← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 48

Sashe 18

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washi gari
Da safe aka yi kosai sadaka aka raba da kunu, da rana aka yi yankar katon rago.

Haka aka raba makota.

Ashe Mama ta saka ayi min saukar Alqur'ani ne, kwana biyu a tsakani ta ce maza na shirya zamu tayi abuja, haka na shirya sai abuja.

A ranar da muka isa aka gama mana kome muka tayi Umara da ita, jajjirtacciyar uwa irin Mama dakyar za a samu irinta, domin kuwa tana tsaye a kaina kamar hasken rana.

Sati biyu da nayi muna addu'a da rokon Allah sai ma ji baki
aya na sallamawa Ubangiji kome nawa yayi duk abinda zai yi a kaina.

Ranar daren Juma'a, ina dawafi, sai naji kamar Mr Turaki yana filin ka'aba ko da na juya ban ganshi ba, amma jikima ya bani yana nan, amma ba yadda xan ina cewa ga inda yake.

Haka na cigaba da
awafina, sau biyu sai na zo inda nake jin yana nan zan ji alamar yana kallona amma da zaran na juya zan ga babu shi, haka nayi karo na biyu muka yi ido hu
u da shi, gefenshi Jasminah ce da Yaranta, Yaran suka tawo da gudu suka rungume ni, sai ya saje da turawan da suke gefenshi.

"Ilham Nadiya!" Na riko hannunsu muka zauna, "Aunty Lunah!" Buge mata baki yayi yana hararanta.

"Lafiya lau Maman Nadiya!" "Ina wuni Sir!" Wani irin kallo ya min irin na rud'anin nan, ina hango yadda yake maimaita kalmar Sir a lips dinsa, ya kara maimaita kalmar yafi sau uku.

"Baby Il nayi kama da cow?" Ya tambaye ta, da yake Yarinyar bata san me yake nufi ba, ta ce mishi.

"Uncle wani irin cow milk cows?" Wani irin kallon ya watsa min ya cigaba da biye mata suna maganarsu, "Yaushe kuka zo?" Na tambayi Jasminah.

"Yau kwana biyu kenan!" Shiru nayi tsakaninmu kwana uku kenan, na saci kallonshi waya yake yana raba idanunsa a ko ina, can muka yi ido hu
u da shi, so nake na kare mishi kallo.

Rigar jikinshi jallabiya ce amma ta wani kwanta a saman kirjinshi, wanda ya fitar da six figures dinsa, a inda nake ina iya hango bakar singlet din da ya saka.

A hankali nake binsa da kallo har idanuna ya sauka kan zoben da Mama ta bashi, yayi mishi kyau.

Koda na d'ago kai na zuba mishi idanun, mikewa yayi zai bar wurin na cewa Jasminah.

"Bari na shiga Masallaci." Sallah zan yi na kara godewa Allah da ya ha
a ni da irinsa.

A lokacin da ban zata ko na kawo zan samu irinsa ba.

Amma me yasa yanzu nake jin tsoronshi?

Wayyo Allah duk wancan maganar da na gaya mishi ne, haka na tafi ta ce min.

"Muma masauki zamu koma." Sallah na je nayi sannan na fito zuwa gida a hanyar komawa ta masauki ni daya ce mace dayawansu maza ne sai daidaiku masu mata, kuma fararen fata ne.

Ina tafiya naji wani ya bangaje ni, ya wuce da Matarshi. abin ya bani mamaki, tsayawa nayi ina kallonsu, tsayawar da suka yi na ga sun juyo tare da nufo ni, kallonsu nayi Mijin ya ce min.

"Don Allah ki yi hakuri ban lura ba ne, Mijinki ya ce ba zai yarda ba." A hankali na kalli inda yake ya wani ha
e rai.

"Kiyi hakuri mun bar Yaro ne da Mahaifiyata kuma nasan ya tashi yana kuka a masauki " murmushi nayi nace mishi.

"Ba kome ku je." Juyawa suka yi zuwa wurinsa suka bashi hakuri sannan suka tafi suna juyowa suna kallonmu, sai da na iso wurin da yake ya cigaba da tafiya kamar yadda wadancan ma'auratan suke tafiya, har zuwa masaukinmu.

Mama na hango suna hira da Yaran Jasminah.

Wurinsu na nufa na zauna a hankali ina fa
in.

"Wash Mamana yunwa nake ji!" Shima zama yayi ya gaida Mama yana mai latsa wayar cikin kulawa ta ce mishi.

"Bilal ka dawo?" Kallon yadda matar nan ta juya min baya zuwan wannan gardin nake.

"Eh Mamana!" Sake baki nayi ina kallonsu.

Cike da mamaki, yaushe wadanda bayin Allah suka koma baka?!

"Bilal me zasu kawo maka!" "Mama yanzu naci abinci, sai dai ko Lunah." Shi bai jin kunyar kiran sunan nan ne agaban mutane.

"Uncle lunar kuma?" Shiru yayi bai ce mata kome ba, can ta ce mishi.

"Uncle lunar ana samun shi ne a watan biyu duk bayan shekara tara."
"Yes My Lady haka nake nufi but ita I found her after many years na same ta?" "Uncle ai lunar a sama ita kuwa Uncle a kasa take." "It's miracle" ya fada yana barin wurin sai lokacin Mama ta ce min.

"Kika ce kina jin yunwa ko?" Me Jasminah zata yi ban da dariya, kwalla ne ya cika min idanu na ce mata.

"Mama ni me nayi kike min rikon Uwar wata shi kuma har da tambayar shi me xai ci ni kuma na fadi na mutu ko." "Yaushe na ce haka?" Ta fada tana murmushi.

