Sashe 20
Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sarki Damina na sauka daga tsaunin boka mai zamani kai tsaye gida ya wuce, yana shiga turakarsa ya samu Usaina zaune ta haɗa kai da gwiwa. Duk duniya babu abin da Sarki Damina ya ƙi jini ya ƙi tsana sama da ya ga ran Usaina a ɓace, don haka a rikice ya dube ta yana tambayarta. "Yake faruncikina uwar gida a wurin Damina uwar Yarima bada kanki a sare. Ya ke Hasana shin waye ya taɓa min ke yanzu na sa a sauke min kansa ƙasa ko shi ɗan gidan uban waye, idan kuma bautarwa kike so ki gaya min wanda kike so duk matsayinsa a yankin nan na sa a bautar da shi." Sai da ta goge ƙwallar munafurci sannan ta ce, "A lokacin da Maharban suka shigo Daular nan haka kawai na ji jikina ya ba ni zuwan su babu alheri a ciki, na ji an ce har da wacce ta zo da jariri a ciki ko?" Usaina ta yi tambayar tana ƙura wa Sarki Damina idanu don ta karanci yanayinsa, tun ranar da tawagar farko ta shiga cikin Daular Bawanta mai yi mata leƙen asiri ya ke kai mata ɓoyayyun bayanai, har ta kai ga ya sanar da ita zuwan tawaga ta biyu da jaririn matar nan kafin Yarima ya hallaka shi. Sarki Damina na gama jin bayaninta tsaf ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya sannan ya furta, "Tuni shalelenki ya gama da shi indai wannan jaririn ne." Cikin kissa ta sake tambayarsa nan take ya zayyana mata duk irin kisan rashin imanin da Yarima ya yi masa. Ajiyar zuciya ta sauƙe a fili saboda ko ba komai ta san ta gama da jaririn da Boka mai zamani ya sanar mata ya wanzu a nahiyar maharba, babban aikin da ke gabanta bai wuce ta gano wane ne tauraro na biyu da na uku da ke cikin masarautarsu ba domin tana gudun kada gaba allura ta tono garma. Ta san ɗayan tauraron cikin maharban shi kansa ba zai yi mata wuyar gani ba domin sannu a hankali za ta saka Sarki Damina ya riƙa salwantar da ruhinsu ɗaya bayan ɗaya. Ganin yadda Usaina ta bashi fuska ya sa shi jin daɗi domin idan bata ga dama ba hatta ɗakin akwai wurin da take yi masa iyakarsa. Don haka a daren ranar Usaina ta bashi haƙƙinsa musamman da ta tabbatar da ta bashi haɗin da Boka mai zamani ya bata ta tashi kuma ko kaɗan bai tambayeta ba balle ya musa mata, tamkar ajiya ya bata haka ya amsa hannu bibbiyu ya kafa kai ya shanye. Washegari sai da yamma ta yi sosai sannan ya saka Dakarunsa su fito da iyayen Kyauta, haka aka sake fito da su jama'a sai kallonsu suke yi. Suna ƙarasawa tsakiyar filin aka saki kiɗe-kiɗe da bushe-bushe, masu giya suka fito da ita suka riƙa sha suna tamɓele a wurin. Abin da ya ɗaure wa su Iyayen Kyauta kai bai wuce yadda suka ga duka al'ummar wurin sun yi ado da zanen fari da baƙi ba. Hatta Sarki Damina da Dogaransa duk sun fante jikinsu da baƙi da fari, sai da suka ƙura ido suka lura da cewa zanen jikin mutanen ba komai ba ne face zanen idanu. Kowannensu babu wanda ba ya zance zuci a cikin zuciyarsa, suna tsaye a tsakiyar rana aka kawo musu dafaffiyar jar dawa babu