← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 48

Sashe 7

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk saboda ni ne me yasa na zama kamar tsinuwa a gare su?" Na fada ina jin wani abu ya tsaya a kirjina, "zauna!" Ya nuna min kujerar office din kaina a sunkuye, na hada hannuna biyu na kifa kaina, shiru nayi ina jin kamar zuciyata zata fashe.

"Please sir ka bar ni na tafi!" Na fada a hankali, "promise me ba zaki yi kuka ba idan muka je" gyada kai nayi, ina hadiye kukan da yake son zuwa min.

Wani irin tsinkewa zuciyata tayi jikina ya kama rawa, na koma na zauna ina dafe kirjina.

Wayarshi ce tayi
ara.

Ya fita can na gaji na fito wayata na kalla babu wanda ya kira ni.

Kokarin kiransu nake amma ya kwace wayar naji ya fisge...........
[12/9/2025, 11:35
AM] Maman Walid: 6
Kashewa yayi baki
aya yana mai kallon yadda na kura mishi idanu.

Juyawa nayi na dauki jakata zan fita ya biyo ni har waje da sassarfa yana fa
in.

"Ki nutsu kin ji!" Wani irin b'acin rai ne ya taso min nayi banza da shi, na cigaba da tafiyar har zuwa waje.

"Ki shiga na kai ki!" Juyawa nayi na ga yadda ma'aikatan kamfanin suka zuba mana idanu abin kunya ce nayi mishi wani abu da zai zubar da mutuncinsa, sannan shi Babba ne bai cancanci kyautatawa daga gare ni ba, sai nayi kasa da kai na ce mishi.

"Kasan halin da iyayena suke ciki?" Lumshe idanunshi yayi ya kuma bude akan lokaci yana mai gyada min kai.

"Kasan yadda nake ji?" Gyada min kai yayi, "amma kasan an zalince mu?" Nan ma ya gyad'a min kai, hawaye ne ya zubo min na yi kasa da kaina.

"Ko wani hali Abba yake ciki!" Bude min motar yayi sannan ya shiga gefen drive, muka bar kamfanin.

A lokacin da muka isa asibitin, Mama da Yadiko sai fada suke tayiwa su Aunty Hindatu da Innah da Aunty Munah.

Ji nayi na kasa d'aga kafaffuna na jingina da bango ina kallonsu.

Tsayawa yayi a gefena, ganin yadda na zame a hankali ina mai fashewa da kuka mai mugun cin rai, durkusawa yayi shima yana me kallon yadda nake kuka, ya ma rasa me zai min saboda yadda nake kukan jikina har rawa yake.

"Ke bana son sakarci, ya isa haka." D'ago kai nayi ina kallon Mama da ta juya gare shi tana mishi fada da fulatancin.

"Ka zo ka durkusa a gabanta kana namiji shugaba kuma kana haka waye ya gaya maka cewa ita mace ana bata dukkan abinda take bukata ne?

Ita mace bata bukatar a bata abinda ba zai zama nata baki
aya ba, ka zama namiji kada ka yarda ka yi rauni akan idanunka.

" Mikewa yayi ya barta tayi ta fada kafin ta shiga rarrashina tana gaya min dalilin da yasa aka ki gaya min kenan, a hankali na mike tare da ciro takardun gwanjon gidajen Abba da duk wasu abubuwan da yake da shi, na cigaba da shashekar kuka.

" Zan saka hannu na tura mishi office
insa, ranar talata mai zuwa zai tafi Bauchi." Tunda na ciro takardan ya juya ya bar asibitin.

Yan'uwana baki
aya suka taru.

Sai kuma suka fara ganin laifina da shi Mr Turaki.

"A'a kul na kara jin wani magana, taya Mahaifinku ya ci bashin banki haka shi zaku fara bincike, ba wai kawai ku ji haushin Yarinya da shi Bilal ba, shi ai kawo mishi banki tayi ya saya ita kuma matsayinta ba sakatariyar shi bata da abinda ya wuce ta saka hannu ai idan bata yi haka ba, taba cika adali ba sau nawa tana saka hannu a na wasu.

