Sashe 23
Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kafin Sarki Damina ya ƙarasa gidan shaƙatawarsa tuni aka tuɓe su kandala kowacce sai kare jikinta take yi cikin jin kunya kasancewar haka bata taɓa faruwa da su ba, lokacin da ya ƙarasa yana shiga ya hau ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya yana lashe baki domin ya jima bai haɗu da kyawawan ƴanmata kamar su ba. Kowacc ya je gabanta sai ya saka hannu ya ɗago haɓarta ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa sannan ya wuce wurin ta gaba da ita. Nan take ya ji zuciyarsa ta yi matsanciyar kamuwa da ƴanmata biyu daga cikinsu, kamar dabbobi haka ya saka su a gaba yana mu'amala da su, idan ya gama da wannan sai ya koma kan waccen. Ban da kuka da roƙo babu abin da suke yi masa, kallon Kandala ya yi wacce yake kwance share-share a jikinta ya furta, "Ƴan mata kukan me kike yi bayan a yadda na jiki kin saba, ba ni na fara sarrafa linzaminki ba?" Kuka ta fashe da shi a hankali ta furta, "Abar bauta ta shiga lamarinka amma ka taimaka ka ƙyale mu ya shugaba nagari." Duk da ya ji daɗin lafazinta duba da ƙanƙantar shekarunta ya sa ya dube sosai yana cewa, "Ba ma buƙatar jin wani abin bauta bayan Sarauniya Shakundum." Gyaɗa masa kai ta yi cike da gamsu, a yadda ta ji muryaraa ta yi tsammanin zai rabu da su kamar yadda ta roƙa amma sai ta ji ya sake lalubarsu yana ƙoƙarin biyan buƙatarsa. Babu yadda suka iya suna ji suna gani ya yi abin da zai yi da su ya gama sannan ya dube ta ita da Saro ya furta, "Daga yau ke da ita kun zama matan huce zafina." Za a bar ku a nan duk lokacin da na buƙace ku zan zo na same ku, kuma duk wacce ta nemi musamin zan sa a ɗauki mummunan mataki a kanta." Daga haka ya ɗauki wasu manyan ganyaye da yake rufe al'aurarsa ya ɗaura a ƙugunsa ya fice. Dakarun da ke bakin ƙofar turakar ne suka shiga suka fisgi sauran mutum ukun suka fita da su, aka bar daga Kandala sai Saro. Lokaci ɗaya suka rungume juna suna matsanancin kuka, kamar daga sama suka ji shigowar wasu ƴanmata wanda ko ba a faɗa musu ba sun fahimci bayi ne. Sababbin ganye suka kawo musu da abinci mai kyau sannan suka kalli su Kandala suna faɗin, "Tabbas kuna cikin masu daraja tun da a yau haɗuwarku kaɗai da Sarki har ya ƴanta ku. Ku taimaka ku roƙar mini Sarauniya Shakundum ta sassauta min baƙar wahalar da nake sha." Daga Kandala har Saro babu wacce ta tanka mata sai binta suke yi da kallo, don su ko kaɗan wannan ƴantawar bata faranta ransu ba.
