← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 48

Sashe 34

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ya janyo ni gadon muka zauna, a hankali yayi ta rarrashina har labarin ya sauya na rasa wani munafuncin ne ya janyo ni na bashi damar yin abinda na ce ko me zai min ba zan kara yarda da shi, na kuwa san nayi yaji domin har barkono sai da ya gaya min yadda ake nomarsa, kiran sallah la'asar ya saka ni mikewa zuwa ban daki nayi wanka koda na fito yayi barci, dama da Alwala na fito na shimfida abin sallah, na shiga gabatar da sallah.

Bayan na isar nayi addu'a, zuwa inda yake nayi na tashe shi yayi sallah, ya janyo ni na fada kanshi yana shafa fuskana.

"Tashi nayi sallah" "hmm but ban koshi ba!" "Cab yunwa nake ji!" Na fada ina kwace kaina na fito na daura abinci, ina ta aiki ya shigo da Jallabiya.

Sumbatar wuyana yayi ya zagayo da hannunshi kan cikina, ina aiki yana hana ni sakat.

"Ka rufa min asiri kada na kone, dama ina bazawara kaga sai ka auro budurwa Virgin!" Shiru yayi ya daina sumbatar ya dawo gefen firj din yana kallona.

"Allah ya baki hakuri." Ban kula shi ba, na gama girkin sannan na fito zuwa waje yana biye da ni na shirya abincin, kiran sallah Magariba ya fitar da shi, wurin karfe takwas suka shigo sanin halinsa yasa na ki fitowa, sai da ya zo don kanshi ya fito dani, na zuba musu abinci, haka dai na gama abinda ya dace musu na dawo dakina na kwanta, har wurin
arfe tara sannan Uncle Auta ya mana sallama gobe zai wuce Jos.

Ya koma lagos.

Ba kunya ya ce mishi.

"Allah ya tsare ka gaishe su ni kan sai kun gani."
Daga haka ya mishi sallama, tunda ya shigo daki wurin karfe goma saura, ya haura gadon da nake zaune ina karanta hisnul Muslim.

Ya kwace ya fara kallona kamar zai hadiye ni, a hankali labarin dai fushi na rasa inda na kai shi, dazun na zata ina masifar kewarshi amma a yanzu dai na gane baki
aya rayuwata zan bada saboda shi, domin yadda kome ya wakana ya kasa barin cikin kaina da zuciyata, abin ya tsaya a idanuna ba zan tab'a mantawa da wannan daren ba, ina kwance a jikinshi shafa kaina yayi ya ce min.

"Kin hakura zamu koma Lagos idan muka huta anan?" Kwantar da kai nayi a kirjinsa, nayi shiru kafin na d'ago ina kallonshi."idan muka koma ka cigaba da
yamar wani ya taba kwanciya da ni?

Kayi ta gaya min ni ragowar wani ne?" Rufe min baki da yayi da nashi, sannan ya kashe zancen babu yadda zaa yi na kara tunawa da mun yi wani rigima, kusan a tare muka yi wanka muka dawo ina kwance a jikinshi.

Har barci yayi gaba da mu, kusan washi gari makara muka yi, ya zuba min idanun ina barci.

"Tashi gari ya waye!" Da sauri na bude idanun, muka shiga muka yi alwala sannan muka fito a tare, bayan nayi sallah na fita waje, fitowa yayi shima yana waya bayan ya idar ya shigo ya samu ina
arin kunna gas, riko hannuna yayi ya ja ni zuwa daki, anya mutumin nan lafiyarshi kalau kuwa?

Kusan ranar yana manne da ni, bini bini, abu daya da na fahimci zai lalata min lokacina na tuna mishi zamu tafi gida yau, sai ya hakura ya kyale ni na huta, har muka ci abincin rana, don sai karfe biyu muka karya abincin rana kuwa sai yamma la'asar likis.

Karfe shida yayi mana a gida, da yake ana sallah Magariba da wuri sai da ya bude min kofar na fita don muna isa cikin harabar gidanmu muka hadu da Hafiz.

Haka muka shiga cikin gidan yana rike da jakata, ni kuma ina lafe a kafad'arshi, don bana son kallon Hafiz ma.

A tsakar gida muka sami Mama da Yadiko, kasancewar ranar juma'a ce ranar, muka gaishe su.

Daga yadda muka tawo Mama ta fahimci mun shirya, haka ma Yadiko sannan ya ce min..

"Bari na je sallah ko?" Gyad'a mishi kai nayi, yana fita suka hadu da Hafiz sai shigo murmushi suka yiwa juna.

Kowa ya wuce.

Dakin Yadiko na wuce na shiga nayi alwala.

Bayan na idar da sallah, na cigaba da azkar har bayan isha, sannan na na fito saboda Yadiko ta min magana, muka shiga ban tab'a sanin haka Abba yake fa
a ba, sai da ya saka Baban Jama'are a gaba ya wanke shi tas, sannan ya koma kan Hafiz ga Ya Umar ga Lauyar da aka dauka da yarjejeniyar kada wani abu ya kara shiga tsakaninmu da Hafiz, Abba ya ce mishi.