Auta ki nutsu ki ga abinda ya dace ita Munah da take cewa ki bar aiki idan ya zo ta kanta itama haka zata yi kowa ya godewa Allah da Abban naku yake raye ba wai ku kara shigar da wani tashin hankali kan wanda take ciki ba.

" Inji Yadiko, sai kuma jikin kowa yayi sanyi, amma kuma zuwa yanzu da muke zaune babu abinda Abba yake bukata kamar addu'a.

Abba bashi da kome banki sun kwace kome matukar gida ya fito da sunansa sun amsa.

Abin ya d'aga hankalin kowa.

"Yadiko garin Yaya haka ya faru?

Nasan Abba shi mutum ne da baya cin bashi kuma baya son bashi, me ya faru da ban sani ba?" Tab'e baki tayi tana me fa
in.

"Hafiz!" Tana fa
in haka naji kome ya tsaya min cak.

Na kura mata idanu ina jin wani irin kuka yana zuwa min.

"Hafiz kuma?" Gyada kai tayi tana fa
in.

"Shi kai shine mana waye yake juya kasuwancin Babanku?

Duk Yaran nan sai da ya kore su ya ce basu da kwarewa basu iya sana'a ba, kai karewa babu wnada bai ce ya cuce shi ba, tunda Hafiz ya shigo rayuwarshi hatta Yaransa bai yarda da ku ba, ni nayi mamaki me yasa Hafiz ya
i hakura da ke ashe wannan ta'asar yayi.

Allah mun gode maka!" Daga haka tayi shiru sai kuma tayi kwafa.

Ni kan tun da ta fadi haka na rasa nutsuwata.

Haka nayi ta zama karshe zuwa yamma Ya Ado ya zo ya mai damu gida, a kofar gida na hango motarshi yana tsaye ya harde hannunsa a kirjinsa.

"Auta ga mutumin ki!" Lokacin da motar tayi tsaya na fito tare da fitowa daga cikin gidan na nufe shi, yana ganina ya tako har indA nake.

"Ya mai jikin?" "Da sauki sosai!" Na fada mishi, "Na bawa SAN offer ko zai kawo shi Kumo clinic amma yaki." "Alhamdulillahi mun gode!" Na fada ina kallon kasa.

"Ki taimaka min da takardun hannunki!" Ya fada kamar yana shakkar abinda zai fito bakina, murmushi nayi mishi tare da cewa..

"A'a adalci ne na tsaya a basu hakkinsu, idan na ce zan bi bayan ahalina ban yi adalci ba sannan suma bankin sun yi adalci da suka yi hakuri har zuwa wannan lokacin.

" "Ni zan biya ku
in ku bani takardun please!" Ya fada kallonshi nayi da kyau kafin na ce mishi." Mun gode!

" Na juya zan tafi sai kuma na juyo na ce mishi.

" Ina son na kasance a cikin masu tafiya Bauchi da Gombe, please saboda ina son ganin kome!" Na saka a raina matukar na dawo daga haka zan ajiye aikin na hakura ban tab'a fahimtar yadda mutane suke ji ba sai yau da ta fado kaina.

Yau na ji yadda mutanen da banki take kwace kayansu, Abba ya rasa hatta gida daya da zai zauna, hadiye kukan nayi ina ji kamar zuciyata zata buga.

"Am sorry!" Ya fada a hankali.

Juyawa nayi na kalle shi, sannan na shiga cikin gidan.
-----
Shiga motar yayi ya bar kofar gidan, burinsa ya hango Khamis, har ya isa KUMO FAMILY MANSION, a kofar gidan iyayenshi ya hango shi, cikin wani irin fushi ya nufe shi, cikin fushi bai gama tsayar da motar ba ya fita kamar wanda aka cilla shi, ya rufe Khamis da mugun duka, shi da ya san me ya aikata dariya yake mishi yana nuna shi da yatsa alamar yayi nasara abinda yake bukata.

