← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 91

Sashe 70

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“Malam ga shi Inna Bintou ta ce a kawoâ€.
Hannu biyu ya sa ya karba ya ce, “Madalla da Bintou da jikanyar ta, an gaishe ku, madallahâ€.
Ta juya za ta fita, sai kuma ta dawo ta tsuguna.
“Malam Aunty Gumsu-Moiram ta yi min waya dazu tace in je in mata kwana biyu, na ce mata sai na tambaye ka tukunnaâ€.
Ya ce, “Ba yanzu ba Moiram ta yi hakkuri, bana so ki je ko’ina sai kin warware dukkanki, har yanzu ban ganki kamar yadda nasan ki ba, a bai wa Gumsu hakkuri inji niâ€.
Fuska a sake ta ce, “toh Malamâ€.
Ta juya ga Daddy ta gaishe shi cikin nutsuwa da sanyin muryarta.
Ya ce, “Anya Aalimah? Haka dan Adam zai rayu da damuwa bayan ba abin da za ta sa, ba abin da za ta hana? Dubi kasusuwan wuyanki, dubi idanunki yadda suka zuzzurma ciki. Don Allah don Annabi Aalimah ni Baban ABOULKHAIR ina mai cewa a karo na sau ba adadi, ki yi hakuri. Ki yi hakuri! Ki yi hakuri…â€.
Ko kafin ya kai karshe ya fahimci hawaye sun gangaro daga idanunta. Muryarta ba ta fita sosai. A sanda take cewa.
“Na yi hakuri Daddy, na dade da yin hakuri. Zuciyata ce ta ki daukar reality, ce min ta ke ba shi ne ya mutu ba, zai dawo. Don Allah Daddy da gaske ne??â€
Malam Raazee da Daddy Ishaq suka juyar da kai don share nasu hawayen.
Daddy ya ce, “Aalimah, wanda ya mutu ba ya dawowa. Ki yarda da ayar Ubangiji subhanahu wata’ala, kullu nafsin za’ikatul maut. Aboulkhair ba zai taba dawowa ba har abada. Ki bai wa rayuwarki da ke gaba kofa ko ya ya ne ta samu farin ciki kin ji Aalimah?â€
Daga kai kawai ta yi, don ba ta da abin da za ta yi bayan daga kan, ko ta yarda ko ba ta yarda ba, ya ce,
“Tashi je ki cikin ‘yan uwanki, Allah ya yi miki albarkaâ€.
Jiki babu lakka ta mike ta wuce cikin gida.
Bayan wucewarta da minti biyar daga Malam har dansa Ishaq babu wanda ya kara yin magana. Daga bisani Malam din yayi gyaran murya ya ce,
“Ni sai inyi ta wani tunani, a duk sanda Aalimah ta zo gabanaâ€.
Daddy ya ce,
“Tunanin mene ne Malam?â€
Malam ya girgiza kai, har da daga hannaye sama ya ce, “Uhum-um-umh-uhm, a bar kazar ‘yan boko cikin gashinta, yanzu in aka yi kokarin fige ta sai kun dawo da George Bush da Mungo Park gidan nan sabida kawo nassi na bijirewa da nuna kin amincewaâ€.
Murmushi Daddy ya yi, shi ma zuciyarsa ta yi nauyi. Babu mamaki idan ba irin tunaninsa Malam Raazee ke yi ba. Bai ja zancen da nisa ba ya yi wa Malam din sallama ya mike ya kwashi takalmansa ya fice don tafiya gidansa, wanda ba shi da nisa da gidan iyayensa trackable distance ne.
7/5/21, 11:40 AM - Buhainat: HAULATU66

