← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 91

Sashe 36

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

******
Bayan fitarta da kamo Yesmin da Khaleesat ta yi, Daddy dakin da Gumsu ta ke ya shiga. Kiranta ya yi suka fito tare. ‘Ya’yan na nan zaune yadda suke tun shigowarsu. Cikin yanayi na zugum-zugum sai Yesmin da ke ta kukan an hana ta bin Mummy.
Zama ya yi a kujerar da ke fuskantarsu, Gumsu za ta zauna kusa da Aalimah ya ce, ta dawo kusa da shi ta zauna. A nutse ta bi umarninsa cikin tsananin ladabi. Ya dube su bakidaya, ya ce, “Ga Antinku Moiram na taho da ita. Ina ganin hakan zai fi min sauki a kan na baro ta a can na dinga zarya. Inyaso duk karshen shekara sai mu je hutu. Basma, Aalimah da Khaleesat dukkanku na san masu hankali ne, kuma masu adalci a tsakanin iyayenku. Ban auro Gumsu-Moiram don bana son mahaifiyarku ba, sai don cika sunnar manzo sallallahu alaihi wasallam, da biyayya ga iyayena. Moiram uwarku ce, kuma gaba ta ke da ku, don haka na hore ku da da’a da biyayya a gare ta. Ku bi ta yadda za ku bi mahaifiyarku. Ke kuma Moiram ga amanar ‘ya’yana nan ki zauna da su yadda za ki zauna da wadanda ki ka haifa. Wanda ya yi miki ba daidai ba, ki sanar da ni, balle kuma dai na shaide su dukkansu masu kaunar Daddy ne ba za su taba kin abin da ya kawo ya ce nashi ne ba. Haka ne ko ba haka ne ba?†Ya maida maganar cikin sigar tambaya, ta wani bangaren lallashi.
Basma ce ta fara amsawa da, “Haka ne Daddy. Aunty Gumsu muna miki barka da zuwa cikin family dinmu. Insha Allahu za ki same mu yadda Daddy ya shaide muâ€.
Khaleesat ta dan ja fasali kafin ta ce, “Welcome Aunty Moiramâ€.
Kallo daya za ka yi mata ka san cewa tafiyar mahaifiyarta ta taba ranta. Gab ta ke da fashewa da kuka tana dai daurewa ne.
Aalimah Daddy yake kallo, yana so ita ma ta yi magana. Da farko ba ta yi niyyar cewa komai ba don a ganinta wannan abu ne da ya shafe su su kadai, ita ai ba ‘yar gidan ba ce. Amma ganin kowa ita yake kallo da saurare, sai ta ce,
“Sannu da zuwa Aunty Gumsu. I’m Aalimahâ€.
Daga nan kowacce ta fadi sunanta. Yesmin ma ta share hawaye jin kowa na fadin suna, ta ce, “Aunty I’m Yesmin, Mummy’s loveâ€.
Sosai ta ba wa kowa dariya. Gumsu ta matso ta janyo ta jikinta ta dora ta a cinyarta, cikin faransanci ta ce, “Ni kuma sunana Aunty Gumsu. Yesmin’s Auntâ€.
Yesmin ta girgiza kai cikin rashin yarda, “I’ve my Aunty, her name is Aunty Aalimahâ€. Ta fada tana nuna mata Aalimah.
Daddy ya ce, “Sun zama su biyu Yesmin, Aunty Aalimah da Aunty Gumsuâ€.
Cikin hikima Gumsu ke jansu da hira cike da kulawa da nuna kauna. Ba ta iya Hausa ba sai faransanci, abzinanci da turanci, don haka da turancin kadai suke magana da ita. Suna jin faransancin amma sama-sama amma. Tun suna dan jan jiki har suka ware musamman da ta ce kowacce ta je ta canza kaya ta zo ta daura apron su shiga kitchen tare. Abin da kowacce ta ke so shi za ta dafa mata, daga yau sun daina cin abincin mai aiki sai nata, tsakaninsu da mai aiki yanzu share-share da wanke-wanke ne kadai. She has a degree in Pastry-Art (tana da digiri kan girke-girke) kuma a gidansu za ta bude ofis dinta (tana nufin a kicin dinsu). Duk kinsu da shiga kicin kasa musa mata suka yi.
Aalimah ta ji dadin hakan sosai, don ita duk yadda za ta yi da su ba sa yarda. A ganinta da a gida Nigeria suke, duk sun isa aure. In aka aurar da su me za su tabuka a gidan miji?
******
Washegari suka koma makaranta dukkansu, Aunty Moiram kawai ake bari a gida, sai ko Easther in ta zo aiki, da ta gama ta ke tafiya. Abulkhair tunda ya kai Mummy gidan Mu’azzam bai dawo ba. A kwanaki uku da suka biyo baya sabo ne mai tsanani ya shiga tsakaninsu da Auntynsu Gumsu, wadda ke kula da komai nasu tsakani da Allah. Shi kansa Daddy yanzu da wuri yake dawowa gida don ya san in ya dawo zai tadda mai jiransa, abinci lafiyayye sai wanda ya zaba. Tun Gumsu na jin kunyar hawa upstairs turakan Daddy sabida idanun su Basma, har ta gaji ta zubar, inda ta fahimci yaran daban suke da irin wadanda ta sani a Nijar, wadannan masu budadden ido ne, kowa rayuwar ‘yanci yake yi babu takura. Sannan ginin benen ya fi na kasan girma da fadi sosai, a can dakin Mummy Zulaiha yake, na Daddyn da na su Basma. Inda aka batan karami ne, Mu’az ne ya zauna a dakin farkon dawowarsu gidan, kafin ya tafi jami’a a Las Vegas. Daddy ya ce zai kama mata apartment na haya a nan kusa da su, amma ta ce in dai hakan ba zai zama matsala ga Maman su Basma ba ita ta fi so ta zauna tare da su, dakin ya ishe ta, don hade yake da bayan gida, ba ta iya rayuwar kadaici ba, sai dai in zai ba ta yaran bakidaya. Shi ma zai fi son hakan, sai dai ya san Mummy ba za ta taba amincewa da kowanne a ciki ba (ba ta ‘ya’yanta ko zama tare da ita).
Ranar kwana na hudu ya yi musu sallama, ya ce zai bi bayan Mamansu. Abulkhair ne ya yi masa waya kan ya daure ya zo, don sun kasa tankwara ta shi da Mu’azzam, tana shirin barin America.
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: HARUNA TANKO

