← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 48

Sashe 23

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuba min idanun, ni kaina ina jin abinda ake fada tsaki yayi ya ce mishi." As you wish!" Rigima suke da Kakanshi akan ya zauna a part din iyayensa musamman na mahaifiyarsa shi kuma yace ba zai zauna ba, shine ake ta kai ruwa shi ya nace sai gidansa.

Kallon kwayar idanuna yayi kafin ya ce min.

"Zaki iya zama a wancan jahannamar?" Lumshe idanuna nayi kafin na bude akanshi.

"Duk inda ka kai ni zan zauna." Bakinshi ya kai tare da sumbatar goshina, "Muje su Auntynki sun tafi fa!" Zare idanun nayi ina fa
in, "me yasa suka tafi?" "Ji gulma da kika samu Mijinki, kika manta da wasu aunty a can!" "Ni ba ruwana kai ne ai!" "Amma yarinyar nan kin ga girmana, lallai ma dole na shiga lamarin nan ayi mana Shari'a akan wannan sharrin da kika min." Ya fada yana murmushi, har muka isa inda motar da xata mai mu airport an saka kome na mu, ya bude min na shiga sannan ya zagayo ya zauna a kusa dani.

Rike hannuna yayi yana shafa lallen hannuna.

"Kin yi kyau!

Amma.

Jiya don wulakanci kika yi ta kuka har naji tsoron kada Mama ta ce an fasa tarewar da sai na ce kowa ya tafi mun gode anan zamu cigaba da zama!" Kifa kaina nayi ina dariya, ashe haka yake da surutu, an kira shi ya kai sau biyar karshe kashe wayar yayi, "idan suka gama bidiarsu dole na dauke ki mu tafi honeymoon!" Murmushi nayi wato ina ga ko Radio sai zuba yake min, har muka isa airport
in Uncle Auta yayi ta mishi fada akan bata lokaci da yayi ya ce musu.

"Ni fa bance a shirya wani biki ba, yawwa don da na san da wani bikin nan da na wuce honeymoon da matata ni bai dame ni ba, kowa ya zo ya kwashi gara yayi tafiyarsa ko Lunah!" Ya tambaye ni yana kallon fuskana, kasa motsi nayi Ubaid.

"Amma kai dai daga dan iska sai kai, Allah yasa ka wuce bangon duniya ba honeymoon ba." "Tow ina ruwana, lunah kina jin yunwa na kawo miki wani abu?" Wato shi dai haka Allah yayi shi da bala'in niman magana, har muka shiga jirgin a wurin zama ne fa ni zan zauna da su Aunty Hindatu da Goggo Alti, sai Ummanmu, suka janyo ni na zauna a wurinsu.

"tsayawa yayi ya ce musu, ku bani matata, ni na muku al
awarin zuwa aikin hajji in sha Allah, muna sauka zan tafi da ita idan kafin a fara zan dawo muku da ita."
Kallonshi nayi kamar zan yi kuka na dauke kai, yadda yayi ta tsara su har suka bada hadin kai, na sha mamaki.

Kafin mu isa lagos ya shawo kansu, muna isa airport na lagos wata mota ta zo ta dauke shi da ni.

Ina kallon yan uwana cike mamaki su kansu lamarinsa kara basu mamaki.

Duk jikina ya
auki rawa.

Haaka muka isa wani gidanshi a can victory Island, gidan yayi kyau, ya riko hannuna muka shiga avinda muka fara shi ne sallah, muna idarwa ya fita can sai gashi da abinci, kusan a tare muka ci yana bani ina kauda kai karshe ya janyo ni kamar yarinya karama haka yayi ta dura min, har na ji na koshi.

Kafin ya riko hannuna zuwa parlour ya zaunar da ni akan kujeran parlourn, sannan ya fito ya zo ya zauna ya saka ni a gaba yayi ta kallona.

Kafin ya kwantar da kanshi a cinyata, hannuna ya ja ya daura akan kirjinsa, tun yana min hira har barci yayi gaba da shi.

Zama nayi ina kallonshi.

A hankali nima na daura kaina kan kujeran na cigaba da nazarin rayuwa, kafin barci yayi gaba da ni.

Wasa-wasa sai karfe shida saura muka farka, shi ya fara tashi ya zuba min idanu.

Ji nayi an sumbaci hannuna, a hankali na ji dumin lips dinsa, bude ido nayi na kalle shi na ce mishi.

"Kin tashi?" Gyada mishi kai nayi ya ce min.

"Sorry ko ni na tashe ki?" Murmushi nayi na tashi zuwa dakin da muka cin abinci a cikin na shiga ban daki biyo ni yayi, zuba min idanu yayi da yatsu biyu ya nuna min abinda zai yi.

Juyawa nayi zan fita ya riko hannuna na tsaya, ya gama yayi duk abinda Muslunci ya shara'anta sannan ya fito nima nayi nawa na fito na zo na samu yana jirana, a bayanshi na tsaya ya jamu sallah, bayan mun idar ya dauki Babban rigarshi ya ce min.

"Muje kin ji suna can suna ta Bala'i!" Ya fada yana murmushi, gyara zaman mayafina nayi yana gamawa ya riko hannuna muka fita, har waje ashe dA mutane a gidan a harabar gidan na gansu suna taya shi murna.

Motar ya bude min na shiga, sannan ya zagayo ya shiga yana zama muka bar gidan kafin mu isa har an kira Magariba, muna shiga can cikin gidan.