"Banda rashin kunya da rashin mutunci, yarinyar nan har hauka ta kusan yi kai nima sai da ka kusan kashe ni, a haka ban rabu da kai ba, ka lalata min suna ka ciyo bashi da sunana duk na rabu da kai Hafiz idan kai ba Tsinanne asararre bane ka fita hanyar Lubnah idan na kara jin wani abu ya kara tasowa akanka, zan ajiye zumunci da kara na daure ka sai igiya ya saura mara kunya, Ali yau na dawo maka da karar danka, idan ya lalata min auren Y'a wallahi zan dauki matakin da sai an rasa mai bani hakuri, ka ja mishi kunne idan ya har dan halak ne shi ya kara bibiyar rayuwarta sai na lalata mishi nashi rayuwar maciji da bai da ramin kanshi sai na wasu." Tass Abba ya mishi tare da buga mishi kashedi........
[12/24/2025, 10:15
PM] Maman Walid: 27
Sannan ya juya ga Baban Jama'are ya ce mishi.

" Na zata kasan yakana ne, amma na fahimci baka fahimci haka na, idan na kara jin labarin Hafiz a bakin Lubnah ko mijinta da sunan ya shiga rayuwar aurenta, na rantse da Allah zan yi abinda zai baka tsoro.

" Murmushi yayi kafin ya kalli dan uwansa ya ce mishi." Da gaske nake ba da wasa ba, rayuwarta da aurenta yafi min kome muhimmanci ban damu ba ace don tana auren mai kudi ne ba kome, na ji kuma na amince" yayi fadar ni kaina sai naji kamar an yantani daga wani kunci zuwa jin dadi, ya juya ga Turaki ya ce mishi.

"Idan ba zaka iya zama da ita a haka, ka sake ta yanzu nan!" Ya ajiye mishi takarda da biro, ba Turaki ba hatta ni sai da gabana ya fadi, muka kalli Abba da yake wani muzurai.

Alamar no mercy a cikin lamarinsa, kallon Turaki nayi da yake Allah bai mishi burbushin kunya ba, janyo ni yayi ya ce mishi."Wai Alhaji i love my wife, zan iya kome domin tayi farin ciki.

Daga yau ka kuma ganin Lubnah a gidanka matu
ar ba dalili bane babba kayi karana kotu domin a nima mata hakkinta, Alhaji a dokar
asashen duniya idan tayi
arana duk abinda na mallaka sai an raba biyu, a nan kuma ka bani takarda da biyo, wai ina son Matata wallahi idan zan fada maka ita mace ta biyu mai daraja a rayuwata, ni ba gara ka fille min kai zai min sauki da na sake wannan abin!" Ya shiga rattaba bayani, zamewa nayi na barshi ya yi ta rashin kunyarshi, na rantse bai da kunya har cewa yake.

"Ni fa naga
arin Lubna da ta xauna da mai furfura irina, waye ya sani ko hakuri take da ni, amma Alhaji ina kula da kaina!

Ina cin abinci me kyau ina.

" Da gudu na shiga parlourn na riko kunnenshi, ya kuwa taso.

" Ya zaa yi, ai haka zan bi Umarninki!

" Muna fita waje na ce mishi." Wai kai baka da kunya ne?" " Da nayi me?" Ai ban yarda mun kara shiga cikin gidan ba, na ja shi muka bar gidan.

Wannan tarin rashin kunya nashi.

Sai da muka dauki hanya na ce mishi." Ba kyau rashin kunya, ba kowani magana ake fada ba, wani ana shiru a gaban manya ko mutane, ba laifi bane confessing yadda kake ji, but abin kunya ne kayi ta magana ina kunyarka ya tafi?" Shiru yayi yana saurarena kamar wanda yake daukar maganar da nake amma can ya ce min." Hmmm meye amfanin na fadi abinda yake raina ku dai Hausawa akwai ku da daukar aiki ja!" Jan kumatunsa nayi, ya sake murmushi muka cigaba da hiran.

Wani lokaci baka sanin yadda kuke son juna, sai wani abu ya gifta tsakani zaka fahimci ai dama ashe irin wannan rayuwar akwai shi, koda muka dawo gida wani magani da Yadiko ta bani tun da muka isa na shiga kitchen ina damawa da madara ya shigo, zagaye cikina yayi da hannunsa yana sinsinsar hijab dina.

"Me ake dama mana ne?" Share shi nayi na cigaba da abinda nake ya sumbaci kaina yace min.

"Nima zan sha?

Idan ta mallaka ce sai mu mallake juna." Murmushi nayi na ce mishi." Yanzu ma ban mallake ka ba, ake ganin haka idan kuma na mallake ka sai an hada da rokon Allah." Shiru yayi bayan na gama dama gumbar na ajiye, fruit da nake da shi ja ciro na yanka na nika mishi, kankana ds kokumba na saka madara da zuma, na fito ina mai tura mishi mug din, ya kurba.

"Meye sirrin?" Dauke kai nayi ina sha muna kallon laptop dinsa da yake aiki.

"Yaushe zan koma aiki?" "Ai na amshi takardan barin aikin da kika yi can baya!" "Ban gane ba ba ka yaga ba?" "Eh amma na saka kin ajiye aiki domin kin zabi zaman aure akan aikinki." Kura mishi idanun nayi kai tsaye nace mishi.." yaushe muka yi haka Sir?" "Sai dai saniya!

Amma aiki kawai ki zauna a gida ki bautawa Allah da aurenki.

"
Naji haushi amma sai na share naki bawa maganar muhimmancin da zai ce ina jin zafi ne, can ya ce min.

"Baki ji haushi ba ne?" Tab'e baki nayi ka ce mishi..

"ko ka
an ban ji haushi ba!" Na fada ina murmushi, kallona yayi kafin ya ce min.

"A'a Lunah kada ki yarda ki boye kin ga ni fada miki kome nake gara ki gaya min kada na fita na ji bakya garin nan!" Dariya nayi na ce mishi.
Chapter 34 · 0% Book details