Sashe 89
Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun daga shigarsu dakin da Mu’azzam ya sanya mukullin shi ya bude, abubuwa basu kara daidaituwa ga Aalimah ba, duniyar ta bata kara zama cikin seti ba, haka shima Mu’azzam. Duk yadda ta zaci kewar data ke jin ta yi ta Mu’azzam mai dumbin yawa ce, ashe na fatar baki kawai ta sani. Ba da sanin ta ba kowacce gaba ta jikinta tayi kewar tasa ba zuciyarta kadai ba. Da farko akwai dari-darin abin da ‘yar fargaba a tare da ita. Kafin wani dan lokaci kuma ta tsinci kanta da mika wuya bakidayan ta. Sakamakon ganewa data yi cewa Mu’azzam din da ba shine yanzu ba. Gabadaya Mu’azzam din data sani a baya ya canza mata, things are going very soft and gentle from him. Ta yarda bayan lafiya da nutsuwa harda kwas (course) a soyayya ya samu wanda a baya bashi da kamarsa. A can baya ta haqqaqe abinda ya sani shine ya biya bukatar sa anyhow; disregarding her own emotions. Kuma akai-akai kamar cin abinci. A hakan kuma take son abinta, take kula da dukkannin bukatun sa, domin tana gamsuwa ta kowannne bangare. Amma yanzu it goes along with her own pleasure and contentment. Tare da kula da rashin jigatar da ita a matsayin ta na mai tsohon ciki. Hawaye ta soma yi na farin ciki da godiya ga Allah. Ta yarda Mu’az ya samu lafiya. Komai ya koma dai-dai yadda ya kamata ya koma. It tastes good.... It tastes romantic. Wata rayuwa ce da bata taba mafarkin samu a Mu’azzam ba. Daga nan kuma sai barci, barcin da suka dade basu yi mai nutsuwar sa ba a kafatanin rayuwarsu. Ba su suka farka ba sai karfe biyar na asubahi, tare suka yi jam’in sallar asubah. Sun dade suna addu’a batare da kowanne ya san abinda dan uwansa yake roka akan dan uwansa ba. Aalimah rokon Allah take ya dorar da lafiyar Mu’azzam, bata taba samun nutsuwa a rayuwar aure irin ta yau ba. Tana rokon Allah ya dorar da wannan rayuwar ya dawwamar dasu cikin alherinsa. Ga Mu’azzam, rokon Allah yake ya sauki Aalimah lafiya, ya raya musu ‘ya’yansu rayuwa ta addinin muslunci. Abubuwan da bai taba ji akan Aalimah ba, su suke kara overwhelming dinsa yanzu. Ashe wannan sune feelings.....sune emotions. ..... sune affection… sune so da kauna wadanda a baya bai san su ba? Idan kuwa har sune dan uwansa Aboulkhair yayi kokari, kokarin da a yau ya jinjina masa, yayi masa sadaukarwar da shi ba zai iya ba! Don abu na karshe da bazai iya ba a yanzu shine rabuwa da Aalimah!!! Suna kwance kalmashe cikin jikin juna, lullube cikin lallausar duvet, sanyin Ontario na yau kamar har yafi na kullum ratsa kashi da bargo. Mu’azzam yace “umh Aalimah, gaya min yaya bayan rabo? Na same ki cikin yanayi na kwanciyar hankali da jin dadin rayuwar da ta same ki, sabanin ni da darare suka yi ta wucewa da yawansu idona biyu har ketowar alfijir. Bana komai sai zubawa ‘ya’yanki ido suna nasu baccin ina kallon fuskar ki cikin fuskokin su. Me yasa ki kayi tunanin cewa rabuwar mu ita ce mafi alkhairi?