← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 48

Sashe 36

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannu da zuwa sannu kun sha hanya?"inji matar Uncle Auta "Alhamdulillahi da fatan mun same ku lafiya?" , Matar Ubaid tana gefe tana cin chew gum.

Kallonta nayi na ga yadda take wani dauke kai na ce mata.

"Sannun da fatan an same ku lafiya!" "Lau ya yaji?" Ta fada tana kallon cikin idanuna, ganin hankalin mazan baya kanmu na ce mata.

"Alhamdulillahi, gamu nan dai mun yi yaji mai capacity.!"
Murmushi tayi tana yar dariyar renin hankali ta ce min.

"Allah yasa ba wurin tsohon kwano aka koma ba, daga nan gida aka nufa." Kallonta nayi da kyau na fahimci maganar da ta min, sai na kallu Turaki da yake d'aga min gira.

"Na wanke na bashi ya sha ko wurin tsohon kwano na koma ba zai iya tari ba, mace da ta isa bata kuka akan namiji bata bin namiji don ya zauna da ita shi yake binta don ta zauna da shi, ni ko ban zauna da Turaki don Allah ba zan zauna don kawunsa da amininsa." Ina gama fadar haka na wuce na barta nan, na je na fito na sami ko ina Tsaf, na fito na cewa matar Uncle Auta.

"Sannu Maman Daddah, gidan yayi kyau.

Ubangiji ya haka Uncle Auta hango wata."
"Ke ya kamata ko fara yiwa kanki addu'a domin mun gaji muna son Yara a gidan Turaki!"
"Eh tow ai ni ban hana Turaki auro wata mace ba, tabbas yana bukatar wata mace a rayuwarsa domin ya haifa mishi Yara, amma ban sani ba ko shi yana maraba da second wife don nasan ni dai ba raguwa ba ce sannan ba xan yi kukan don Turaki yana tare da wata mace ba, domin duk wacce zai aura sauran bazawara ce!

" Na fada ina d'aga mata gira, duk Mazan suka juyo gare mu.

" Wai me kike nufi da ni?" Matar Ubaid ta tambaye ni, dariya nayi nace mata.

"Kamar ya?

Magana muke cikin raha kuma na ga babu fada!" " Karya kike Lubabatu Usman Umar Jama'are, kina jin haushin don Turaki yana son Nihla ce!?

Wato don kin lalata mahaifarki shine bari ki saka idanun akan Yarinyata da yake so!" Dariya nayi mata na ce mata.

" Ni bana haushi akan yarki kuma ba zan fara ba, idan ta ni ce ki na gaya miki idan kin so saboda so ko bashi auren Nihla shine karshen soyayyar da zaki nuna mishi kenan na san kin isa."
Cikin jin haushi ta ce min.

" Shi yasa kika shiga kika fita aka fasa aurenshi da yar uwarsa ko!" Dariya abin ya bani na ce mata.

"Allah ya min tsari, aure ai dole Turaki yayi aure wai tsaya akan me nake baki amsa ne?

Dalla ja tsumman rayuwarki idan kin isa ki hana Mijinki aure mana idan ni na hana nawa, aure kuma ki rubuta ki ajiye turaki zai yi shi amma ba a yadda kike so ba!" Zata kara magana Mijinta ya ce mata.

" Ya isa haka Falilah ya isa kada kuma cewa uffan.

" D'aga mishi hannu Turaki yayi ya tako gabana ya riko hannuna ya ce min." Da gaske kina son na kara aure na haihu?" Na zata ya amshi maganar ne, cikin kwarin gwiwa na ce mishi.

"Eh kai kana bukatar Yara ko ranar a can na ga yadda kake daukarsu kaima ya mata ace akwai a gidan nan." Wani irin kallo yake min ." Kina nufin bakya kishina!" Murmushi nayi na ce masa.

" Ina kishinka kai, kawai ni dai ina son ka haihu!" " Ya Isa ban san bakya bukata na a rayuwarki har haka ba, kin fini idanun ganin mata ne ko kin fini zuciyar son Yara;" daga haka ya juya ya bar gidan, ina ganin yadda take murmushi na ce mata.

"Ki yi dariya a fili, ni bana tsoron fushinsa, amma duk ranar da nayi fushi hatta Mijinki gashi nan bai isa yayi barci cikin kwanciyar hankali ba."
" Kyale munafuka akwai abinda take nufi!" Inji Matar Uncle Auta, Ubaid ma ya mata tas suka fito.

Har dare bai dawo ba har na kwanta cikin dare na ji shi a bayana, juyawa nayi ina kallonshi, shafa kaina yana fa
in.

" Shiiiiii;" tuni barci yayi gaba da ni, da asuba ina farkawa na ga baya nan, haka na farka nayi alwala.

A hankali sai na fahimci fushi yake da ni kuma yaki yarda mu fahimci juna.

Haka yayi ta jera kwanaki yana fita babu karyawar kusan sati biyu, ranar na tashi na ga not yayi tafiya zuwa abuja na kira bai
auka ba, sai dare ya kira ni, nan ma babu wani alamar ya huce, ranar da zai dawo ya turo min sako na shiga aiki na gama.

Koda ya dawo ya fita ya dauko Nihla suka shigo gidan, wurin karfe shida sai ga wata yarinya budurwa kusan suna yanayi da Maman Nihla, ta shigo tana wani dan jiji da kai kallo daya nayi mata na watsar cikin iyayi da kwailanci take gaida shi yana parlourn sau daya ya amsa bai kara bin ta kanta ba, wai tazo daukar Nihla, amma ta zauna tare da saka shi.