Ya bude min na fita ya riko hannuna sai da ya ja min mayafina ya rufe min fuska, sannan ya rike ni gam, muka shiga tafiya kasancewar gidan ana ta hidima ga mutane sun taru, hotonmu da muka yi aka saka a wurin da za ayi taron, a hankali muke tafiya saboda tun da muka shigo gidan ake daukarmu hoto, lokacin da muka fito aka mana caa, sai da na ji baki
aya kome ya tsaya min har cikin gidan muka shiga hannun shi rike da nawa, gam lokacin da zamu shiga yan matan family din sun fito, hannunsa ya kai kuguna, ya kara janyo ni jikinshi, kallonshi nayi murmushi yayi min da wani karamin murmushi, haka muka shiga cikin gidan ana rangad'a gud'a, kaina a sunkuye har gaban Kakarshi ta wurin Uba wato Daddah tare da Kakarshi ta wurin Uwa.

Gu
ar da ake yasa ko ina na gidan ya amsa, riko mishi kunne wata babbar baturiya tayi tana mishi fada.

"Aunty Mom barci nake ji.

Idan na ce ku bari mu yi barci ba zaku yarda ba, amma gata Lunah bayan barci akwai wani abu da na.." ture keyarshi tayi tana fa
in.

"Allah ya shirya ka wuce masjid;" ta tura shi waje, daga nan ta riko hannuna ta kara kawo ni gaban Mamarsu.

"Mum ga Lubnah!" "Labubu!" Kaina a kasa ta rike hannuna, ta rasa bakin magana sai kuka, Daddah tsabar dad'i wani abun wuyarta na gwal ta cire ta saka min, "tunda turaki ta kawo ka da sunan tana sonka, nasan bai yi zabin tumin dare ba." Ba ta kara cire warwaronta, ta saka min a hannu.

Yan uwan Mamanshi da suke zaune da kawayensu ba sai gashi anata zuba min kudi fa kyauta kamar ana hidima.

Da yake an tura a kira su Aunty Hindatu, sai gasun nan, haka suka d'aga ni zuwa vangaren da xan zauna aka hada min ruwan wanka Aunty Zakiyah ta hada min kayan kamshi nayi wanka na gyara jikina na fito nayi sallah, sannan na gabatar da sallah da ya wuce min, sannan nayi isha domin za a yi min kwalliya, bayan na gama aka kawo min wani kaya irin na mutanen Ethiopia, haka saka min kayan tare da mayafinsa sannan aka gyara min gashina, ban ji dadin wannan kwlliyar ba.

Ana cikin kwallyar ya shigo yana ganin gashin a bude ya ce bai san wannan zancen ba, hular da aka daura akan gashin ya kara fitar da ni, kasancewar Kakarshi Kirista ce har yanzu don haka kayan akwai Cross amma sai aka cire na kan hular, sannan muka fito bayan an gama shirin, su Aunty Zakiyah sun jima da barin gidan domin tas zai kunyata su.

Tunda aka ce zamu fito aka haska wani fitila da camera wanda suke can baya suna hango mu a majigi, sai suka huta da mikewa, flower girls dinmu Yaran Jasminah ne da Yaran mazan Uncle Auta, suka bude mana hanya muka cigaba da tafiya, Nusaiba yar Aunty Nuratu Kafaya ita ce da wasu yan Gym dinmu suka fito a bridesmaids, suka take mana baya a mazan da suka rufa mishi har da Ubaid.

Haka muka isa wurin zaman muka zauna.

Gashi an saka wakarsu ta can wanda suke yi da kafada, wasu daga cikin dang
insu na can, sai wurin yayi kyau.

Haka akayi ta gabatarwa har aka gama kafin aka kira Ubaid ya bada labarin abokinsa, a hankali yake bada labari har ya gama sannan aka kira Nusaiba ta bada labarina, tun daga bude taron da Addu'a zuwa yadda take ba da labarina, kallon Aunty Zakiyah da ta d'aga min hannu nayi murmushi, bayan ta gama aka saka waka musamman namu na yan arewa, kafin aka saka wakarsu na Fulani.

Kallona yake yana murmushi, bayan an fito da ni da shi.

Aka yi ta zuba mana ku
i, daga shi har ni ba gwanayen rawa ba, haka muka tsaya musamman inda ya
an saka hannunshi a kuguna da kuma rike hannunsa ina kallonshi.

Wani abun da ya kara tashin hankalin a wurin masu adawa da aurenmu, musamman Badr ban ganta ba, na samu kyautar abin arzikin da abin duniya baa tashi ba sai karfe daya saura sannan aka raka su Aunty Hindatu zuwa gidan Ya Ado ango da yan uwansa, ni kuma aka wuce da ni bangaren fa aka gyara shi tas, aunty Innah har da cewa.

"Yanzu ba mamaki fitar nan har kin bashi hadin kai ko?

Tow wallahi ba wani
oukin da zai yi akanki." Tura baki nayi ina fa
in.

"Wallahi ba abinda muka yi barci kawai yayi fa!" Na fada ina jin haushi ko me na bashi ai hakkinsa ne, tun da muka dawo take fada, kamar nayi wani zunubi, bayan sun tafi Aunty Mom ta bani wasu abubuwan har da tarkacen mata irin na turawa, muna nan zaune da ita har suka dawo da yake har da Matar Ubaid da Uncle Auta, ana ta hira sama-sama, na lura matar Ubaid tana jin kanta ita wata shegiya ce, nima na nuna mata ni iyaka ce, suna shigowa kai tsaye wurina ya nufo ya cire min mayafin yana fa
in..
Chapter 23 · 0% Book details