†Aalimah ta kwantar da kai bisa kirjin Mu’azzam tana mai jin komai na rayuwa yanzu yayi mata daidai, daidai da yadda take kwana tana addu’ar Allah ya mayar mata da shi, daga lokacin data yanke musu hukuncin da ta ke ganin shine abinda ya dace dasu bakidaya, tace. “Ya Mu’az nima bansan dalilin da yasa na yanke hukuncin dana yanke ba, abinda na sani a lokacin shine I’m desperate, hopeless. Amma daga ranar da hakan ta faru ni kuma ban kara rayuwar farin ciki da jin dadi ba, ji nake kamar na yanke bangaren daya kunshi dukkan farin cikin na yar. It was regrettable, though, ko kai ne a matsayi na a lokacin abinda zaka yi kenan. Dawowar Monsieur Aboulkhair abin farin ciki ce a garemu amma hakika ta ruda ni sosai. Wani al’amari sai Ubangiji. Zawarcin bashi da dadi ko kadan, bana son tunawa, kowa bai min ta dadi ba sai Daddy da Mummy, su kadai suka karbi uzrina, kai dan gata ne Ya Mu’az ban ga wanda ake so a zuri’ar mu kamar ka baâ€. Dariya Mu’azzam ya saki yayi cuddling dinta sosai, dan kankanin bakin ta yayi kissing kafin yace. “Kina jin dadin yimin wannan gorin Aalimah; ba wanda ake so a gidan RAZEE kama na, na yarda basu yi miki ta dadi ba amma kisa a ranki duk a cikin son da suke miki ne. Fatan su da burinsu shine mu kasance tare, mu raini ‘ya’yan mu tare. Me nake da shi a duniya da zan sakawa Aboulkhair wannan sacrifice din da yayi min? Wallahi babu. I love him to an extent. Ji nake idan zan yi ta haihuwar ‘ya’ya maza ina saka musu Aboulkhair yayi kadan ya nuna godiyata a gare shiâ€. Haka suka karar da wunin yau bakidaya a gadon barcinsu, sallah kadai ke tada su. Abinci daga hotel din ake shigo musu dashi, Ilham ta ce zata aiko Mu’azzam ya ce ta bar shi. Baya son ko kuda ya gitta a tsakanin su. A shekaru bakwai da suka yi tare a baya, basu taba samun shaquwar da suka samu a kwanaki ukun nan da sukayi a Ontario ba. Soyayyar ta ninku, ta karu, ta rubanya. Basa ganin kowa a gabansu sai junansu. Mu’azzam ya kira Madame Ruqayya mai rainon su Basma yace ta bashi Aboulkhair da Basma. Basma na karba ya mikawa Aalimah, sallama kawai Aalimah tayi Basma ta shaida ta, soyayyar uwa da Da sai Allah. Maimakon Basma tayi murna da jin mamarta kuka ta saki, tana fadin Mummy kin guje mu, kin barmu mu kadai a wajen Madame da Daddy, kin ki dawowa saboda kin daina sonmu.....â€. “Basma uwa tana daina son dan ta? Wannan impossible ne. Baki San uzrina ba Bassy, I’ve a green great giant surprise gift for you. Tare da sabon Baby zan dawo, mace ko namiji wanne kika fi so?†Nan da nan Basma ta share hawaye ta saki dariya tana fadin “Allah Mummy? In dai da gaske kike to na daina fushi, dama duk ‘yan ajin mu suna da baby a gidan su banda ni, yaushe zaki dawo?†Aboulkhair ya kwace wayar daga hannun Basma, “Daddy your boy is missing you, yaushe zaka dawo?†Aalimah ta lumshe idon ta, soyayyar uwa da Da na ratsa ta. “Yaron na Daddy ne kadai ko? Ya manta da Mamansa?†Aboulkhair ya zabura, ya sake kankame wayar a hannunsa. “Mummy ke ce?†Nice Monsieur Aboulkhair, ina fatan ba ka yiwa Madame Ruqayyah rikici?†Shima sai yasa kuka yana fadin “mummy me muka yi miki kika tafi kika bar mu mu kadai? Ko a waya bakya kiran mu? Daddy kullum baya bacci sabida kin ki dawowa, don Allah Mummy ki dawo bana son zama da Madame Ruqayya ke da Daddy nake so....