← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 91

Sashe 46

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ne da yawa, amma a yalwace yake. Komai fari tas a cikin falon, hatta curtains da kujerun leather duka farare ne kal-kal! Tana nan tana baza ido ta jiyo takun Aboulkhair yana saukowa, amma ba ta ji taku na bayan nasa ba, duk da cewa su biyu suke saukowa. His own steps ba ya making sound sabida babu takalmi a kafarsa. Kuma ma dai hatta tafiyarsu ta bambanta, taku yake kamar basarake. Kallo daya ta yi masa ta ji ba za ta iya ci gaba ba, kada idanunta su samu rauni, ko nakasu. Domin kwarai kwarjininsa da cikar zatinsa ya dusashe ‘yan idanunta. Ga wata irin kamala da charismatic personality. Da ganinsa ka ga ruwa biyu (Nigeria da Niger). Cikin iyayensa bai dauko mutum daya ba, mixed appearances dinsu ya debo sabanin Aboulkhair fari tas! Kalar abzinawa masu tarin sumar kai, Ishaq Raazee bakidaya. Shi Mu’azzam kansa babu tarin suma, wani irin saisaye ne mai aji. Kananan kaya ne a jikinsa (farfetch) army green colour daga T/shirt har wandonta. Wani irin agogo daure a damtsen hannunsa mara walkiya, sai daukar hankali samfurin ‘Blooming Dale’s’ ruwan azurfa. Ya fi Aboulkhair tsayi, ya fi shi kauri. Alamu duk sun gama nuna mata he is living in an affluent life of the western world wanda a duniyarta ba ta san da irin rayuwarshi ba, ko mutane masu irin personality dinsa. Duka wannan observations Aalimah ta yi su ne a kallon farko da ta yi masa, daga haka ba ta kara ba. Fargaba ma ta shiga ta yadda za ta bai wa wannan handsome GENTLE din tuwo, Aboulkhair ya fi ta gaskiya. Ji ta yi duk ta muzanta, ta soma Allah-Allah su bar gidan don ko a fuskarsa ba ta hango wani maraba da zuwanta gidansa ba. Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta. Tana jin maganganun da suke yi shi da Aboulkhair sai Aboulkhair ya fadi biyar bai ba shi amsar biyu ba, kamar mai ciwon baki. A karshe ta ji zaman mutum a gefe ya ja kujera karama ya zauna yana fuskantarta. Kamar daga sama ta ji yana mata sannu da zuwa cikin harshen Hausa, sannan ya tambaye ta ya ya bakunta, kuma ya ta samu kanta a Las Vegas? Zamowa ta yi daga kujera tana amsawa, sannan ta gaishe shi cikin nutsuwa. Ya ce, “Koma kujera ki zauna, ni ba surukinki ba ne, dan uwanki ne. Ya ya Kawu Mansour, Mama Asi da Aboubacar?†Mamaki kamar ya zauta Aalimah, sai kuma ta tuna su ma mutanen gidan nasu ai sun sanshi, har mamaki suke da ta ce ita ba ta sanshi ba. Kafin ta samu zarafin amsawa ya mike ya bi wata kofa. Sai ga shi da lemon Sangria Mocktail cikin kofin gilashi biyu, ya mika mata daya ya zauna da daya a hannunsa yana sha a hankali. Aboulkhair ya yi narai-narai da fuska, wai shi ba a ba shi ba. Murmushi ya yi, ya ce, “Na dade da yayeka, ka bar ni in yi wa bakuwata barka da zuwaâ€. Ita dai har zuwa lokacin duk da ya saki fuska yana kuma kulata ta kasa sakin jikinta. Ta rike kofin mai cike da kananan fruits kamar fruit-salad cikin ruwan grape juice, sanyinsa na ta ratsa tsokar hannunta. Sosai ta ke so ta sha ko don ta ji ya dandanonsa yake, amma ba za ta iya sha a gabansa ba. Ya tambaye ta abin da ta karanta, ta gaya masa. Sai ya juya ya dubi Aboulkhair yana masa hararar wasa, “Da ma kun zo garina ne don ku cika min gida da magani ko?†Dariya Aboulkhair ya yi, itama tayi dan murushin abinda yace din, ya ce, “Da na rubuta zan bata ta hado in kawo. In har ita ma za ka nema mata ko cikin pharmacies din asibitinmu neâ€. Ya ce, “Wannan abu mai sauki? Ka ba wa Dr. Kennieth takardunta. Aalimah could you work at Las Vegas?†Murmushi ta yi, ta ce, “In ya amince(tana nufin Aboulkhair)â€. Ya ce, “Karewar amincewa, ba ni na ce a nema miki ba? Youonly have to eradicate all kind of smiles from your lips, daga sanda kika fita har ki dawo aikinâ€. Murmushi Mu’azzam ya yi kamar bai ji ba, ya soma duba agogo (kada su shiga lokacinsa). Aboulkhair ya janyo basket din nan gabansa, “Girkin dare ne amarya ta yi maka na neman albarka, ta ce in ka kasa ci in mare ta sau ukuâ€. Sunkuyawa ya yi ya bude yana murmushi, ya ce, “To zuba min in gani, ko Allah zai sa a yi marin amarya a gabanaâ€. Murmushi ta yi ta nade mayafi ta hau serving din, amma maimakon ta fara zuba masa, sai ta fara zuba wa mijinta, tukunna ta zuba masa. Mu’azzam ya lura da abin da ta yi, ya kuma yaba da hankalinta a ransa, “Miji first! Before anybodyelseâ€. “Tastes goodâ€. In ji Mu’azzam. Daga haka bai kara magana ba sai empty plate ya ajiye wa Aboulkhair a kan cinyarsa, “Ina ya kamata a mara kenan?†Dariyar jin dadi Aboulkhair ke yi. Ya saci kallon Aalimah ita ma murmushin ta ke yi. Ya ce, “Ban taba ganinka kana cin tuwo ba ne shi ya sa na yi mata musu. Ko Mummy ce ta yi sai in ga ta maka wani girkin dabanâ€. Mu’azzam ya mike yana fadin, “Na gode da ziyara da girki mai dadi amarya Aalimah. Indeed bana son tuwo, amma na ji dadin naki, saboda kin yi shi da nutsuwa ga dukkan alamu. Kamar yadda na fahimci ke ma kanki mai nutsuwa ce. I wish you the best. Have a good stay in Vegasâ€. Ya ciro biro ya yi rubutu a ‘yar takarda ya ajiye mata tare da wani dan kati, ya juya yana ce da Aboulkhair, “Na sallame ku, zan sha magani in kwanta gobe sammako zan yi zuwa seminar din nan da na gaya makaâ€. Daga haka ya bi matattakala ya haye upstairs da tafiyarsa mai nutsuwa, wadda babu garaje a cikinta. 6/29/21, 9:00 AM - Buhainat: BEHIND
Chapter 46 · 0% Book details