Asubar fari a sirrance Boka mai zamani ya rikiɗa zuwa siffar Tsuntsun kai tsaye ya tashi ya nufi cikin gidan Sarki Damina, daga kan katangar ɗakin Usaina ya tsaya yana wani irin kuka da ba kowa zai fahimci inda kukan ya dosa ba. Cikin bacci Usaina ta yi mafarki da Boka mai zamani yana tsala matsanancin gudu ga wata baƙar guguwa na biye da shi, tana daga nesa har suka tunkarota gadan-gadan. Duk yadda ta kai ga yin gudu abin ya gagara ko ƙafarta ta gagara motsawa, don haka ta fara karara ihun neman ceton sai dai bata yi aune ba baƙar guguwar ta turnuƙe su gabaɗaya. A zabure ta tashi zaune jikinta na rawa, sai da ta buɗe idanunta ta riski kukan tsuntsun kamar yadda ya saba zuwar mata a duk lokacin da yake da wata muhimmiyar magana da ita. A hankali ta miƙe ta fice ta bar Sarki Damina buɗe da baki yana sakin munshari. Tana fita ta buɗe wani ɗan ƙanƙanin ɗaki da je can nesa da ɗakinsa tsuntsun na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ya yi girgiza ya dawo suffarsa ta ainihi Usaina ta dube shi ta ce, "Mai zamani akwai matsala." Boka ya dube cikin damuwa ya ce, "Ita ce take tafe da ni. Ni na ga masifa yau ganin idona." Nan take ya bata labarin duk abin da ya faru a kogon Tsafinsa, tana gama jin jawabinsa ita ma ta zayyana masa abin da ta gani a mafarkinta sannan ta ɗora da cewar, "Sirrantaccen bawana ya sanar da ni abin da ya hana ni bacci, wannan baccin ma da ya ɗauke ni ɓarawo ne kuma rabon zan ga wannan mafarkin ne. Ya sanar da ni an kawai Yarima yanmata shabiyar kuma tun da ya gama mu'amala da su yake wani irin bacci da bai taɓa yin irinsa ba. Yana farfaɗowa ya fara wani irin tarkacen amai, kasan aman me aka ce min ya yi?" Boka ya girgiza mata. Usaina cike da damuwa ta ci gaba cewa, "Ina laƙaninnikan da ka ba ni na bashi yana yaro?" Boka ya gyaɗa kai.Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Su ya amayar an ce har da baƙar allura da kan maciji. Kai ba za su lisaafu ba kuma wai yana dawowa hayyacinsa ya fara cewa me yake yi a wannan gidan. Mai zamani in taƙaice maka labari alamu sun nuna Yarima ya dawo hayyacinsa don har ni da Damina mun je mun gano halin da yake ciki." Boka mai zamani ya yi taku biyu jiki a sanyaye ya ce, "Ta faru ta ƙare... Amma duk da haka ba za mu tozarta ba zan kira Manyan baƙaƙen aljanun ƙarƙashin ƙasa na nemi agajinsu. Abu ɗaya nake so da ke." Usaina ta zuba masa ido tana jiran jin ta bakinsa, boka mai zamani ya ci gaba da cewa. "Ko da wasa kada ki yadda Damina ya lura da halin da kike ciki. Ki sani har yanzu yana kallonki da sunan Hasana, ki nuna masa kin fi kowa farinciki da samun lafiyar Yarima haka zai sa mu sake samun yadda za mu murƙushe rayuwarsa." Usaina ta saki dariyar ƙeta tana faɗin, "Kada ka manta ni ce fa Usaina. Bari ka ji ko ni ina tsoron shu'umancina ba don komai ba sai don sanin makircina. Waɗannan ƴanmata sha biyar da aka kai wa Yarima dole su baƙunci lahira ko ta tsiya ko ta arziƙi. Kuma samun lafiyar Yarima ba shi zai sanyayar da ni ko ya ba shi damar ɗarewa karagar mulki ba, na yi rantsuwa da tsantar makircina ko da Hasana za ta dawo Daular nan Damina ba zai taɓa aminta da ita ba balle Yarima da nake kallo a tafin hannuna nake iya sarrafa linzamin rayuwarsa yadda nake so." Cike da jin daɗi Boka ya ruƙo ƙugun Usaina ya ce, "Ba don ni nake haɗa miki kayan mallaka ba da sai na ce an ya ba maƙale mata kika yi min ba Usaina? Ba na gajiya da ke da duk wani abu na jikinki, a yanzu da za ki ba ni dama da na huce tulun zafin da ɗauko daga cikin kogona. Amma yanzun ma ba zan ce komai don kin wuce tunanin duk wani mai tunani shalelena, ina fatan dai watarana ba za ki harba min ƙarinki ba dom ba zan iya jurar budulcinki ba." Usaina ta ci gaba da hillatar boka mai zamani tuni suka faɗa duniyar masha'arsu cikin kissa ta furta, "Ka bar min komai a hannuna sauran bayanin za ka ji daga baya. Mai zamani idan na yi maka butulci ai sai na ɗaiɗaice wa nake da shi da zan jingina na ji daɗi. Wancen lusarin mijin nawa kowa?" Boka mai zamani ya taɓe baki ya ce, "Haba Usaina ko kin manta na san kuna ƙulla irin wannan alaƙar da wannan sirrantaccen bawan na ki." Sai da gaban Usaina ya faɗi amma da yake ta ita bariki sai ta wayance ta ce, "Hmm idan wannan bawan ne kar ma ya dame ka domin ina nuna masa kulawa ne domin biyan buƙatar kaina ya ci gaba da yi min biyayya yana kawo min saƙƙonni. " Tana gama maganar ta ci gaba da rikita mai zamani da salo kala-kala.