← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 46

Sashe 19

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, ban rubuta don cin zarafin kowacce ƙabila ko yanki ba. Daga sunayen garuruwa zuwa na abin bauta duk ƙirƙirarru ne, kuma ban lamunce a sauya min littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba.⚠️

Free page 9

🥳 in ka ji busa tabbata Sarauniya ce ta ƙaraso, ina kuke matan ƙwarai, mata ba muna mata ba, shin kin jaraba kayan *HONEY-DROPS* me kike jira har yanzu?, Manyan mata, mata masu aji na ta dafifi wajen kwasar kayan gyara, me ya sa za ki kashe kanki da ƙuruciyarki, ko tsohuwar ma na zuwa karɓar nata, kina fama da matsalar bushewar gaba, ɗaukewar sha'awa da ni'ima, ƙaiƙayi ko ƙurajen gaba, jin zafi yayin tarawa da maigida, sanyi ya taɓa miki mahaifarki?, Kina ta allura da shan magunguna ba su miki aiki ba, wane kalar infection kike fama da shi?, Staphylococcus, Gonorrhea, Syphilis, UTI, STDs ne?, Share hawayenki kukanki ya ƙare je ki nemi *HONEY-DROPS INFECTION FLUSHER* ke da sanyi sai dai ki ba da labari, kin gama cacar kuɗi, cikin kwana uku zaki fitsarar da duk wani sanyi da dattin da ke tattare a mararki, ki gyara zamanki gidan aurenki don sanyi kashe mace yake har buzunta, duk wani magani da za ki sha muddin da sanyi a jikinki iyakar shi cikinki, ba zai sauka ba. Magani ne ingantacce made of herbs, In kin gama da wannan akwai na gyaran other room, akwai Exclusive Gumba ta manyan mata ke nan, ko matar Gwamna ita take sha, ga Gumbar babbar mace mai tada tsohuwar soyayya, akwai fa tsuumi na matan gaske, akwai *HONEY FLOOD TSUUMI* kan ƙiftawar ido ni'ima ta yi ta kwararo miki, akwai BUJENTA JAGAB, da Tsuumin Ɗafau, daga jin sunan kun san akwai zance na bar muku ku ƙarasa, akwai sauran kaya masu zafi🔥

Muna da bridal package

Diamond - 100k
Gold - 50k
Silver - 30k

Ga kuma na postpartum (wanda suka haihu don dawo da martabarsu)

Diamond - 50k
Gold - 30k
Silver - 15k

Kuna iya samun mu ta 08167888934, ko 08067770852

Duk wata al'ada da ake gudanarwa kafin ya shiga tsaunin Boka mai zamani sai da ya aiwatar, daga matsayar da Dogarawansa suka saba tsayawa wannan karon ma a nan suka yi carko-carko. Ko ba a faɗa musu ba sun fahimci sauyi a tattare da Sarkin nasu, sai dai sun ta'allaka hakan ne sanadin baƙin bayin maharban da aka yi wanda su kansu ba su san takamaiman tsattsamar alaƙar da ke tsakaninsu da Maharban ba. Lokacin da Sarki Damina ya shiga cikin Kogon dutsen tsirara ya same shi a tsakiyar kogon, hannunsa ɗaya ɗauke da ƙwarya ya ɗaga ta sama yana biya waɗansu irin ɗalasiman tsafi. Wata jar akuya ce tsaye a gabansa da alama tsaface ta yake yi da baƙaƙen zakaru uku, sai wani gudan abu da ke hannunsa da hagu tamkar gudan jini yana matsa shi a tsakiyar kan akuyar. Jin motsin Sarki Damina ya sa shi waigawa a hargitse don a wannan ranar ya tabbata babu wani mai kawo masa ziyara, daskare wa Sarki Damina ya yi saboda fargaba, tsoro da tashin hankali. Saboda gabaɗaya ya manta da wannan ranar ba ya ziyartar Boka mai zamani domin ranar ta kasance masa ranar neman biyan buƙatarsa ga Sarauniya Shakundum. Tun boka mai zamani bai yi magana ba bakin Sarki Damina na rawa ya furta, "Ina neman gafarar zunubin da na aikata na kasance mai mantuwa a gafarce ni kada Shakundum ta yanke mummunan hukunci a kaina." A fusace Boka mai zamani ya nuna masa ƙofar kogon a hargitse yana faɗin, "Ɓace wa ganina idan ba haka ba yanzu na roƙar maka a zaba wurin Sarauniya Shakundum ta la'anceka ka ɗaiɗaice." Kamar sabon munafiki haka Sarki Damina ya fice sum sum sum rai a ɓace, cike da hargowa ya rufe Dogarawansa da faɗan babu laifin tsaye balle na zaune.