Aalimah ta yi sallama a shigifar kakansu. Daga shi sai Daddy 2 ta tarar a dakin, babu kowa. Ta samu gefen Malam ta zauna. Malam ya dube ta cikin kulawa, ya ce,
“Uwata me ya faru ne?â€
Ta saci kallon Daddy 2 wanda kallon fuskarsa kawai ta yi ta ji ya ba ta tausayi, da alama cikin damuwa mai tsanani yake. Ta ce, “Malam wai Daddy ne ya ce zai min aureâ€.
Yayi murmushi.
“Ke kuma ba kya so ko?â€
Ta ce, “Malam ba zan iya mantawa da Aboulkhair ba, balle in hada rayuwa da wani a bayansa, kullum ji nake a jikina zai dawo. Idan ya dawo ya same ni da aure, na ci amanarsaâ€.
Murmushi Malam ya yi kafin ya ce, “Ko da a ce MU’AZZAM ki ka aura ba za ki manta da shi ba?â€
Idanunta suka kara girma, at the same time suka kankance suka firfito waje, cikin sanyin murya tace.
“Malam, wanne Mu’azzam din?â€
“Mu’azzam Raazee Yayan Aboulkhairâ€.
Wannan karon Daddynta ne ya ba ta amsa, with every affirmation a cikin muryarsa.

Sai Aalimah ta gurfana a gaban mahaifinta a kan gwiwoyinta. Rokonsa ta ke idan wasa yake yi tana mai rokonsa da girman Allah da darajar zatinsa da ya bari, Mu’azzam tamkar uba yake a gare su daga ita har Aboulkhair. Gara ya aura mata mazan duniya bakidaya ta amince, a kan ya aikata wannan babban zunubin a gare ta.
Kamata ya yi ya tasar da ita daga durkuson da ta yi a gabansa kamar mai neman gafara. Idanunsa sun kada sun yi jajir da tausayin ta. Sai dai ko sama da kasa za ta hade ba ya jin akwai abin da zai sa shi fasa hada wannan aure, muddin yana raye ita ma Aalimah tana numfashi.
Ya ce, “Ki nutsu Aalimah ki fuskance ni, Mu’azzam shi na so tun farko ki aura Allah bai cika min wannan burin ba. Idan har da gaske kina kaunar Aboulkhair ba abin da za ki yi ki nuna masa wannan kaunar a lokacin da kasa ta rufe masa ido, banda tallafar rayuwar Mu’azzam. Kin sani Aboulkhair ba shi da wani buri da ya wuce Mu’azzam da lafiyarsa. Aalimah ba kya tausayin Yaya Ishaq? Mutumin da ya dauke ki babu bambanci da ‘ya’yan cikinsa ya karrama rayuwarki? Kina sane da cewa ba shi da buri a yanzu da ya wuce lafiyar Mu’azzam da cikar rayuwarsa. Ba za ki kasance mai rama alheri da sadaukarwa ba?â€
Aalimah cikin gunjin kuka ta ce, “Daddy, bana gudun Mu’azzam don rashin lafiyarsa. Ko kadan. Ina gudun aurensa ne kasancewar sa wanda ya fi kowa kusanci da Aboulkhair, ina matukar ganin girmansa, aurensa shi ne babban cin amanar da zan yi wa Aboulkhair a lokacin da babu shi…â€.
Wannan karon malam ne ya tare ta, “Uwata, shi ne babban farin cikin da za ki sanya shi. Shi ne babban gatan da za ki yi masa. Shi ne kauna ta hakika da za ki nuna masa. Hakkin ki ne mu ba ki dama wannan karon ki zabi mijin aure, shi ya sa har muka zaunar da ke a nan muna neman yardar ki da amincewar ki, ba don haka ba da ba za ma ki san an yi ba sai bayan an yi.
Ni na san uwata mai biyayya ce ga umarnin mu, mai farin ciki da farin cikin iyayenta. Kin zauna da Mu’azzam ko da ba gida daya ba a kalla za ki iya bada shaida a kan WANE NE SHI? Kuma kin ga yadda dan uwansa ke kula da shi, akalla muna da kyakkyawan zaton za ki iya taimakawa rayuwarsa a matsayinku na shakikan juna, ku taru ku rufa wa juna asiriâ€.
Aalimah ta rasa abin cewa, ta rasa hujjar kare kanta wajen Daddy da Malam, ban da ta zuba musu ido, sun riga sunyi nisa akan kudirinsu, kome zata ce bazasu gane ba, bazasu saurareta ba, tana mai jin abin da suke fadi kamar almara a cikin kanta. Tana mai kallon fuskokinsu na wulgawa kamar a majigi, tana ganin wasu abubuwa masu kama da taurari cikin idanunta suna ratsa fuskokinsu cikin idonta. Daga haka ba ta kara gane me suke cewa ba, kuma ba ta kara samun kalmar furta musu ba.
******
Chapter 70 · 0% Book details