Sashe 45
Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****** Kwanaki uku da suka biyo baya wata irin rayuwa ce mai cike da soyayyah, Aboulkhair da Aalimah ke gudanarwa a gidansu. Su yi girki tare, su ci abinci tare, su yi wasa su yi dariya, su sanya juna nishadi. Tarairayarta yake da jinya har ta warware. In ba wani abu da ya kama dole zai sayo musu ba, ba ya fita. Sallah kuwa jam’inta suke su biyu sau biyar a rana. Nata dakin sun kulle shi da nashi suke amfani. Sun yi wata irin shakuwa mai ban mamaki fiye da shekaru biyar din baya. Yau suna zaune a dan karamin dining dinsu mai kujeru biyu kacal, wanda ke cikin kitchen dinsu suna cin abincin rana. Wayarsa ta yi kara, ya kalle ta da gefen ido, bai yi niyyar amsawa ba don a kwanakin nan ma amsa waya wahala yake masa, ta fi zama a kashe a yawancin lokuta kafin ya karasa cinye kwanakin hutunsa da suka rage. Amma ganin mai kiran da sauri ya dauka. Aalimah na ganin yadda ya tattara bakidaya hankalinsa a kan wayar, ya kuma mike tsaye. Hatta muryarsa canzawa ta yi, magana yake with utmost respect. “Ban san ka shigo gari ba, da tuni na zo na kwance jaka. A yi min izini na kawo Aalimah ta kwashi gaisuwa wajen babban Yaya, ba ta taba ganinka baâ€. Ba ta ji amsar da Mu’azzam din ya bayar ba, ta dai ga Aboulkhair ya kara nutsuwa yana rokonsa ya barsu su zo. Har yana fadin, ya fadi iya mintunan da zai iya ba su da bakinsa in suka haura gobe kada ya barsu su sake zuwa. Takaici ya kashe Aalimah daga zaune, sarkin ina ne wannan? Dole ne zuwa wajen nasa? Me yake rabawa da sai an roke shi za a je inda yake? Ba ta gama wannan tunanin ba ta ga Aboulkhair ya cillar da wayar tasa gefe ya rarume ta ya mikar. Cike da zumudi ya ce, “kiyi girki, wanda ya fi kowanne dadi mu kai wa Mu’azzam, ki hanzarta mintuna talatin kawai ya ba mu in mun je, yana da wata seminar gobe da (Concophillips oil Gass) yana shiri, kada ki bata lokaciâ€. Aalimah ta rausayar da kai, ta ce, “Me zan dafa? Ban san me yake so ba?†Ya koma ya zauna ya hau lissafi. “Girkin da ya fi kowanne dadi with aroma and maggiâ€. Ba ta san sanda ta saki dariya ba, ta tabbata Aboulkhair yana matukar son Yayansa, ba ta taba ganin ya dau lamarin wani da muhimmanci irin haka ba. “Kowanne girki ai dole a sa masa aroma da maggi, I mean irin abincin da yake soâ€. “Tashin hankaliâ€. In ji Aboulkhair, “Ai wato menu ake ba shi daga WALDORF ASTORIA (mafi shaharar restaurant a Las Vegas) ya zabi abin da yake so, ni kaina ban sani ba. amma ke me ki ka ga ya dace?†Aalimah kamar ta yi kuka, a ranta ta ce, ‘Haka kawai ina zaman-zamana za ka taro min aradu da ka, wannan basaraken naka ai sai kaiâ€. A fili kuma ta ce, “Burabisko da miyar tausheâ€. Ya zaro ido, ya ce, “You are not serious. Gero zaki dafa masa ya shaqe shi? Tukunna ma kin san wai wajen wa nake magana ne?†“Ka ce sunansa Mu’azzamâ€. Ya ce, “Ba ki san Yayanmu ba ne?