← Book details Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 46

Sashe 43

Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rangaji ta fara yi tamkar bishiyar dalbejiyar da take kaɗawa da iskar damuna, a hankali Kabiru ya ɗan fara ja baya don ko kaɗan hankalinsa bai kwanta da ita ba. Cikin wata irin murya mai jan hankali ta fara magana, "Ka amince min da buƙatata ƙwaya ɗaya ce tal na yi maka alƙawarin yaye maka wannan matsalar da take jikinka." Kabiru da yake jin wani abu yana yawo a zuciyarsa game da ita ya runtse idonsa sannan ya fara magana cikin wata irin kasalalliyar murya, "Ba na buƙatar ganinki cikin wannan yanayin." Tun bai rufe baki ba ta ƙarasa wurinsa ta sa hannu tana ƙoƙarin taɓa shi ta furta, "Laƙani aka bani domin cikar burina a kan Daularmu ta Daulatul jinnul-Turabiy. Idan har ka amince min za ka kusance ni kuma zan warkar da kai, idan ka yi min haka zan mallaki Daularmu da abin da yake cikinta, na zo a sirrance ne ta sanadi ƴar uwata wacce ta yi maka haka..." Tana tsaka da magana ya katse ta da furta, "A'uzubillahi minnasshaiɗanirrajim." Da sauri ta ja da baya tana hakki saboda yadda ta ji wani irin hucin zafi daga jikinsa. A hankali ya tattaro jarumta ya ci gaba da karanta ayoyin kariya da duk wata addu'a da ya san ya taba biyata. Nan take ta ɓace daga gabansa don yadda take ji tamkar zai halakar da rayuwarta, ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa saboda yadda hankalinsa ya sake tashi fiye dana da. A wannan lokacin ya yanke ƙauna don ji ya yi zama a gidan ya fice masa daga rai, gani yake zai iya haƙura da zaman gidan idan ya so duk wata sana'a da ya sani zai fita ya nema don ganin ya ci gaba da nemawa mahaifinsa lafiya. Yana gama nazarin ya miƙe ya ɗauki buhun kayansa, sai da ya leƙa ta window ganin hankulan mutane baya wurinsa ya sa ya yi zaraf ya fice daga ɗakin sannan ya zare sakatar gate ɗin ya fice daga gidan. Gudu-gudu sauri-sauri haka Kabiru ya fara tafiya, kasancewar unguwar shiru babu mutane ya sa bai haɗu da kowa a hanya ba, ta bayan wata doguwar katanga ya raɓa yana tafiya ba tare da ya san inda yake saka ƙafarsa. Yana tsaka da tafiya ya ji ya ci karo da mutum a gabansa, a hankali ya fara ja baya yana ƙoƙarin sake hanya ya ji mutumin da suka yi karo da juna yana faɗin, "Assalamu alaikum." Kabiru da ya fara tsorata a ɗan ja da baya sannan ya amsa masa sallamar, don gabaɗaya a rikice yake. Mutumin da har lokacin Kabiru bai tantance ko shi waye ba ya ci gaba da cewa, "Bawan Allah da wa ka dogara?" Kabiru ya fara sakin jikinsa don ya fahimci ɓoyayyan baƙonsa ne, murya can ƙasa ya ce, "Da Allah na dogara." Mutumin ya ƙara taku biyu zuwa gaban Kabiru ya ce, "Ka dogara da shi a ko'ina kake shi zai isar maka." Kabiru ya jinjina kai yana shirin yin magana, mutumin ya ci gaba da cewa: "Ina ƙaunarka fisabillahi don haka zan baka shawara karka ji tsoron kowa idan ba Allah ba." Kabiru na jin haka ya zaburo da sauri da niyyar kama hannun mutumin yana faɗin, "Don Allah wanene kai da kake yawan zuwa kana gaya min maganganu masu daɗi, da shawara akan al'amuran rayuwata?" Tun bai ƙarasa wurinsa ba mutumin ya ɓace, da sauri Kabiru ya hau waiwaye don neman wurin da zai ƙara ganin ɓullowarsa. Daga can bayansa ya ƙara jin muryarsa yana faɗin, "Karka damu da sanin wanene ni domin mai ƙaunarka na tare da kai a koyaushe, ni masoyinka ne ina mai ƙara tunasar da kai muhimmanci dogaro ga Allah." Yana gama maganar ya sake ɓace wa daga wurin. Jiki a sanyaye Kabiru ya jingina a jikin katangar, ban da kukan kwaɗi da ƙananan ƙwari babu abin da yake tashi a wurin. Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa ta aminta da nasihar da bawan Allahn nan ya yi masa, nasihar da Mahaifinsa yake yi masa ta sake dawo masa, a fili ya fara furta Astagfirullah sannan ya koma ya nufi hanyar gidansu Raihan.