A raina na ce yau dai ga budurwa nan a gidan.

Haka ta gama iyayi bai d'ago ya kalleta ba, yana gama cin abincin ya dauki yarinyar ya fita da ita, itama zuruf ta bishi, na gyara zamana.

Abubuwan sun min yawa, don haka na zauna jiranshi har karfe sha biyu ba dare, bai san ina parlourn ba, ya shigo na haska wayata.

Cak ya tsaya a hankali na isa bayanshi, don ina ganinsa ta gaske da yake shigowa na waje, na rungume shi gam.

"Ina sonka Bilal, ina sonka ina kaunarka ina kishinka, amma ka tambaye ni dalilin da na ce kayi aure?

Kasan me yasa nake son kayi aure?

Idan kace ba ka so ban isa nayi maka dole ba, amma ka sani ko ban saka ka kayi ba dole kayi domin Yara suna cikin jin dadin duniya, ka sani ba zan maka dole ba, amma wannan silent treated din yafi kome zane ni, gara ka gaya min gaskiya zai fi min sauki da sassauci.

Ba zan kara maka magana ba amma ka daina azabtar dani da haka Please." Na fada ina kuka, janyo ni yayi yana fa
in.

"Am curious da kika ce na kara aure, ni a ganina na auri mace ta haihu da ni ba ke ba, cin amanar kauna ce, ba adalci ba ce ba kome ba ne son zuciya ce.

" Girgixa kai nayi ina kuka na ce mishi." Ba cin amana bane, adalci ne zaka yi don ka haihu da wata mace mace ba wani abu ba ne.

Wallahi ba kome ba ne kyautatawa ce da adalci!"
" Ba zan iya adalci akanki ba, zan auro mata nayi ta zaluntarsu, zan ta cutar da su saboda ke ina sonki da bana iya dauke idanuna akanki a kwanakin da nayi hakuri nake, amma ba zan iya son wata mace bayan ke ba.

Zan cutar da ita su kuma zasu cutar min dake!" Rike fuskarshi nayi cikin kuka nace mishi.

" I miss you baby;" na fada ina shashekar kuka, rungume ni yayi yana fa
in.

"Bana da ra'ayin wata mace Allah ya gani amma idan wata tazo ba yadda na iya ke daya nake so!"
Shi kenan fa fada ya kare nayi alkawarin ba zan kara mishi maganar aure ko haihuwa ba, kwanaki biyar tsakani ya shirya mana tafiya zuwa ganin likita ni da shi, kasar Ingila.

Dama nasan matsalata ban boyewa likitan ba, ya bamu test ya kai goma, kullum ana mana daya kullum sai da muka yi kwana goma aka tsaya jiran sakamakon.

Sai da muka samu kwana hudu kafin aka kiramu likitan ya kalle ni ya kalle shi kafin ya ce mishi.

" Kana da Chance sosai na haihuwa, amma ita gaskiya babu Chance sosai domin duk wani hanya da kwayar halittar zata shiga ta wuce har ta samu kwan halittar ta ya toshe.

Don haka zamu iya cewa kai baka da matsala akai haihuwa matsalar ta Madam ce itama da a iya magance ta amma sai ta amince ko nace kun amince sai ayi mata.

HSG" zuba mishi idanun muka yi kafin muka kalli juna yadda kuka san ana mana hisabi, saboda tsananin tashin hankali.

Mene ne kuma HSG?

Kamar yasan abinda muke nazari ya sake murmushi ya ce mana.

" Ku kwantar da hankalinku ba wani babba al'amari ba ne!"
(Kuyi hakuri don Allah bana jin dadi amma da sauki sosai sannan masu kodai kodai
Wallahi bashi ba ne hmmm idan shine ai maganar rubutu ya kare wai wata Shekara zan cigaba idan da shine Nagode sosai Ubangiji ya karo zumunci)
[12/25/2025, 10:02
PM] Maman Walid: 29
Sauke ajiyar zuciya muka yi lokaci guda, yana rike da hannuna.

Wani irin tsoro yana fisgana.

Na kalle shi murmushi yayi min irin na kwantar da hankalina, sannan na mai da idanuna kan likitan.

Murmushi yayi ya fara zubo bayani kamar haka.

"Da farko dai zan muku karin bayani akan yadda ake yin HSG"
" A harshen Hausa, HSG (wato Hysterosalpingogram) wani nau'in binciken likita ne na musamman da ake amfani da hoton X-ray da wani magani mai ruwa (dye) domin duba mahaifa da magudanar kwai na mace."
"Ga daki-daki bayanin ma'anarsa da kuma dalilin da yasa ake yinsa" sai da ya sauke numfashi kafin ya kalle mu, ganin yadda na gama firgita, ya kalli Turaki yana murmushi ya ce mishi.

"Na ga kamar kai kafi madam karfin zuciya ko akwai tambayar da zaka yi ne?"
Jinjina kai Turaki yayi yana matsa hannua ya ce miishi,
"Mene ne Ma'anar HSG?"
Cikin nutsuwa da kwarewa likitan ya ce mishi.

"HSG gwaji ne da ake yi a sashen hoton X-ray.

Likita zai sanya wani siririn roba ta farjin mace zuwa cikin mahaifa, sannan ya tura wani ruwan magani.

Wannan ruwan yana haskaka cikin mahaifar da bututun da ke kai kwai (fallopian tubes) domin a ga yadda suke a cikin hoton X-ray."
Gyad'a kai yayi yana me kara kallona, jin irin azabar da za ayi min ban san lokacin da hawaye ya fara sauko min ba.
Chapter 36 · 0% Book details