komai a cikinta. A yunwace suka ɗauka suna na ci kafin wani lokaci tuni sun cinye sakamakon dama ba wata ta kirki aka kawo musu ba, wani irin jan ruwa aka kawo musu kamar turɓaya. Shi ma ba su ɓata lokaci ba suka daka masa wawa, nan take suk shanye shi. Sarki Damina ne ya ɗaga hannu lokaci ɗaya mutunen wurin suka yi tsit, Waziri ya miƙe da wata sanda a hannunsa mai kan zaki ya fara kallon mutane ɗaya bayan ɗaya sannan ya ce, "Musha giya mu ji daɗi don yau ranar ido ce a gare mu babu wanda ya isa ya zura mana ido." A hankali Mahaifin Kyauta ya sake maimaita maganar ta shi don ko kaɗan bai fahimci komai a maganar ba, yana cikin nazari ya riski Wazirin ya ci gaba da cewa. "A yau ba za mu duba tsofaffin Bayi ba za mu ɗauki sadaukarwar idon babban dodo a wurin waɗannan la'anannun bayin maharban,
." Ya ƙarasa magana yana nuna wurin da su mahaifin Kyauta suke tsaye. Ilahirin jikinsu ban da rawa babu abin da yake yi, Waziri na rufe bakinsa ya ƙarasa wurin ya jango Mahaifin Gogo saurayin Kyauta. Sai da aka kai tsakiyar filin aka zaunar da shi a kan kujerar ƙasa aka ɗora kansa a kan hannun kujerar, wasu garadan Dogarai ne suka ƙarasa suka ɗaure hannuwansa ta baya sannan ya ɗauko kaifaffiyar wuƙa ban da sheƙi babu abin da take yi, saita ramin idonsa ya danna wuƙar da ƙarfi ya ƙwaƙwalo ƙwayar idonsa. Wani irin gurnani yake yi saboda azaba jikinsa na wani irin karkarwa kamar ransa zai fita, a cikin wani ƙoƙon kai ya saka ƙwayar idon sannan ya sake saka wuƙar ya ƙwaƙulo ɗayan idon sai kuma ya ɗebo wani ruwa mai koriyar kala ya zuba masa a ƙwayar idon. Daga haka Dakarun suka ɗauke shi aka wuce da shi ɓangaren makafin cikin gidan, wannan lamarin da suka gani ya sake ɗugunzuma hankulansu. Don haka wasu daga ciki suka riƙa zubda ƙwallah wasu kuma suna roƙon mutuwarsu kafin a ɗanɗana musu wannan ukuɓar. A karo na biyu Waziru ya zaƙulo Mahaifiyar Kyauta, ganin haka ya sa ta fashe da kuka mai tsanani tana ɗaga wa mijinta hannu, ko me Waziri ya tuna sai kuma ya hankaɗata ta koma, ya miƙa hannu ya janyo wata matashiyar yarinya da ba za wuce shekara goma sha uku ba. Tana kuka mahaifiyarta na riƙe ta haka Waziri ya fisgeta ita ma ba a ɗauki lokaci ba aka cire nata idanuwan aka wuce da ita. Bayan ita Wata mai tsohon ciki suka ɗauko ita ma sai da suka ƙwaƙwale nata sannan ya burma wuƙa a cikinta ya zaro jaririn da ke kwance a cikin cikinta. A daidai wannan lokacin ayarinsu Kyauta suka ƙarasa cikin filin manyansu da ƙanana, ƙura ce ta gauraye wurin saboda yawansu sakamakon tawagar dakaru biyu ce suka shigo. Yawan mutane da tashin hankalin da suka yi tozali da shi ya sa kowannensu ya sha jinin jikinsu, mummunan kamannin da danginta suka sauya ya sa ta gagara bambamce ainihin surarsu, sai dai a lokacin da ta gan su ta fahimci irin suturar yankinta ce. Lokaci ɗaya tunanin iyayenta ya faɗo mata hawaye ya ciko idanunta take tunanin halin da suke ciki, don a tunaninta ƙila tuni an gama da su.