Hawaye ne ya zubo min na tashi na bar su a wurin don na ji haushi, sai da na tsaya na amshi abincin sannan na koma dakinmu, a hanya muka hadu da shi zai koma kasa, tun daga nesa nake watsa mishi harara domin ya janyo na rasa kulawa daga Mama.

Murmushi yayi ya wuce ni.

"Kome sai ka raba ni da shi ne?

Itama da take tausayina yanzu ta daina kula ni haka xan rayu duk mazan da na zauna a kasan su sai sun raba ni da dangina suke jin dad'i."
Murmushi yayi ya cigaba da tafiya, "ka kyale min Uwata don Allah!" Murmushi yayi bai kara min magana ba yayi tafiyarsa, karshe da na shiga dakin abincin ajiye a nayi ban ci ba, na kwanta da takaicin kowa.

Lokacin da ya isa ya samu tana hira da Jasminah.

" Mama me yasa baki saka an kawo mata abincin ba?

Idan ta kwana da yunwa fa?" Ya fada cikin yanayin rashin jin dadi.

Baya kaunar abinda zai saka tayi kuka har kuka har cikin ranshi yake jin haka.

"Lubnah ba yarinyar ba ce ka kyaleta
" "A'a Mama Lunah yarinya ce a gaban kowa ma yarinya ce.

Idan bata ci abinci ba ciwo zai kamata.

Mama anyi min laifi abar matar turaki da yunwa?" Tashi yayi ya koma kofar dakinsu ya buga kofar yayi har lokacin ba a bude ba.

Tura kofar yayi ya ganta kwance.

" Ke tashi ki abinci bana son bakin ciki, ki bawa jikinki azaba kafin aurena." D'ago kai nayi ina kallonshi murguda mishi baki nayi na juya mishi baya.

Ja iska ya fesar.

"Zaki gaya min ranar da na kama ki, yadda kika murguda min baki isa kin gaya min wanda kike yiwa rashin kunya." Share shi nayi na cigaba da kwanciyata.

"Tashi ki ci abinci wallahi kika sake na shigo da kaina, abinda zai faru ba zai mana dad'i ba." Jin yadda ya rantse yasa na tashi da sauri na fara niman abinci na fara bude madara na sha sannan na fara cin ganyen da wani tsokar bana, ina ci ina kallon inda yake, gani nake kamar zai shigo da gudu ya turmushe ni cikin rawan murya na ce mishi.

"Ka tafi kada a ganka a dauka wani abu ne?" Tab'e baki ya ce min.

"Allah yasa ni ne mutum na farko da na fara wanke miki period dinki, babu abinda wani dan banza zai nuna min tunda ni a can baya mai kwaila nace ina so ba budurwa ba, balle yanzu da kika zaka uwar mata." Ya fada yana kallona, ni dai sake baki nayi wannan mutumin dama haka yake bai da kunya, sai da abinci ya kusan kware ni.

" Ci a hankali, naga kina Min kallon zargi ne me zanyi da macen da babu igiyana akanta.

Tsawon shekarun da nayi ina tattalin samartakana ya tashi a banza kenan, ke ni ba dan iska bane ki sani kamar yadda kike da kamun kai haka nake kome na barwa Allah idan kika shigo gidana zaki fahimci ni saurayi ne, gal a leda.

" Da gudu na wuce ban daki ina fa
in.

" Don kaunarka da mai ka'aba ka fita wallahi ba zan iya jin maganarka ba.

" Shi bai ga wani abu da ya fada mara kyau ba, asalima gaskiya ya fa
a da ace shi dan iska ne da tuni bai tara yara a layi ba, duk yadda ya ga mata masu manyan kaya bai ta
a jin ya je gare su ba, sai yanzu wata kwaila da ita zata na mishi kallon tuhuma, yana hango yadda yake mishi kallon zargi.

Shi kan Allah ya tuba ai da rayuwar bata mishi dadi ba ace sai yanzu zai farwa matar da zai aura.

Amma itama she too shy, kamar irin yaran da suka fara zama yan mata.

Sai kuma abin ya bashi dariya ya sake murmushi....... (Da alamu shi kuma na shi salon kenan da maganar banza
saurayi yake gal a leda)
[12/15/2025, 4:48
PM] Maman Walid: 15
"Allah na tuba!" Na fada lokacin da na shiga ban daki, ina ji kamar kirjina zai bu
e zuciyata tayi waje.

Shi dai bai da kunya.

Motsin da naji a dakin yasa na ce.

"Waye?" "Ke bana son gulma fito uwar me kike a ban dakin?" Goge hannuna nayi na wuce na kwanta.

"Kin ci abincin?" Tura baki nayi ina kallon gefe.

"Kin koshi ko Yaya?" Ban ce mata kome ba, ta gama yar fadarta sannan ta kuma shiga rarrashina da nuna min kada na
ara wasa da da cikina, zan samu matsala idan ina wasa da cikina zai haifar min da matsala.

Ni dai ban ce mata kome ba har barci ya dauke ni.

Kwanakin da muka yi bana shiga harkansa koda kuwa ya samu ina wurin tashi nake na basu wuri, don na fahimci matu
ar yana wuri Mama mantawa yake da tab'a haihuwar mutum irina, ni kuwa kishi da haushin baya wani kula ni, nima haka kusan Mama ta fahimci haka ta ce min na je yana kirana a kasa, tunda na zo ma zauna mutumin nan yake danna wayarshi.

Kusan minti talatin bai da lokacina, haushi ya kara kama ni na mike zan tafi ya ce min.

" Can we walk?
Chapter 18 · 0% Book details