Sashe 4
Bakar Daula Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun ban rufe baki ba ta zabura da matsanancin gudu sannan na rufa wa sawunta baya. A lokacin da na ƙarasa wurinsu tuni na riski zaren carbin rayuwarsu ya kusa tsinkewa, ilahirin jikinsu ƙayoyi ne kwatankwacin yadda suke lulluɓe a jikin bushiyar da na aika musu, ganina ya harzuƙa Barde ya dube ni cikin huci yana cewa, "Uwar dawa me ye haɗina da ke da za ki aikata min haka ina cikin shaƙatawata? Ba don ina ganin mutumcinki ba da tuni na roki Abar bauta ta la'anci ruhinki kamar yadda kullin muke yi wa Baƙar Daula wannan addu'ar..." Tun bai rufe baki ba na ƙarasa wurinsa haɗe da yi masa mahangurɓar da ta kusa gigita lissafin rayuwarsa, a fusace na sake kai masa duka a maƙoshi ina faɗin, "Barde yau akuyancinka ya kai ka wurin da ba za ka sake sanin wata ƴa mace ba sai a rayuwarka ta gaba idan ka na da rabo, ka roƙi Abar bauta da ta yafe maka zunubinka wataƙila ka samu sauyi a rayuwar da za ka dawo nan gaba." Wata sakaran dariya Barde ya saki sannan ya ce, "Wai kina nufin ƴar shilar da na latsa ta gidan ku ce? Ya aka yi haka bayan na san ke kaɗai kika wanzu a cikin gidanku?" Ban ba shi amsa ba sai wani mahaukacin duka da riƙa kai masa ta ko ina, ganin haka ya sa ya damƙi ƙasar gabansa haɗe da ɗaukan cinnaka ya ɗora a kai ya dunƙule su wuri ɗaya sannan ya ɗaga hannunsa sama ban yi aune ba na ji ya watso min ƙasar da ta rikiɗe zuwa jinsin cinnaku. Nan take muka fara sabon artabu kowanne yana son nuna ƙwarewarsa da ƙarfin jarumta da na tsatsuba, ganin hanyar da ya ɓullo da ita ba mai ɓille wa ba ce ya sa ya dube ni cikin hakki yana faɗin, "Kin cika zabuwa mai tsoro don na tabbata da ace ƙarfin damtse za mu gwada babu abin da zai hana ban yi nasara a kan ki ba, ya ke ƙasƙantacciya la'ananniya marar rabo, ya ke gajiyayyiya watsatssiya ƴar taka hayen maharba ba ƴat na koya ba. Wallahi ko giwa ta yi mushe ta fi ƙarfin bakin karnuka, dawa dai dawa ga mazaje ba mata ba Aradu mai tarwatsa ƙananan la'anannu ni Barde kabari nake duk daren daɗewa ina sauraronka." Wata irin kuɗa na ji har tsakiyar kaina yayin da maganganun Barde suka fara amsa-amo a majiyar sautina, daga bayana na fara jiyo sautin haniniyar dawakai tare da ƙarar ƙarafa da miyagun makamai, sannu a hankali na waiga don ko kaɗan na ƙi jinin wannan yanayin da nake riskar rayuwata a ciki. A duk lokacin da wannan yanayin ya riske ni na kan gaza sarrafa gangar jiki da ruhina don na banzatar da abin da nake gani a zahiri ba tare da wanda nake mu'amala da su sun riski abin da nake tozali da shi ba. Kamar wacce guguwa take fisga haka na riƙa jin ana fisgar gangar jikin da ke jingine da ruhina zuwa ga mayaƙan da nake riska suna tunkaro ni gadan-gadan, a koyaushe ina jin baƙincikin yadda nake yaƙar ƴan uwana wato jinsin Maharba da Mafarauta waɗanda su ne nake ganin rundunarsu cikin ƙwayar idona.
Ƙaddara wata abada ce da take sarƙe da gangar jiki da ruhi! Ni tawa ƙaddarar salonta mai tafiyar kura ne, ko a tarihi ban taɓa riskar makamanciyar irin tawa ƙaddarar ba.
Na fito daga cikin jinsin Maharba da Mafaruta, don haka na fi jin daɗin rayuwar cikin dabbobin daji akan mutane. Sai dai kash! Na tsinci ruhina a jikin wani gangar jikin da ba ta ahalina na Maharba ba, na rasa yadda aka yi nake iya rayuwa cikin jinsi biyu. Ko na aikata wani mummunan zunubin a rayuwata ta baya ban sani ba? Idan haka ne na cancanci hukunci irin wannan tun da gangar jikin da nake rayuwa da ita bata ji ba bata gani ba? Ban gama zayyana wa kaina jerun gwanon tambayoyin ba na hangi yadda suka zagaye ni tamkar yadda ale zagaye bakin rijiya, kamar yadda kullin nake ji a wannan karon haka gangar jikina ta riƙa ingiza ruhina ba don na so ba tafi da gudu na riƙa kai sara ina kare kaina. Da alama Barde mamakin abin da nake aikatawa yake don duk wanda yake tare da ni ba ya gani ko fuskantar abin da nake gani a maganaina. Ganin ya samu wannan damar ya sa ya biyo ta bayana a zabga min sara a kafaɗata, wanda fitar jini daga jikina ya haddasa wata irin gigitacciyar tsawa a dajin kamar yadda yake faruwa a duk lokacin da jini ya fita daga jikina. Abin sai ya haɗe min hagu da dama don na rasa wanne daga ciki zan kare duba da rundunar dake kawo min sara ga Barde da yake niyyar yin galaba a kaina. Ban yi aune ba wata irin juya ta fara katantawa da ni tun iya daga tsaye har na gagara mallakar kaina, wani saran na sake riska a gadon bayana wanda silar haka ya sa na durƙushe a wurin ga rundunar da ke gabana na son hallaka ni nan take.
