← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 48

Sashe 14

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsoro da kunyar Kakanshi ya hana ni komawa asibitin har sai da ya cika kwana biyar, a lokacin Ya Ado yayi tafiya, lokacin da na je ni da Yaran Ya Ado suka raka ni.

Ubaid na samu sai wata yar uwar Babanshi, shi ya tsayar da ni tare da nuna min shi ana wanke mishi ciwon da yake kafad'arshi, mutumin nan akwai taurin rai.

Domin ko gizau kai yadda yake latsa laptop zaka tabbatar da cewa shi fa bai san ana yi ba, a hankali na kai hannuna kan kofar, d'ago kai yayi idanunmu ya hadu da juna.

Wani ha
e rai yayi kamar bai ta
a dariya ba, kasa da kaina nayi ina jin wani irin kunya.

Har matar ta gama dress din ta duba kanshi sannan ta fito daga dakin.

Bude kofar Ubaid ya min muka shiga har da
an abin tab'awa nayi.

Yaran suka isa gare shi ni ina tsaye rike da basket din na kasa motsi haka ya kula yaran har da ciro musu apple da banana, amma ni ko inda nake bai kalla ba, kasa motsi nayi ina kallon kasa.

Wani irin tsoro yana kama ni, Yaran yayi ta tambayarsu.

Ina tsaye a wurin aka. turo kofar dakin, Yan matan family
insu ne, sai da suka kalle ni kafin suka nufe shi.

"Hamma ya jikinka?" Murmushi yayi ya ce musu.

"Da sauki sosai?" Badr da ta koma gefenshi kamar zata shige mishi, tayi ya iyayi har da kukanta, ni dai kaina a sunkuye sai wani abin isgilanci suke suna dariya, ina rike da basket din.

"Badr hada min ruwan zafi." Da sauri na kalle shi, bai kalli inda nake na, na sunkuyar da kai, haka ta shiga hada mishi sannan ta fito cikin kulawa take gaya mishi ta ha
a,kwalla da haushi ya cika ni, amma wannan ba matsala ba ce da xan nuna akan idanunsu.

"Ku bani wuri na shiga wanka." Kafin su fita na riga su fita, koda Yaran suka fito na mikawa Ubaid basket na ce mishi.

"Allah ya bashi lafiya zamu tafi!" "Ki tsaya ya fito mana!" Murmushi nayi na girgiza miishi kai na ce.

"Ai mun sallama da shi!" Na kama hannun Yaran ina jin wata cikin yan matan tana jefa min magana amma ban kula da batunsu ba, muka bar asibitin.

Gobe ma zan dawo jibi ma xan dawo ga ta ma zan dawo sai ya gaya min har sai ya gaya min baya bu
atar ganina a rayuwarsa zan tafi zan koma inda na fito.

Haka da na saka a raina, har muka isa gida.
---
Bayan tafiyarsu ya fito idanunsa yana kan kofa, amma kasancewar ya iya takunsa ko irin a fuska ya nuna yana son ganinta bai yi ba, ya cigaba da abinda yake ta yi.

Ganin yadda ya masu a gabanta basu san yayi amfani da su bane don ya cusa mata b'acin rai kuma yayi nasara, shigo da basket din, Ubaid yayi yana fa
in.

"Ga abinda aka kawo maka." Kallonshi yayi da harshen larabci ya ce mishi.

"Ina take?" "Ba kunyi sallama ba?" Murmushi yayi yana daga cikin abinda yake karawa zuciyarshi kaunarta tasan kanta, "zuba min abincin?!" Haka ya shiga zuba mishi abincin, masa ce da miyar koda.

A hankali yake ciki da dumi kuwa.

"Ka mata bakin hali ko?" Ubaid ya tambaye shi, banza yayi mishi ya cigaba da cin abincin.

Yasan idan Ubaid ya san me tayi mishi da kanshi zai ce ya hakura da ita.

Amma ya kalli kwanon yadda yake cikin abincin.

"Hamma ka hana bazawarar ce zuwa mana?

Babu amfanin zuwanta wurin ka." "Wurinki take zuwa?

Idan da ke ce kika samu irin darajar da take da shi ai da kin hauka ce." Inji Ubaid, " kallonsu yayi da kyau ya ce mata.

"Na san dukkanku nan babu wacce bata ta
a kwanan a waje ba?" Tsuru-tsuru suka yi suna kallonshi.

" Ita kuwa saboda tarbiyyar da aka mata, ko hannunta wani namijin bai rike ba sai wancan Tsinannen yaron da ya aure ta.

Ina sonta ne don ita din ta cancanci zama uwar Yarana." Murmushi yayi ya ce musu.

" Kuna son aure na ne don abinda nake da shi ita kuma tana gudu na ne saboda abinda nake da shi, kada wata rana na kalle ta nace ta aure ni saboda abin duniya da nake da shi ne........
[12/12/2025, 7:52
PM] Maman Walid: 12
" Ku kanku baku da qualified na matan da nake son aura, baku cancanci na aure ku ba.

Ita din rabi da kwatan rayuwata ce, duk abinda xan yi mata ina yi ne don ta san ko babu ita xan rayu kuma zan iya rayuwa da wata mace bayan ita, ina son ta san da cewa akwai mata dayawa da suke bina ina gudunsu ba irinku da basu da aikin yi ba.

Sai harin abinda ba nasu, kada na kara jin wani ya zage ta ban hana ku zuwa amma wata tayi mata kallon banza zata gamu da ni." Daga haka ya cigaba da abinda yake yi.