†Ganin kamar ya soma harzuka ta shiga nutsuwarta sosai, ita haka kawai ranta bai son Mu’azzam din nan tun daga lokacin da ta fahimci irin life style dinsa, da maganganun da kannensa ke yi a kansa na irin rashin kirkinsa da ginshirarsa, sannan shekaru biyar ta kwashe a gidan Ishaq Raazee daidai da rana daya ba ta taba ganin sawun wannan Mu’azzam din a gidan ba, da sunan ya zo gaida iyayensa. Sai dai kullum ta ji Mummy a hanyar zuwa gidansa, what a life! Sannan yanzu ta kara fahimtar wani abu, Aboulkhair ba ya hada lamarin Mu’azzam da na kowa, ita kanta ba a bakin komai ta ke ba in dai a kan Mu’azzam ne. She has to be careful don tsira da mutuncinta a idon mijinta-mai-kaunarta. Da kyakkyawan sauti ta ce, “Ina ganin mu yi masa tuwo. Ka fahimce ni Mon Amour (my love), ba abin da ya saba ci ya kamata mu kai masa ba, ba za mu burge shi ba. African cuisine shi ya kamata. Idan Mu’azzam ya kasa cin tuwo na ka mare ni sau ukuâ€. Bai san sanda ya yi murmushi ba, amma kwarai ta bata masa rai da farko, zancen Mu’azzam fa yake mata, amma ta maida shi kamar wani marainin wayonta. Kodayake ya mata uzuri, ba ta sanshi ba, ba ta taba ganinsa ba, ba ta san komai a kanshi ba. Wanka ya shiga kafin ta gama, ita kuma ta dukufa sarrafa kyakkyawan farin tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa da ta markadata da blander. Ta yi masa kyakkyawan tuki, ta kwashe shi kananan malmala a farar leda ta jera a food warmer madaidaiciya. Kafin ta saka kaza a miyar sai da ta soya ta, sannan ta zuba su a miyar suka dahu tare. Kafin ta gama zobon da ta jika da ruwan zafi ya jiku, ta tace ta yi masa hadin danyar abarba da danyar ginger (citta), ta sa sukari da pineapple flavour. Ta juye a cooler irin ta zuwa picnick din nan. Ta jera komai a kwandon abinci har farantai da cokullan da za su yi amfani da su ta dauka. Sannan ta fada wanka. Dukkansu sun yi tsaf cikin Hausa Attire, sai kamshi suke yi. Suna tafe a hanya Aboulkhair ya kunna musu kira’ar Abdurrahman Sudaith cikin suratul Ma’idah, wadda ta kara sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a zukatansu. Aalimah cikin ranta cewa ta ke yi, yau dai za ta ga Mu’azzam din nan, ta ga shin me ya taka a rayuwarsa? Wane ne shi? Wane irin mutum ne shi? Zaman me yake yi shi kadai a gida babu iyali? Ba mamaki ma matan banza yake kai wa gidan, wanda ko gaida iyayensa ba ya yi, ba ta zaton masa wata rayuwa mai albarka. Sosai ta ke jin rashin kaunarsa a zuciyarta. Ta tuno kannensa da yadda suka tsane shi, da kuma yadda kullum zancensa ya ratso cikin hirarrakinsu suke kiransa ANNOYING son of Mum. Kalmar da ke da tarin ma’anoni masu yawa daidai da fahimtarsu. A saninta kalmar annoying na nufin irritating, infuriating, tiresome kuma troublesome. Da ta tattara ma’anonin wadannan kalmomi, hadida tattara su wuri guda in a nutshell suna nufin Yayansu Mu’azzam mai yawan fusata ne, mai tayar musu da hankali (ta hanyar yi musu fada), mai tilasta su su yi abu ko da ba sa so, mai yawan damuwa a karan-kansa, kuma mai tarin matsalolin rayuwa. Idan ta jimlace wannan fassara a ma’auni na hankali da tunani da zurfin iliminta, za ta iya fahimtar lamarin ba komai ba ne; is simply