← Book details Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 48

Sashe 25

Alaƙar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda na za
i wasu abubuwan wasu kuma na bari ya sake murmushi yana fa
in " kina loss weight ko?" Ci yayi yana fa
in "cigaba da rage kiba, kin ga ni na ci Abinda kika bari ina laifi." Haka muka gama sannan aka kwashe ya riko hannuna muka tafi dakin da Kakarshi ta wurin Uwa take, ina shiga ta rungume ni tana fa
in.

"Labubu kin ji sauki kenan?" Gyada mata kai nayi ya ce mata.

"Granny meye matsalarki da ni yanzu bayan na yi aure kina min kallon banza ko kishi kike ne don nake na yi ba?" "Allah ya rufa min asiri." Ta fada tana buga mishi sanda ya kauce yana dariya sannan ya fita ya barmu a dakin, mun sha hira da ita kafin ta ke gaya min "an jima zamu koma gida ma yaushe zaki zo mana!" Murmushi nayi na ce mata "Sai ya kawo ni!" Haka muka yi ta hira jife-jife har na tayata hada kayanta, ta dauko kudi me yawa ta bani, nayi ta Godiya.

Shigowa yayi ya ce mata.

"Ki fito gashi an zo
aukarki!" Ai kuwa na rakota zuwa waje, a lokacin suke gaisawa da sauran mutanen gidan, haka ya rakata har wurin motar ta kira ni.

A hankali na isa wurinta na tsaya, riko hannuna tayi ta saka min abu a cikin hannuna.

" Ki kula da Mijinki da kyau, ki kuma kula da kanki." Ta rike hannuna alamar tana bani abu me muhimmanci, sannan ta sake hannuna yazo gefena ya rufe mata kofa yana fa
in.

"Granny yarinyar nan ta kwace min ke!" Murmushi tayi tana fa
in.

"Ka taimake ni ka rike musu yar mutane!" "In sha Allah!" Ya fada, bayan ya ja hannuna baya, suka tashi motar suka bar gidan, yana d'aga musu hannu.

Sannan ya mai da ni can parlourn Alhaji ELYakub Kumo, muka zauna a rough carpet din parlourn, mika min wani album yana fa
in.

"Wannan hoton zuriarki ne!" Amsa Yayi ya mika min, a hankali na fara bude shafi zuwa shafi.

Hoton Babanshi ne na farko ya matso kusa da ni.

"Wannan shine Papa!" Juyawa nayi ina kallonshi.

"Kuna kama!" Bakin shi na ji a kan hancina.

"Sosai kai!" Ya fada bayan ya sumbaci hanci.

Sosai ya matso kusa da ni, kamar zai boye ni a jikinsa.

Wani hoto na bude, hoton Mamanshi ce.

" Mammy ko?" " Ya aka yi kika san Mammy nake kiranta?" Ya fada yana sumbatar kuncina.

" Bari mana Chairman yana nan fa?" "Tuni ua gudu parlourn wurin Matarshi." Da mamaki na kalli wurin da yake babu alamar shi.

Gira ya d'aga min.

"Ai na gaya miki, ni lamarina mai karfi ne!" Tura baki nayi, yayi maza ya rike bakin da yatsarsa guda biyu.

"I like this lips!" Ya fada yana sakewa.

"Kika kara tura min baki sai na ciza!" Hoton bikinsu ba bu
e.

"Lokacin ina zero kafin na zama plus." Shi dai bai da kunya ya more, ture shi nayi ina hararansa.

"Me yasa kake da matsala?" "Saboda ni ne gidan haya!" Murmushi nayi ya kai hannunsa yana tab'a ni, "don Allah kada ka hanani kallon!" Ihun da muka jiyo a waje yasa muka kalli juna sannan muka kalli kofar, Badriyyah ce sanye da wasu kananan kaya a jikinta.