â€. Ta kasa tsayar da hawayen da suka shimfido mata, ta kai yatsunta ta share su, tace “Aboulkhair it’s a promise nan da kwana biyu zaka ganni a Vegas tare da Daddy. Amma sai ka daina cewa baka son zama da Madame Ruqayyah, kaga bazata ji dadi ba tana iya kokarinta a kan kuâ€. Ya juya ya dubi matar ya yi mata murmushi ya ce “Madame sorry. My Mummy is coming back soonâ€. Yau dai wayar ta uwar da ‘ya’yanta ce ko uban basu nema ba har suka kare hirar, wadda ake yin ta ana sharar hawaye da koke-koke. Mu’azzam yana daga gefe Aalimah ta yi matashi da gadon bayan sa duk yana jin su yana murmushi. Ya karbi wayar daga hannunta ya kira Malam Razee, ita kuma ta shiga toilet don yin alwala. Tana jin su suna hira yana gaya masa ai yazo yayi biko gashi a hotel tare da Aalimah. Daga bayin Aalimah ta saki salati tana fadin “haba haba Ya Mu’az? Haba don Allah†Malam Razee yace “hotel kuma? A wane gari kuma?†Yace “wani kayataccen hotel ne a birnin Ontario, ita Ontario din cikin kasar Canada take, nan Aalimah tayi hijira gidan Baffanta na wajen uwa, a cewar ta tunda bakwa son taâ€. Murmushi Malam Raazee yayi yana hamdala a fili da boye saida ya baiwa Mu’azzam tausayi. Ya tabbata har hawaye yake yi duk da baya ganinsa. Malam yace “ko yau mutuwa ta zo, burika sun gama cikka. Kowa dake cikin ‘ya’ya da jikoki na ya samu rayuwar da hankalina ya kwanta da ita. Ka rike ‘yar uwar ka amana Mu’azzam ku rufa asirin juna. Allah yayi muku albarka, ya albarkaci zuri’ar kuâ€. 7/13/21, 6:00 PM - Buhainat: Kafin kace meye wannan zance ya tadda su Inna Kasisi, Inna Bintou, gidan su kawu Oussama da gidan Daddy1. Aalimah da Mu'azzam sun koma har sun tafi yawon amarci. Zancen ya baiwa Gumsu dariya tace da wanda ya zo ya gaya musu “wane amarci da zungureren cikin?†Amma zuciyar ta kal kamar takarda. Gumsu ta dau waya ta hau doka kira Nigeria, Basmah ta kira tace “kin ji wai yar tawayen can ta gaji da zaman gida ta koma gidan ta har an tafi honeymoon wata kasa, nace wane yawon amarci da zungureren ciki?†Basmah tace “kayyasa! Dadi na da gidan Malam Raazee karawa miya gishiri, wani lokacin har da onga, ba wani yawon amarci da suka tafi dama tana can shine ya bita†Gumsu tace “wai ba tana gidansu ba?†Basmah tace “tunda son kai ya rufe maku ido yaushe zaku damu da inda take? To masu sonta sun dauketa zuwa Canada ko wata daya bata rufa anan Kano baâ€. Gumsu ta ji duk kunya ta kama ta, tunda Aalimah ta bar Niamey bata kara neman ta ba balle ta tambayi lafiyar cikin jikin ta tace “don Allah ki bani lambar taâ€. Basmah tace “wallahi banni badawa, in da kunya ai baza ki nemeta ba yanzu data dawo gidan Dan ki. Watanni sama da hudu baki kirata ba ko don jin lafiyar abinda ke cikinta sai yanzu data yarda ta koma gidan dan ki? Wannan son kai a fili da me yayi kama!â€. Gumsu tace “ki yarda dani Basmah ba son kai bane ba, tausayin Mu’azzam da yaran nake ji. Yanzu data yarda ta koma baki ji dadin dana ji ba, ba shikenan komai ya wuce ba?â€