a subject matter that others around him are not understanding what he is going through. Ita ce makalar da ke tattare da rayuwar Yayansu Mu’azzam, har ta kai ta kawo cewa, he lack positive emotions like happiness and laughter… wanda kannensa suka fassara shi yadda suka ga dama, ba tare da bin ba’asin dalilan da suka mayar da rayuwar tasa hakan ba, ko abin da ya janyo masa wannan rayuwar da yake ciki. everything has CAUSE! Wato komai yana da tushe. Haka kawai ta ji jikinta ya yi sanyi, zuciyarta ta dugunzumarta da son sanin WANE NE MU’AZZAM??? Za ta bi kwakkwafi ta ji mene ne cikin rayuwarshi haka da ya maida shi hakan ta hanyar mijinta, mafi kusanci da shi ko da hakan na nufin canzawarta daga mai harhada magunguna zuwa ethnographer ne. Shebecame extremely intrigued. Ta yi nisa cikin wasikar jakinta ta ji yatsun Aboulkhair saman fuskarta yana shafa kuncinta a hankali, ashe ya jima da kashe motar a kofar gidan Mu’azzam. “Mrs. Thinker tunanin me ki ke yi? Ga mu gidan Mr. Mu’azzam Raazi, taho mu jeâ€. Sai kuma ya dakata alamar ya yi mantuwa, “In mun shiga kada ki zauna a kusa da ni, kunyarsa nake ji sosai, har fiye da Daddy. Ko hannunki ba zan kama baâ€. Dariya ta kama Aalimah matuka, da ma akwai wanda Aboulkhair ke jin kunya a duniya? Ta ga dai a gaban Mummy ya ce da Gumsu ta dawo dakinsa su kwana, ita ya bari da ji masa kunyar. Girgiza kai ta yi, ta murguda baki, ta ce, “In ka ce masa ma ba sona ka ke ba sadaka ta aka ba ka, duk daidai neâ€. Hannu biyu ya dora a ka yana leken idanunta, amma ta ki yarda ta kalle shi, ya ce, “Ya fi ki sanin yadda nake son naki, da wahalar da na sha kafin in same ki. Ba don shi ba da ba’a kawo yau ba, da tuni na watsar da karatu na rungumi Aalimah a cikin gida. Da ma karatun don shi nake yinsa, kuma with his support and encouragement, yau na tsira da ku bakidaya (ita da karatun)â€. Murmushi ta yi tana kici-kicin fiddo kwandon abinci daga bayan motar. Ya karbe ta yana fadin, “Idan ina kusa, ko Babyn mu ba za ki dauka ba balle wasu kayaâ€. Wata harara ta sake masa, “Wai baby, har yaushe akai daren da garin zai waye?†Ta fada a karkashin zuciyarta, tana dubansa ta kasan ido cike da so da kauna. Aalimah ta daga ido a hankali tana kallon kyakkyawan gidan da aka kira mallakin Mu’azzam Raazee ta hanyar rubutawa a jikin kofar shiga gidan, wanda ke cikin kebantacciyar unguwar HillsboroughEstate, mai hawan sama da kasa. Irin gidajen da suka kira ‘Fairfield Terrace’ wadanda sai dai mallaka ba dai haya ba (rent). Wani mutum yana goge motoci da ya juyo, sai ta gane shi, shi ne direban da ya debo su daga airport ya kuma kai su Mummy gida. Da fara’a ya gaishe su, ya karbi kwandon hannun Aboulkhair ya bi bayansu. A falon da suka fara tararwa Aboulkhair ya ce ta zauna ya hau sama ya kira shi. Da gudu-gudunsa yake hade steps biyu-uku yana kiran, “Mu’azâ€. Har ta daina ganinsa. Ta shiga wurga ido tana kallon wani irin English parlour da ko a talabijin ba ta taba ganin mai tsari da kayatuwarsa ba. Ta fahimci gidan ba mai girma ba