Domin yayi imani a ransa zata dawo.
***
Tunda na isa gida na ji a raina kamar kada na kara dawowa amma kuma sai na ji ina son na kara komawa domin na ji yadda yake ji, haka na kwana susuku.

Washi gari kuwa bayan Aunty Zakiyah ta tafi aiki kasancewar Yara suna hutu na kara shiryawa muka tafi asibitin da safe.

Lokacin da naje na samu har su Uncle Auta, gaishe su nayi suka ce na shiga ana mishi dress juyowa nayi zan fita ya cewa Yaran.

" Adil!

" Kallonshi yayi a tsorace ganin yadda ake wanke mishi gefen cikinsa yana murmushi.

Juyowa nayi na kalle shi, shima ni ya kalla ganin yadda na zare idanu ana wanke ciwon, wani irin kallon banza ya min ya mikawa Adil hannu.

Ya zo ya rike shi ban san me suke fada ba, amma yaron ya daura kanshi a kafad'arshi, shi kuma yana shafa bayan Adil kama sauran yaran nayi muka fita wani irin tsoro yana kama ni.

Zama nayi kamar zan yi kuka, na ce.

"Haka ake mishi wankin ashe jiya ban ga kome ba?" Na fada ina shashekar kuka, dariya Uncle Auta yayi yana fa
in.

"Kin ga shi da yake haka yake bai san wani emotional ba, shi yasa kika ga idanunsa babu tsoro ko karaya.

Kece rauninsa idan da zaki shiga damuwa sai yafi ki shiga damuwa." Murmushi yayi yana kallon yadda nake rike basket din Abincin, hawaye ya shiga zuba min kamar zan cire ciwon a jikinsa na dawo da shi.

A hankali na tashi lokacin yana bawa Adil ayaba yana ci tare da nuna mishi dantsen shi.

Ina shiga Adil ya fito daga dakin.

Kallonshi nayi a hankali na taka zuwa gabanshi jikina a mace, wayarshi ya dauka yana dannawa.

Yadda na zauna na ce mishi.

"Am sorry!" Mutumin banza yayi kamar baya dakin, nayi ta bashi hakuri, ina kuka amma bai ce min ci kanki bai ce min ba, tashi yayi ya bar ni a dakin na sha kukana sannan na mike tare da barin dakin, kafin ya fito mun bar asibitin.

Haka nayi ta jera zuwa asibitin amma babu abinda yake hada mu, baya ce min uffan.

Ranar da na je na karshe aka ce min an sallame shi, sannan aka bani basket din Abincin da nake kaiwa.

A kasar basket fa
in takarda ce da dan girma na bude kudi ne dubu dari.

Sai yar shot not.
*Kada ki nime ni, ki koma wurin Ex dinki!

Na yanke alakata da ke har abada* sai na ji abin kamar a mafarki gashi bai ambaci sunan Hafiz balle na ce kishi ne, tow bai ambata ba, sai nayi ji kamar zuciyata ce ta bar gangan jikina, haka na durkusa a wurin, wani azazzaben tsoro ya shige ni mai cike da tashin hankali, sai naji kamar bani da amfani akan kome.

Na ji kome na duniyar ya tsaya min cak, tausayin kaina da rayuwata.

Haka na kwashe minti goma har aka fara min magana na tashi da kyar na dauki jakata da basket din da wanda na kawo abincin, na tsare abin hawa ina kuka yau.

A can nesa da inda take durkushe Ubaid ya ce mishi.

"Wallahi ta tuba kada ka mata haka, hukuncin yayi zafi ka saurare ta." Sunglasses dinsa ya saka ya ce mishi.

"Matsalata ce ba taka ba, muje gida." "Gaskiya you too heartless, haba ka ga yadda take tafiya har." "Uncle Auta matata ce kake fasala tafiyarta wallahi zamu samu matsala da kai!" "Allah ya baka lafiya!" Daga haka suka bar asibitin.

Akwai karamin hauka da wanda ya dara soyayya yake, wnada na fahimci cewa ina cikin wa
anda suka haukace ko suka zauce a kan sha'anin zuciya.

Baki
aya na ji kome ya tsaya min cak.

Tunda na dawo gida na gane bani da hankali, sai na ga ashe da ban yi kome ba, domin a daddafe na yi kwana biyu me kyau na uku kuwa sako nayi ta tura mishi both what'sp da Text message, amma babu reply sannan uwa Uba ko zan kare ranar ina kiranshi wayarshi baya shiga, kaina ya kunce bana son fita koda waje, ina nan zaune na rasa meke min dad'i.

Haka na kira Mama ina kuka na kasa magana.

" Ba kin ce gidan Hafiz zaki koma ba?

Tow wata sati na ce Yayanki ya dawo dake gida sai ki ji dadinki.

Tunda gidansa kika zab'a amma ki sani ko namarki Hafiz yake yanka yana gasawa wallahi ba abinda ya dame wawuyar banza shi kuma Turaki Allah ya bashi budurwa ba ma ke da wani ya gama da ke ba, ba wani baki da lafiya.

Lafiyarki lau iskancin ne kawai da renin hankali mara kunya wacce bata da godiyar Allah." Tayi ya fada kafin ta ce min.

"Ki sani tunda Hafiz kika zab'a bani ba ke, ki je kada ki sake ki shiga inda nake na gaya miki."
Zan iya cewa ko abinda nayi Mama da Yayuna basu dauki zafi kamar yadda suka dauka don sai na ji ina tsoron kiran kowa bayan Ya Ado.

Shi
aya yake saurare na.

Bayan ya dawo ya sake min fada da nasiha.
Chapter 14 · 0% Book details