← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 46

Sashe 21

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dum! Na ji kaina ya yi min tamkar an ɗora min dutse, haka kawai na ji hajijiya na neman ɗaukana har sai da na jingina kaina jikin sauran mutanen da ke tare da ni. A hankali na samu damar buɗe idanuna, ban yi aune ba na hango wata ƙasaitacciyar kujerar zinari daga can nesa da ni, Jarumin mazajen da ya saba faɗo wa rayuwata na hango yana kirana da hannunsa. Farin dokin ne ya fara takowa har ya zo gabana yana ci gaba da goga kansa a jikina, karon farko na kalli Kyauta sannan na ce, "Kyauta kina ganin farin doki a kusa sa ni?" A wahalce ta girgiza min kai ta ce, "Sai dai idan gizo idanunki suke yi miki amma yanzu haka muna wani wuri mai iya tsinka zuciya, na shiga tashin hankula kala-kala amma ban taɓa cin karo da makamancin wannan ba." Ina yunƙurin bata amsa na riski sanarwar mutumin da nake tsammanin shi ne mai mulkar wannan yankin bakiɗaya, sai da ya miƙe tsaye sannan na ji fara sanarwar da cewar. "A ware mini al'ummar Maharba ɓangare guda ba na buƙatar a haɗe su da waɗannan bayin da suka shigo wannan Daula tamu mai albarka yanzu." Tun bai rufe baki ba Dogarawan suka zabura da sauri suka fara yi mana iyaka da al'ummar da aka kira da Maharba. Tun da na ji ya ambaci haka na riƙa leƙawa koda zan samu na yi tozali fa mahaifana, duk da na aminta da zuciyata ba ƙaramar yaudarata take yi ba. Kwatsam! Kamar a mafarki na yi kwalli da su, kamaninsu duk sauyin yanayin da suka samu ba zan mance su ba. Iyayena da nake ƙishirwar gani, da su na yi tozali a lokacin da ganinsu ba zai yi mini amfani ba. Hawayene ke bin idanuna bibbiyu ya yin da na sake tabbatar da wanzuwar halitata tana da sanadi da ƙaddara wacce bawa baya taɓa tsallake mata. Ina cikin wannan yanayin na ji ya sake faɗin, "A kunkunce wannan tagawar sannan a zaɓo mini kyawawan ƴanmata daga cikinsu, a wannan ranar ba zan kira Yarima ba domin ya fi ƙarfin gabaɗaya waɗannan ƙasƙantattun don haka a zaɓi nagartattu sha biyar a tura masa su." Babu musu suka aiwatar da abin da ya umarce su, suka shiga kwance mu nan take daɗi ya mamaye zuciyata ko babu komai za mu samu hutun ɗan taƙaitaccen lokaci. Hannun Kyauta na riƙe muka riƙa kutsawa tsakiya don kada su ɗauki ɗaya daga cikinmu domin tun da na ji an ce za a kai ƴanmata wurin Yariman Daular na san ba abin kirki zai aikata mana ba, ina daga lungu ina hango yadda ake fitar da ƴanmata mafi yawa daga cikinsu iyayensu na jansu suna ihun rabuwa da su. Ban yi aune ba na ga wani Gabjejen Badakare ya fisgi hannin Kandala, a hargitse na yi kukan kura na cafko hannunta ya fara fisgarmu tare. Yana ganin ina jan hannunta ya ƙaraso a fusace ya ɗauke ni da wani irin gigitaccen mari wanda zafinsa ya sa na kife a katsa tare da jaririn hannuna, cike da azaba ya tsanyare da matsanancin kuka. Inna wuro ce ta ƙaraso wurina ta karɓe shi ina yunƙurin tashi ban yi zato ba na ji ya dawo ya fisge ni, ya hankaɗa ni da ƙarfin gaske. Kandala na ganina ta rugume ni tana kuka ni ma ban da zaɓi da ya wuce na zubda na wa hawayen, muna cikin wannan yanayin na ji Badakaren nan ya kwarara ihun da ya sa idanunmu suka koma kansa. Zaro idanuwa na yi cike da fargaba abin da na gani, gefen fuskarsa ce ta hau daddarawa haka kawai kamar ana yaga tsuman zani. Wani abin mamaki ɗaya ɓarin wurin babu abin da ya same shi. Ganin yana neman hautsina wurin ya sa Sarki Damina ya tura wasu daga cikin Dogarawansa suka kai shi turu (Gidan mahaukata.) Da kansa ya ƙaraso wurinmu ya fara zaɓar ƴanmatan da za a kaiwa yarima, ba zato na ga ya sa da ni a ciki wanda za a kaiwa Yarin, hakan ya sake sabbaba mini kaɗawar hanta. Mu goma sha biyar ya wara daga cikin waɗanda aka zaɓa sai ƴanmata biyar da na ga ya lissafa daga ciki har da Kandala. A gaban dubbanin jama'a babu kunya maganaina suka hango min yadda ya fara kai hannuwa jikin su Kandala yana taɓa al'aurarsu. Duka babu wacce bai kai hannu jikinta ba sannan ya bada umarni da akai masa su can gidan shaƙatawarsa da ke bayan gari. Mu kuma ya sa aka tarkata mu aka wuce keɓaɓɓan gidan Yarima da mu, tun daga tsakar gidan Dakarun suka yi ta tsige mana suturar da ke jikinmu. Tamkar dabbobi haka suka tura mu cikin ɗakin da na hangi wani matashin saurayi na zaune ya kifa kansa da gwiwa, jin motsinmu ya shi ɗagowa yana zaro idanu haɗe da kallonmu ɗaya bayan ɗaya. Ban yi mamakin ganinsa ba domin fuskarsa ba baƙuwa ba ce a wurina, sai dai na yi mamaki a tsawon shekarun da ya shafe yana ziyartar duniyata da bai sanar da ni yana da alaƙa da wannan Baƙar Daular ba. Dama shi ƴan biyu ne bai sanar da ni yana da wani ɗan'uwan ba? Idan haka ne kenan yana da alaƙa da zuwanmu wannan azzalumar Daular, ya aka yi na bar shi a filin can na sake riskarsa a wannan ɗakin har na ji ana ambatonsa da sunan Yarima? Ban gama jerawa zuciyata tambayoyi ba balle na bawa kaina amsa na ji ya yi kukan kura ya fisgi ɗaya daga cikinmu ya fara biyan buƙatarsa da ita, kuka nake mai tsuma zuciyar mai sauraro tausayin kaina ya mamaye zuciyata. Yana gama amfani da ita ya rufe ta da duka kamar ya samu jaka har sai da ta daina motsi. Haka ya bi mu ɗaya bayan ɗaya yana amfani da mu, wanda ni ce mace ta ƙarshe da ya keta wa haddi ya raba ni da martabata ta ƴa mace. Tun yana jikina na ji ya fara wani irin munshari mai ban tsoro wanda haka ne ya tabbatar min da bacci ya ɗauke shi, da ƙarfi na ture shi na koma gefe ina ci gaba da hawaye. Dakarun da suka kai mu ba su suka zo suka kwashe mu ba sai da dare ya tsala sannan aka ɗauke mu aka kai mu wani ɓangare wanda na ji suna kira da, ƴantattun bayi. Wani abu da ya tsaye mini a rai bai wuce yadda komai na Yarima yake min kamanceceniya da Jarumin da ke ziyartata ba, sai dai lokaci ɗaya tsanarsa ta mamaye zuciyata na ji danasanin shigowarsa rayuwata. Gari na waye da shi na yi tozali a tsakiyar kaina ina yunƙurin magana na ji ya furta min, "Kada laifin wani ya shafi wani domin kin san kama da wane bata wane." Bai jira cewata ba ya ɓace min da gani, a hankali na miƙe ina zagaya lungu da saƙon wurin tafiyata keda wuya na ji Dogaran Sarki sun zo da shelar kiran gaggawa da Sarki Damina yake yi ga waɗanda aka kai ɗakin yarima.