Lokacin da Sarki Damina ya sa aka kai su Mahaifin Kyauta ɗakin duhu gabaɗaya sun gama galabaita saboda tsananin zafin rana da yunwar da take sasaƙar cikinsu, a can tsakiyar gidan masarautar ɗakunan suke. A ƙarƙashin ƙasa aka samar da wurin saboda waɗanda suka aikata mummunan zunubi ko kuma waɗanda Sarki Damina ya yi mummunan fushi da su, baƙiƙƙirin wurin yake saboda babu ɗigon haske da yake ratsawa da ciki. Duk yadda ka kai ga son ganin tafin hannunka ba za ka iya ganin ba balle waɗanda aka saka ku tare da su, sai dai ku riƙa lalubar juna kuma yin magana a haka. Cikin ɗakunan cike yake da kunamu suna harkokinsu kamar yadda kiyasai suke kai kawo a doron ƙasa. Ana saka su ita ce ta fara yi musu marhabun lale ta rinƙa sakar musu cizo ta ko'ina ban da ihun yara da na iyayen su kansu babu abin da kake ji. Da suka lura ihu ba zai kai musu ba haka suka riƙa lalube da hannuwansu da sun ji ƙatuwar kunawa su saka hannu ko ƙafa su murtsuke ta. Duk da haka ko kaɗan ba su tsira ba haka suka haukace saboda azabar harbin da take yi musu, a yammaci zuwa wayewar gari ƙananan yara huɗu ne suka rasu da manya biyu sanadiyyar mummunan harbin da kunamar take yi musu. Washegari suna nan zaune jigun-jigun cikin baƙar azaba suka ji an buɗe ɗakin da suke ciki, sai a lokacin da hasken rana ya hasko suka fahimci a zaune suka kwana har gari ya waye, cike da ƙarajin ban tausayi suka fashe da kuka suna faɗin, "Ku taimaka ku cece mu duk abin da kuka saka mu na aikin wahala mun amince za mu yi bakin ƙoƙarinmu." Badakaren da fuskarsa babu alamun wasa ya furta, "Ba don Sarki Damina ya so ku da rahama ba da a nan za ku dauwamma har sai kunamun ciki sun hallakar da ruhinku. Ya ba ni umarnin a fito da ku zuwa sararin haraba zai rarraba ku gida-gida domin kowa ya san irin aikin da zai rinƙa yi." Saboda murna har kwanciya suka yi suna gode masa suna cikin godiya suka ji ya buga musu tsawa yana cewa, "Yau kwananku nawa rabonku da abinci?" Bakinsu har rawa yake suka furta, "Yau kwana huɗu." Girgiza kai ya yi sannan ya furta, "Idan kun je za ku ci a cen." Daɗi ne ya mamaye zuciyarsu sannan ya buɗe musu suka riƙa fitowa ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda ya san su a baya matuƙar ya gan su a wannan lokacin ba zai taɓa gane su ba, saboda wani irin burɗun-burɗun da jikkunansu ya yi. Da wata irin rama ta ban mamaki da suka yi sun yi wani irin baƙi tamkar waɗanda suka shekara suna matsananciyar jinya.
Chapter 19 · 0% Book details