"Idan ka ce ba zaka aure ni ba it's ok, but ka auri wannan karuwan yafi kome disguise a cikin wannan Familyn wallahi sai na kashe ka na kashe ta, sannan na kashe kaina.

" Ya fada tana nuna mu da wuka.

Mikawa yayi ya nufe ta, ta fasa ihu tana fa
in.

" Kada ka matso kusada ni" ta fada da karfi zata yanka hannuna, kafin ta d'ago daga kallon inda ya dace ta yanka ya rike hannunta.

" I don't care idan kika min wani abu, kuskuren da kika yi shine involved din Matar turaki cikin lamarin shine kuskurenki!" kwa
a mata mari sai da ta sake fitsari, ai wannan katakon hannun nashi nasan za ayi haka..........
[12/18/2025, 3:54
PM] Maman Walid: 20
" Bilal kashe ta zaka yi?" Inji Uwarta, ta fada da hargowa.

Bawan Allah nan ya shafawa idanunsa toka yana fa
in.

" Kika sake riko wani abu da sunan matata don ubanki sai na binne ki da ranki ina wasa da ke?

Mara kunya ni nayi maka da wadancan sakarkarun da suke bin ki ne?

Na kara ganinki da sunan kin zo gidana ko wurin Matata da sunan hauka sai na rufe tarihinki!" Ya hankad'a ta can, t fa
i tana kuka.

Kallon Uwarta yayi ya ce mata.

"Ba ita ba ke kanki, ki fita idanuna wallahi idan wani abu ya samu matata sai na baku mamaki." Ya dawo inda nake ya zauna ya barsu da bakin ciki kallonshi nayi ya sake murmushi.

"Yi kallonki kin ji ai namiji na gefenki babu karen da ya isa ya miki haushi na kyale shi." Ya fada yana rike min habba na.

Sai da suka fita ya ce min.

"Lubabatu?!" Na sha mamaki da ya kira sunana domin bai ta
a yin haka ba.

" Dangina ne, kada ki rena min su.

Zan yi iyakar kokarina na ga sun miki adalci.

Tun ina yaro na taso bama shiri da su, sai Uncle Auta." Murmushi yayi ya kwanta tare da daura kanshi a cinyata yana fa
in.

"Ina kewar Mammy sosai!" "Papa fa?" "Not yet!" Kallonshi nayi na tuna abinda Granny ta gaya min, wato ba iya fusata yake da kowa hatta mahaifinsa bai bari ba, Innalillahi wainnalihir rajoun, wallahi sai naji ya ban tausayi.

"Papa ya bata abubuwa dayawa." "Bai bani ba, ya bani ya kwace je betrayal me." Sai na rasa bakin magana, nayi shiru lokacin da aurena ya mutu Abba fushi yayi da ni ya kuma zare hannunsa a kaina, a lokacin ni ka
ai nasan yadda nake rayuwa.

Ganina ake but ina matukar shiga damuwa.

Dakyar ya fara amsa gaisuwar da nake mishi.

Shafa kanshi nayi na ce mishi.

"Ba kyau fushi da iyaye!

Kowani irin Yanayi zaka tsinci kanka kada kayi fushi da su, ba ina son na ce kayi hakuri ba ne, amma ina son na tuna maka hakkinsu akanka ne.

" Wato akwai wani abu da na fahimta a rayuwa ba zuwa Islamiyya ka haddace kur'ani ake bu
ata ba, yaro ya san waye Allah da hakkin Allah shine ake bukata, sannan yasan soyayyar Allah da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kafin ahalul Baitu da Sahabbai, har zuwa kan iyaye.

Mafi kololuwar daraja na wannan matakai uku ne, kafin zuwa ga Iyaye.

Shafa kanshi nayi ina jin tausayinsa har cikin raina, duk yadda aka yi yana da trauma akan Iyayensa.

Hawaye ne ya shiga zubowa daga idanuna yana d'iga akan fuskarshi.

