← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 48

Sashe 3

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana da kirki amma bana jin Matarshi zata zo ya zauna da wata mace bayan ita?" Da mamaki take kallona.

" Yana da mata dama?" Na kirkiro haka ne don kada su saka burinsu akanshi.

Amma nasan bai da mata kuma bai ta
a ajiye ta ba.

Haka muka gama hiran take bani labarin abinda ya faru da kashe ku
in.

" Kuma na ga kamar kina farin ciki da ganinsa fa." Ban ce mata kome ba har zuwa yamma sai gashi tare da Mama, yadda suke hira da Mama sai nayi ta mamaki, gayen nan ya iya shiga jikin mutum, Sallamar Ya Sani da Taj muka amsa na rike baki ina fa
in.

"Kai ne a Bauchi?" " Eh kai Hajiyata gani nan nazo cin masar Bauchi koda yake mutumina ya bani na ci.

" Sai nayi ta kallon Taj ina murmushi.

" Lallai ka ji dadin ka, shine kazo asibiti ganina?" " Oga na zo
auka!

" Ya fada yana nuna min shi da idanu, sai lokacin na lura da ha
e rai, tare da shiru kuma da hira yake yiwa Mama.

Itama ganin yadda yayi shirun sai ta zuba min idanu.

Sai na diririce baki
aya na rasa me yake min dad'i.

Shi kanshi bai ji dadin yadda nake sake da Taj ba.

Mikewa yayi na ji yana yiwa Mama magana da fulatanci, am surprised da naji Mama itama ta amsa mishi suka fita ko kallona be yi ba ya saka kai ya fita abinsa.

Ban san lokacin da na leka na ga da gaske tafiyar yayi sai kuma wata zuciya ta ce min sai me?

Da wannan kwarin gwiwa na cigaba da jiran fadar Mama ai kuwa da ta dawo na sha fada, shigowa Aunty Innah tayi tana fa
in..

"Ke a ina kika samo mutumin kirki haka?

Dubu dari biyu ya bani na gyara motar fa." Yadda tayi ta zuzuta shi Mama tana wani blush, irin ya mata abinda ya dace.

Washi gari aka sallame ni cike da farin ciki kusan wani ikon Allah baki
aya sai a bar min katinsa.

Haka muka dawo gida na samu Baban Jama'are ya zo shida Goggo Uwani, nan san me suke tattaunawa a kai ba, amma na sha jinin jikina, sai dai ba ayi nisa ba, Mama ta musu tass haka suka kwana washi gari suka koma Jamaare, nima washi gari muka bar Bauchi Mama ta ce gara mu wuce kawai domin zamanmu a Bauchi kara fitina yake amma bamu tafi ba, yankari muka wuce da su Ya Umar da Tahir, Aunty Hindatu da Aunty Innah, suma su Ya Umar kowa da Matarshi, baki
aya muka wuce har da Sani, mota guda muka dauka.

Hankalina yana kan wayata har muka isa dinduma anan muka hadu da wasu motoci, muka shiga cikin garin yankari.

Tunda muka isa gate din Yankari ja hango kamar shi ne, ya fito a motar yana.

"Kambu kamar Mr Turaki?" "Eh shine kai!" Inji Aunty Innah tana dariya, "ai shi yayi invite dinmu nan!" "Shi din?" "Eh kai!" Shiru nayi ina kallon yadda suka ci amanata da shi, har ciki muka shiga cikin, sai da muka fito ja gyara zaman mayafina, na fito ina kallon inda yake waya alamar magana ce mai muhimmanci, yadda iya daura hannu daya a kirji, daya yana waya kunnen.

Janye idanuna nayi da sauri saboda yadda ya kama Ni ina kallonshi.

Na shiga cikin mutane.

Haka kawai ya kama ni ina kallonshi.

Haka muka shiga cikin kafin ya iso suka bashi hannu aka gaisa, Yaran Yayuna suka gaishe shi ya amsa yana fadar sunansu kamar an bashi irin sunan kowa.

Kallonshi nayi a fakaice.

Da wutsiyar idanu ya kalle ni, ai kuwa muka kama juna, dauke kai yayi ya shafa kanshi wanda yake dan dauke da ratsin fari alamar furfura.

"Wannan mutumin ya tsufa amma sai wani abu yake kamar yaro!" "Waye?" Aunty Zakiyah ta tambaye ni, kallonta nayi ina fa
in.

"Ban ce kome ba!" "Munafuka cikin
ananan kayan ne ya tsufa Allah ki sake ranki bature ni ba ruwansa da wani harkar al'ada kada a kashe mishi rayuwa.

Irinsu zasu jima suna ririta mace musamman." Tura mata baki nayi ina fa
in.

"Ni ban tambaye ki ba!" Nayi gaba abina, domin na lura..........
[12/8/2025, 11:21
AM] Maman Walid: 3
Ta saka min idanu, tunda mutumin nan ya fara zuwa gidan Ya Ado na lura da Aunty Zakiyah Yar sa'ido ta koma, tura baki nayi na naki kulata haka muka shiga cikin wurin shakatawar, masu karban baki suka shiga mana jagora, zuwa dakunan da zamu zauna.

Wani karamin jaka aka kawo min, "inji Mr Turaki ya ce a kawo miki." Amsa nayi ina kallon jakar na shiga cikin dakin, ni daya ce kamar mayya.

"Tow me zanyi da jakan nan?" Na yi magana ni
aya, wayata ce tayi
ara ma
auka don number bakuwa ce.

