya karɓe zancensa da cewar, "Idan suka hallakar da mu kenan sun yi nasara a kanmu? Shi ke nan za a rufe shafin farauta da mafaruta a faɗin duniya? Kuna nufin nan gaba tarihi zai bayyana Maharba ƙasƙantattu ne kamar yadda wannan azzalumin sarkin nan yake faɗa?" Mahaifin Kyauta ya sauke ajiyar zuciya ya sake dubansu cike da tausayinsu a fuskarsa ya furta, "Tun shigowata cikin Daular na na hangi mutuwata da ƙwayar idona, na sani kun sani tun da muka shigo daular nan babu mai fidda mu cikin salama, sai dai jikina yana ba ni da sannu nan ba da jimawa ba wani mummunan al'amari zai faru da su domin jinin Maharba ba zai tafi a banza ba, koda za su ƙarar da mu kaf waɗanda muke nan gabansu na tabbata akwai ɓurɓushin zuri'armu kuma sai sun fansar da jininmu..."

Bai ƙarasa magana ba suka riski wata gigitacciyar tsawar da ta sake hautsina ƴaƴan cikinsu, nan take suka sake lura da duniyar da suke ciki. Suka riski muryar Sarki Damina yana cewa Dogarawansa, "Ku ɗauki Yarima ku kai shi tsakiyar wulaƙantattun can na yarje masa ya yi duk yanda yake so da su kafin na san irin hukuncin da zan yanke musu." Da sauri suka fisgi Yarima har za su nufi wurin su Mahaifin Kyauta ko me Sarki Damina ya tuna a gaggauce ya dakatar da su da cewar, "Ku dakata!" Ilahirin mutanen wurin ba ƙaramin mamaki suka yi da jin kalaman Sarki Damina ba, da kansa ya miƙe ya kira wasu zaratan dakaru guda goma ya sa suka fara kwance su ɗaya bayan ɗaya. Wani sanyin daɗi ne ya ratsa su a tunaninsu wani sassauci za su samu, da kansa ya sa aka fara ware ƴanmatan cikinsu gefe ɗaya sannan ya sa waɗannan Dakarun suka tafi da su sihirtaccen gidansa da ke bayan gari. Ganin haka ya sa suka fashe da kuka don ba su san abin da zai aiwatar musu ba, yana gama zaɓarsu ya sa aka sake mayar da sauran aka ɗaure. Ya janyo hannun Yarima da kansa ya kawo shi tsakiyarsu, gudun kada ya haɗa da shi ya sa shi matsawa da sauri. A haukace Yarima ya kwarmata mahaukacin ihu, zaro idanu yake yana wage baki. Wani tsalle ya buga cikin shammata ya fisgi jaririn da ke hannun mai jegon da suke kira da Lantan, yana fisgarsa ya riƙe ƙafafuwansa da hannuwansa biyu, kan jaririn na ƙasa ƙafafuwansa suna sama. Tsalle ya fara yi a haka daga shi da wani guntun ganyen da ya rufe masa al'aurarsa, tsallen da yake yi sa ganyen ya faɗi ya zama babu komai a jikinsa. Cike da azaba jaririn ya fara ƙwalla matsanancin kuka, lokaci ɗaya Sarki Damina ya ƙyaƙyace da dariyar ƙeta yana nuna wurin da yatsansa. Ganin haka ya sa sauran mutanen wurin suma suka fara ƙyaƙyata dariya mugunta, sai da ya ƙara ɗaga jaririn ya yi wani irin gurnani da ƙarfin tsiya ya yaga jaririn gida biyu kowanne hannunsa ɗaya da ƙafar jaririn, take ya sake tsanyarewa da wani irin gigitaccen kuka na fitar hayyaci, Yarima ya riƙa nunawa mutane sannan ya saka baki ya cisge kunnensa na hagu. Ganin haka ya sa nan take mahaifinsa ya faɗi a wurin sumamme, Mahafiyarsa tun lokacin da ya karɓe shi ta fara wata irin shaƙuwar baƙin ciki da tashin hankali. Lokaci ɗaya tari ya sarƙe ta; ta fara aman jini ana cikin haka ta sulale a wurin matacciya.
Chapter 17 · 0% Book details