Wannan shine shafi na biyun ƙarshe na free pages. Hajiyata kada ki bari a yi wannan tafiyar domin wasan yanzu ya fara ɗaukan zafi💃🏼 Wai ko dai Yarima ya warware ne🥵🤣😂

*KU MATSO KU TAHO*💃🏼

Wannan labarin salonsa na daban ne💃🏼 cike yake da sarƙaƙiya da tsananin ban tausayi😰 ku dai kar ku bari a yi babu ku.🏂

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 400 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Idan kati ne MTN. Idan kika bari na kammala cmplt 700 ne.

Idan kin san kin sayi ɗaya daga cikin litattafan nan *AN YA BAIWA? KO DUBU JIKAR MAI CARBI KO ZAUJATU JINNUL-ASHIQ* za ki biya 300 wannan ragin na waɗanda suka sayi wannan littafan nan ne kaɗai.💃🏼

Na ɗaga hannuwa riƙe da takobi da kwari da baka na salaƙe na sunkuyar da kai ina miƙa gaisuwa da kirari cau cau cau cau, sai ni Ameera 'yar Alhaji Adamu Amiriyan Mamanta, uwar Aslam da Ayman Amanar Oganta turmi sha daka 🥰
Wiiiiiiihuuuuuuhuuuu mace mai kamar maza ko cikin maza sai an duba domin wuya ake yi wa lissafi daɗi sai an jinkirta. Allah dai ya biya wuya a ƙofar Na'isa, wuya a ƙofar Kabuga wuya a ƙofar Nasarawa wuya a doka wuya, wuya a ƙofar kansakali mun buga a dajin Jemagu mun buga a dajin Falgore ko dajin Sambisa albarka. Sai ni ƴar Kanawan dabo amanar mutanen Rigana, idan ka ga matsoraci ko rago a Rugana baƙo ne domin jarumi ba'a nuna masa hanya, sa'a dai 'yar gaban goshin *FIRST CLASS WRITER'S* Amanar Marubuta La'ilaha'illahu. Sai ni ta hannun Matar Habibu ni ce dai ƙawar Mum Amnash amanar Masoyanta, cau cau cau cau makaranta ku matso ku ji wannan kafcan don idan kika bari aka yi babu ke an barki a baya. Domin duk wacce ta bari aka yi wannan tafiyar babu ita ta fita daga cikin jaruman mata masu aji.🌚

*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
[11/25, 7:00 AM] Ameera Adam🌚: *BAƘAR DAULA*

©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

Last free page 10
Chapter 21 · 0% Book details