"Me kuma aka yi?" "Ba kyau fushi da iyaye!" Cike da mamaki yake kallona bayan ya tashi zaune.

"Me ya kai ki personal life dina?" Rike hannunsa nayi, kuka na saka mishi..

"ka janye fushinka akan Mahaifinka ba haka yake bukata ba!" Zuba min idanu yayi ina iya hango yadda fuskarshi tayi ja.

"Ke idan aka miki haka zaki ji dadi?

Ko da yake kema ai kin yi min karya na rashin gaya min baki da aure me yasa rayuwarku take cike da karerayi ne?" Kallonshi nake na kai hannu zan rike shi ta kwace hannun.

"Na gaya miki gaskiya, kada ki kara tab'a ni!

Kannena uku da mahaifiyata hudu suka mutu bai iya kiran Makarantar ya gaya min ba, ya boye min haka bai ishe shi ba sai dawowa nayi na samu yayi adding another wife, gaya min me kike so nayi?" Baya na ja musamman yadda ya hayayyako min, na kara fashewa da kuka.

"Matar da ya aura sakatariyar Mahaifiyata ce, taya ba zan tsane shi ba waye ya sani ko sun kashe mahaifiyata ne don su cigaba da abin!" Da sauri na kai hannuna bakinshi.

"Allah yana ganinka kada ka yi mishi kazafi, kada ka tozarta shi.

Sadauki ne da yayi kokarin baka kyakyawar rayuwa.

Yayi maka adalci ta hanyar ka fuskanci abinda yake gabanka.

Bai d'aga maka hankali ba sai da ya tabbata ka sami abinda yake ganin zai gyara maka gobenka, iya adalci ya maka ya maka adalci bai lalata mutuncinsa da kimarsa ba, ya aurota duk da bata addininsa da ta same ka ta amince da addininsa, ta kuma zauna da shi ba tare da ta hango gazawarshi ba, shi din jarumi ne da babu irinsa har ya koma ga Allah yana son ya zauna da kai ya fahimtar da kai waye shi, ya gaya maka yadda yake jin ka.

Amma baka fahimce shi ba.

Yayi kuskure wurin auren yar dakinta amma kuma rabon Jasminah kike tsammanin bai isa ya dauki rayuwarta ba ne." Rike hannunsa nayi tare da matsawa kuwa da shi, kafin na rungume shi ina kuka.

Na janyo kanshi na rungumar a kirjina ina shafa bayansa.

" Nasan anyi maka laifi amma kada hukunta shi ta haka, wata rana kai Uba ne da sannu zaka fahimci me yasa iyaye suke hakura da wani abu domin Yaransu.

Zaka gano yadda suke tsoron kare yaransu daga wani abin da zai shafi bayansu.

Wallahi ban tab'a ganin jarumin Uba irin Papa ba je did him best to protect you!

Kuma har yana kan kare ka, ya cusa maka kiyayyarshi domin ka zama dodonsu, kuma yayi haka ne domin ka tsaya da kanka.

Yaki nuna maka soyayya domin kada ya saka maka soyayya da kawazuci kamar yadda Mammy tayi yake damunka, ba nan kulawarsa ya tsaya ba, ya bude maka idanunka ka fahimci mutanen da suke zagaye da kai, ya cusa maka niman na kanka domin kada ka jira abinda Mammy da shi suka tara maka.

Idan har haka dai saka na zama Uwa ta gari zan yi tsalle na rungume wannan halin nashi.

Domin ya nuna min ba koda yaushe ake tafiya a yadda ake so ba." Kai ya d'ago yana kallona da idanunsa da suka yi jajjur, ga Daddah a kofar shiga parlourn.

" Dubi ka ga mahaifiyarsa ce, kalli yadda take kuka danta ne fa, and kasan yadda take
aukar abin a ranta?

Kasan yadda Uwa take girmama me kaunar danta?
Chapter 25 · 0% Book details