"Lubabatu ce?" "Eh waye?" "Hmmm Hajiyar Hafiz ce, na kira na gaishe ki ne na kuma gaya miki Hafiz tunda ya ganki bai da lafiya!" "Ayya Allah ya bashi lafiya," na kashe wayar tare da kallon kofar dakin da na ji ana tab'awa, shine ya bude a hankali ya
an tsaya tsakanin kofar dakin da kuma ciki, wayar ta kara yin kara kamar ba zan daukar ba, na saka raina a inuwa na dauka.

"Luluna ki saurare ni?

Luluna ki yafe min." "Allah ya yafe mana baki
aya amma don Allah ka kyale ni saboda kai ba zan sauya layi ko nayi ta b'ata lokacina ina blocking dinka Please ka daina kirana." "Luluna ki dawo gare ni, zan daina kina dawowa ne kawai zai saka na daina bibiyarki?" "Idan naki fa?" Na tambaye shi cikin masifa da tsiwa na ce mishi..

"idan naki fa?

Kashe ni zaka ko hana ni aure zaka yi kamar yadda kake fada?

Tow ka sani kafin kayi wani ya rigaka." Na kashe wayar baki daya koda na d'ago kai babu shi babu dalilinsa, fitowa nayi na samu baya nan wurin, haka na koma na zauna.

Wurin karfe Bakwai na dare, Aunty Hindatu da Innah suka shigo sai matan Yayuna suka bude wannan jakar da aka turo min suka ciro wata doguwar riga mai kyau suka bani na saka.

"Me yake faruwa?" "Muje zaku gani?" Inji Aunty Zakiyah, ni sai abin ya dame ni zan kara magana ta saka min hannu a bakina.

"Shiiiiii!" Haka nayi shiru tare da bin duk abinda suke aikatawa, har aka gama muka fito lokacin anyi sallah isha domin sai da muka yi sallah, kallon kaina nayi tayi ina mamakin yadda nayi kyau ba wani kwalliya nayi ba amma sai nayi na dan yi kyau, fitowa muka yi zuwa wani babban hall, abun dariya wai birthday aka shirya min, kasa magana nayi ina kallon abin kamar irin how dai ayi maka abinda baka zata ba, in fact sai abin ya zo min wani iri ban tab'a kawowa ni za ayi min wannan abin ba.

Idanuna ya cika da kwalla.

A hankali suka fara waka idanuna cike da mamaki.

Har suka gama.

Wukar suka bani na fara yankawa.

Kallon wurin baki daya nayi ga shi ne bako a cikinmu, a hankali na mika mishi cake, murmushi yayi ya saka hannu ya amsa tare da cewa.

"Happy birthday Lunah!" Hawaye ne suka zubo min, anya wutsiya rakumi bata yi nesa da kasa ba?

Haka na bi Yayuna na basu, wani hoton majigi ya bayyana a hall, a ina aka samo hotona.

A hankali na taka zuwa wurin da yake zaune na dan tsaya a jikin bangon da yake gefe shi.

Shima tashi yayi ya jingina da bangon.

Shiru ya ratsa tsakaninmu, kusan rabin hankalinmu yana kan majigin, yayinda yake ta fama da wayarshi.

Satar kallonshi nayi kafin na ce mishi.

"Baka da lokacin kowa sai na wayarka." Murmushi yayi ya ce min.

"Tunda kika zo kin duba aikin office dinki?" Kallonshi nayi kamar bashi yayi Maganar ba hankalinsa yana kan wayar.

"Ina da meeting ki zo muje?" A dan razane na ja da baya.

"Ba zan tab'a wuce iyakata ba, yayunki xan tambaya." Dan ajiyar zuciya na sauke ya tambayi Ya Umar suka ce bi shi, tabbas sune mutanen da na gani yadda muke tattaunawa tare da abinda ya kawo su, har muka gama yana fama wayarshi, wurin karfe goma ya rako ni, sai xa muka fara tafiya ina gefenshi na ji ya riko hannuna tare da fisgo ni, kwace hannuna nayi cike da mamaki, "hmm!" "Hmm what?

Ka dauka ni don bani da aure nima yar iska ce kamar yadda ake yiwa sauran zawarawa kallon, kada ka kara kai hannunka jikina, I'm not whore kada ka ga ina aiki a kamfanin ka, ka zata ni yar iska ce, ka bani kunya kada na
ara ganin fuskarka." Wai ance rashin sani yafi dare duhu, ashe shi Abu ya gani a sama ta inda nake, ban gama masifar ba na yi abu ya fisge dan kwalina kasancewar ko ina haske ne amma ban san meye a saman ba, fisgo dan kwalin yayi birin ya fado, nima tsalle nayi tare da komawa bayanshi, abinda ya faru kenan har inda Ya Umar yake ya kawo ni, kallonshi nayi ta yi amma bai kalli inda nake ba.
---
Washi gari.

Lokacin da na fito wurin karfe daya, na sami yan uwana baki
aya suka ta hiran abinda ya musu na alkhairi.

Basu gaya min ya tafi ba sai da na zauna ina karyawa.

"Ke kan tun jiya kuka yi sallama ko?" "Waye kenan?" Na tambaye Aunty Hindatu da take cin meatpie, "Mr Turaki!" Kwarewa nayi, abinda ya faru a hanyar dawowa dakin ya fado min, shiru nayi bayan na gama tarin, tabbas nayi rashin hankali.

Da nasan cewa jiya biri ne a saman bishiyar da nake tafiya a wurin da ban gaya mishi magana, har bayan la'asar da muka gama yawo a yankari muka dauka hanyar Jos domin mun tattara kome na mu, haka muka samu rakiyar Yayuna har Jos da dare muka isa gidan Aunty Raliya mu kwana saboda gidanta Babba ne, tunda na shiga ban dAki nake kallon wayar hannuna, can na yi shahadar kuda na kira shi.

Ringing daya yayi ya dauka.
Chapter 3 · 0% Book details