Inno kusan suma suka yi ban da juwa babu abin da suke ji, Huzaifa ya ƙarasa gabansu ya ya zaro musu ido. Suna haɗa ido suka ga ƙwayar idonsa na ci da wuta, kakin yawu ya yi ya tofar a kan tafin hannunsa nan take wuta ta tashi. Goggo tuni ta saki fitsarin da take matsewa ta sunne kai ƙasa cikin tashin hankali, Huzaifa ya buga musu tsawa yana faɗin, "Duk wacce ta sake gangancin shiga lamarin Raihan sai na banka mata wuta ta ƙone ƙurmus, kuma duk wacce ta sake ta furta wata magana a kaina da abin da ya faru sai na hallata shi cikin dare." Huzaifa ya ɗago ya damƙi wuyansu sannan ya ci gaba da cewa, "Kuma duk wacce ta ce za ta bar gidan nan tana fita zan ɗaye fatar jikinta." Inno da idonta yake runtse ta ce, "Babana mun gode, ko a ɗakin nan ka ce mu dauwama har ranar mutuwarmu mun bar sauka ƙasa." Huzaifa bai bi ta kansu ba ya ɗebe su ya watsa a saman fanka, sai ga su Inno a maƙale jikin fanka sai ciccila ƙafafuwa suke yi. Sai da suka jigata sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauko su yana nuna musu zannuwansu dake can gefe ya ce, "Maza ku ɗaura zaninku ku fice daga ɗakin nan." Tun bai rufe baki ba Su Inno suka fara wawurar zannuwansu suna yi suna layi kamar waɗanda suka maku saboda juwar da take ɗibansu. Suna zuwa bakin ƙofa Daddy ya turo ya shigo mommy tana biye da shi Inno ta kusa tafiya luuuu za ta faɗi da sauri Daddy ya ruƙota yana faɗin, "Inno lafiya?" Inno ta fisge jikinta tana faɗin, "Sake ni ka ji Audullahi, jeka kan Raihanu Allah dai ya watsawa Likitanan albarka." Daddy ya yi murmushin jin daɗi don ya ga sauyi a wurin Tsofaffin saɓanin kafin fitarsa da ya tafi suna kwashe wa Likita albarka. Su Inno na fita suka zube a bakin ƙofa suna mayar da numfashi, Goggo ce ta fara rarrafawa tana sauka daga ƙafar bene, Inno ta leƙa tana faɗin: "Kai jama'a yanzu a daren nan za ki rarrafa Zinaru sai makarai sun makeki a hanya." Goggo da ta gama zuwa wuya a zuciye ta juyo ta ce, "Yooo shi wanda kika kuɓuto daga hannunsa Mutum ne? Ki yi ta kanki daga nan ni kam Albasu zan wuce don na tabbata ko ba aljani bane yana cikin ƙungiyar asiri, don wallahi mutum ba zai aikata abin da ya yi ba idan ba haka ba Malam mai allo bai haife ni ba." Nan take cikin Inno ya sake kaɗawa da sauri ta fara rarrafawa ta bi bayan Goggo suka sauka, suka wuce ɗakinsu.

Su Inno na fita Huzaifa ya koma kan Raihan tare da gayyato Jabin Raihan don ta maye masa gurbin Raihan ko ya samu ya sake dulmiyar da su Daddy ga zuwa ƙasar Indiya, saboda matuƙar suka je Indiya hakan zai taimaka masa wurin gano takamaimai abin da yake faruwa da ita. Kafin ƙiftawa ido sai ga Jabin Raihan ta fara motsawa tana sauke ajiyar zuciya, Sai dai babban abin da ya fi ɗaga masa hanakali da ya so ɗaukar gangar jikin Raihan zuwa Tsauninsa abin ya gagara, wannan ya sake tabbatar masa da akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da ciwon Raihan, tashin farko Mugaza ce ta faɗo masa don ya san akan baƙin kishinta tana iya aikata komai don biyan buƙatarta. Daddy ne ya tsinke masa tunanin da yake yi yana faɗin, "My Raihan barka farkowa." Mommy da ke gefe ta ce, "Sannu Raihan." Da ido take bin su da kallo tana gyaɗa musu kai tamkar ƙadangaruwa. Mommy ce ta koma daga ɓangaren Raihan ta tsugunna ta fara karanta ayatulkursiyyu tana tofa mata, da sauri Huzaifa ya zabura ya matsa gefe cikin huci a gaggauce yana faɗin, "Shi kenan yanzu zan wuce Alhaji duk abin da ake ciki za ku ji ni saboda akwai wani patient da yake jirana." Daddy ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin jin daɗi ya ce, "Ba damuwa na gode sosai Dr." Da sauri Huzaifa ya yi gaba har ya je bakin ƙofa Daddy ya ce, "Dr babu wani magani da za a ƙara mata akan na da ka san fa wancen ya ƙare." Huzaifa ya fara sosa kai sannan ya ce, "Babu damuwa zan turo maka text ta waya." Tun bai jira cewar Daddy ba ya fice daga ɗakin.

A hankali Mommy ta ɗago Jabun Raiha tana yi mata sannu, Daddy ya zauna a ɗaya ɓangaren sannan ya riƙo hannunta ya ce, "Allah ya baki lafiya My Raihan." Jabun Raihan ta ɗago tana gyaɗa kai. Mommy ta miƙe tana faɗin, "Mu je na raka ki, ki yi sallah kin ga Magriba ta wuce ga Isha'i ita ma tuni an yi ta." Ras gaban Jabun Raihan ya faɗi don ko kaɗan bata ƙaunar sallah ba abin da ta ƙi jini irin ta ji an ambace ta. Idan aka ce ta yi ma bata san ta inda za ta fara ba tun da ba addininta bane, tana cikin nazari ta riski muryar Daddy yana faɗin, "Haba Zainab yaushe yarinyar nan ta farfaɗo, don Allah ki bari ta huta ta ci abinci ta sha magani tukunna." Mommy ta ɓata fuska tana faɗin, "Daddy babu wani uzuri game da mara lafiya a kan sallah, hatta majiyacin da yake kwance baya iya tashi matuƙar yana cikin hayyacinsa dole a yi masa alwala ko yana daga kwance ya gabatar da sallah..." Daddy ya katse Mommy cikin ɓacin rai yana faɗin, "So kike ki kafirta mu ni da Ƴata kenan? Ce miki na yi ba za ta yi sallah ba? Ki fita idona Zainabu akan katsalandan ɗin nan da kike min yana neman wuce gona da iri." Mommy ta miƙe cikin fushi ta fice daga ɗakin don ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba.
Chapter 43 · 0% Book details