Daular Sarki Damina.
Bayan watsewar tawagar rundunar mayaƙan Sarki Damina, daga harabar wurin kai tsaye keɓaɓɓan gida ya nufa wurin da Yarima yake rayuwarsa a ciki. Gidan an keɓe shi ga Yarima kaɗai saboda gata da kulawar da ake bashi sakamakon mummunar larurar da yake fama da ita, idan kuka zauna kuna ma'amala da shi ba za ka taɓa tsammanin yana da wannan ciwon ba har sai ya motsa za ka tabbatar da haka. Tun daga bakin ƙofar gidan har zuwa ƙofar ɗakin Yarima Maza ne suke gadinsa sakamakon mummunar lalurar da yake tare da ita, wannan dalilin ya sa hatta masu yi masa hidima maza ne don gudun abin da kaje-ya-zo. Saboda kafin a farga da lulararsa a baya mata ne suke yi masa hidima wani abin mamaki duk ranar da aka wayi gari sai an samu gawarwakin ƴanmata waɗanda ya yi musu fyaɗe, waɗansu su galabaita gudun ƙarin wahala Sarki ya sa a ƙonne su ko a binne su da ransu. Ba wannan ne dalilin da ya sa Sarki Damina ya kwashe mata ya sa aka zuba masa maza ba, saboda duk wani abu da zai faranta ran Yarima shi ya ke so bai da mu ba ko da matan yankin za su ƙare. A lokaci wata jarabta ce ta same su matan daular suka daina haihuwar ƴaƴa mata sai maza, wannan ne ya fargar da Sarki Damina ya taka tsibirin Boka mai zamani ya tuntuɓe shi game da haka, nan take ya sanar masa da matuƙar Yarima zai ci gaba da salwantar da rayuwar ƙanana yara mata tabbas za su wayi da ƙarewar ƴaƴa mata a gabaɗaya yankin. Idan kuwa haka ta kasance Sha-kundum za ta yi fushi da su fushi mai tsanani. Wannan dalilin ya sa Sarki yake saka ake zaɓar cikakkun mata da ƴan matan da suka isa ake kaiwa Yarima duk lokacin da larurarsa ta motsa.
Shigar Sarki ɗakin ya tarar da Yarima na ta wani irin kakari tamkar wanda yake gargarar mutuwa, hakan ce take faruwa a duk lokacin da larurar Yarima ta tashi idan ka ga yana wannan halin sai ka rantse ba zai ƙara rayuwa ba. Cike da tausayawa Mahaifinsa ya ƙarasa gabansa yana zura masa ido, duk dakiya irinta Sarki Damina sai da ya zubda masa ƙwallah. A haukace Yarima ya cakumo Mahaifinsa cikin fitar hayyaci da ɗimauta yana yunƙurin haike masa, da sauri Sarki Damina ya fara yunƙurin ƙwatar kansa amma tsananin ƙarfi irin na Yarima ya sa ya kasa, a kan dole dogarawan da ke kewaye da ɗakin suka runƙuro suka taimaka wa Mai martaba. A wahalce Sarki ya ke sauke ajiyar zuciya sannan ya furta, "Ku ɗebo masa ƴan mata biyar don ba na son na rasa yarima, shi kaɗai na mallaka ko matan garin nan za su ƙare sai an nemo masa wasu a faɗin duniyar nan." Tun bai kai ga rufe baki ba wata gihitacciyar tsawa ta ratsa ciki da wajen ma'adanar sautinsu. A razane Yarima ya rungume mahaifinsa don wannan ita ce tsawa karo ta biyar da suka sake riskar irinta. A baya duk ranar da aka yi musu tsawa irin wannan lokaci ɗayamatan Daular suka riskar kansu cikin ɓallewar jinin Al'ada har tsofaffi waɗanda lokacin yin su ya gushe musu, a gaggauce ya fita don isa ga bukkar babban Dodo don ya sanar musu wannan tsawar da wacce irin masifa ta zo musu. A daidai ƙofar keɓantaccan gidan Yarima ya tsaya ya ɗaga kansa yana kallon sararin samaniya, kururuwar dattijuwar ce ta dawo da shi daga duniyar harsashen da yake yi. Waɗansu manyan barada ne riƙe da gashin wata mai tsohon ciki da alama naƙuda take jini na bin ƙafarta, ɗayan yana riƙe da wani matashin saurayi da fuskarsa ke fidda habbon jini daga hancinsa. Tsohuwar na riƙe da su ana jan su tare tana kururuwa da roƙon Dogaran akan kar su aiwatar da abin da Sarki ya umarce su, gyaran murya ya yi lokaci ɗaya Dogarawan suka tsaya cak kamar waɗanda suka haɗiyi taɓare nan take. Bawan da ke tsugunne a gabansa ne ya lura da inkiyar da Sarki ya yi don haka ya furta musu, "Sarki na buƙatar ganin ku a gabansa." A gaggauce suka ƙarasa gabansa bisa lura da yanayinsa suka fahimci ƙarin haske yake nema game da busasshiyar tsohuwar da take riƙe da mutanen da ya bayar da umarni a binne su. Wani narkeken Dogari mai ƙirar samudawa ne ya kwanta a gaban Sarki Damina, sai da ya lashi saman ƙafarsa sau bakwai sannan ya yi sujjada a gabansa yana faɗin.