"Wallahi ko zaka kashe ni, sai na hana soyayyarku tasiri.

Kai ba haka ba baka isa ka yi aure ba matu
ar ina raye!" Duka kamar ya samu jaki.

Dakyar aka kwace shi ya ce mishi.

"Yarinyar nan har abada ka rasata, ai duk abinda kake so matukar zan gani sai na haramta maka ita, ka saka idanun ka gani." Rike hannun Turaki Ubaid yayi yana jan shi har cikin mota bakin ciki ya hana shi magana.

"Ka sani ko zaka mutu ita din ta haramta a gare ka" "Sake na kashe dan iskan Yaron nan!

" Fisgar motar yayi da
arfi kofar gidan Alhaji ELYakub ya nufa, wani irin naushi ya kaiwa glass din motar sai da yayi tsawa, ya fita tare da nufar cikin gidan Alhaji ELYakub, ya zauna shiru sai a lokacin Alhaji Sameerah ya shigo tare da nufar Turaki kamar zata rufe shi da duka, wani irin d'ago kai yayi ya kalleta da jajjayen idanunsa.

"Me ya faru?" Ubaid ya gaya mishi abinda ya faru wanda ya gani da idanunsa.

A lokacin Khamis ya shigo ya danna fuskarshi da tsumar
ara.

Kallonshi Alhaji ELYakub yayi ya ce mishi.

"Khamis me ya faru?" "Kawai don na nunawa sakatariyarsa takardun da suka yi daidai da sunanta na banki sun yi gwanjon kayan Babanta shine ya rufe ni da duka ni me na mishi da zai dake ni?"
A fusace ya sake mikewa Ubaid ya mai da shi, "Please!" Ya fada, yana taping bayansa a hankali alamar yayi hakuri.

Cikin fushi Hajiya Sameerah ta ce.

"Baffa Marin Khamis yayi a gaban jama'a?

Marinsa yayi a gaban kananun ma'aikata, marinsa yayi da akan mace?

Baffa haka bai yi mishi ba sai da ya zo ya kara Dukanshi s gaban jama'a, ka yi wani abu domin wallahi abinda Bilal yake ya fara wuce makadi da rawa."
Kallon Bilal Alhaji ELYakub Kumo yayi rabon da ya ganshi haka tun rasuwar Iyayensa, yadda ya zauna ya sunkuyar da kai tare da dunkule hannunsa yayi murmushi ya ce mishi.

"Lubnah ce ko?" Bai d'ago kai ba amma ya damke hannunsa sosai, alamar Eh.

"Me yasa zaka je gaban Macen da yake so da irin wannan al'amarin?" Murmushi yayi mai sauti sannan ya cigaba da cewa.

"Ita din Matar da yake so ce, ba yau nake jin labarin kana kazamin rayuwa da matan kamfanin ba, na tab'a maka magana?

Sameerah da kike ihu na tab'a yiwa Khamis magana akan abinda yake aikatawa?

Ita yarinyar rabin rayuwarsa ya b'ata yana jiranta, sai ya zuba idanu wani ya lalata mishi damar shi?

A kodayaushe kuka tashi magana kuna mantawa cewa Uban Bilal shine
ana na fari rabin da karin kamfanin dukiyarsa ce gadonsa ce, me ya dace yayi?

Ya kare dukiyarsa da ta al'umma.

Sai kai Khamis ka manta da cewa kana da aure ne?

Kalli matarka da Yaranka biyu amma baka daina tsalle tsalle ba, na maka iyaka da Lubnah ba ruwanka da ita sannan ruwan Bilal ne ya mai da musu kadarorrinsu ruwansa ne ya cigaba da rikewa.
Chapter 7 · 0% Book details