@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@@

Al’amari in dai tsakanin Zulaiha da Ishaq Raazee ne, to dan Adam ka koma gefe kawai ka yi kallo. Ba karamar soyayya ce a tsakaninsu ba, wadda aka gina tun tali-talin kuruciya.
Kwanan Daddy biyu a gidan Mu’az asabar da lahadi ya ya aka yi, ya ya aka yi? Ko su Abulkhair ba su sani ba, sai ga su sun dawo tare su ukun. Shi dai Abulkhair dan kallo ya zama in ya tuna duk irin lallashin duniya da suka kwana uku suna yi wa Mummyn shi da Yayansa Mu’azzam, kan ta yi hakuri ta koma dakinta, ta kau da ido daga auren Daddy. Amma ta ki sauraronsu ta bude wa Mu’azzam wuta ya nema mata visa zuwa kasar da Ishaq ba zai kara sanin tana (existing) ba. Dalilin Abulkhair na kiran Daddyn kenan, wanda da farko ya yi niyyar ba ta sarari har sai ta gaji da zaman gidan Mu’azzam din ta dawo don kanta.
Amma darajar ‘ya’yanta da tunanin da ya yi, kada su ga ya wulakanta musu uwa don ya yi aure ya sa ya sauya niyya ya je din. Shi kadai ya san irin lallashin da ya yi mata har ta sauko. Abin har dariya yake bai wa Abulkhair, yana tuki yana jinsu suna ta muhawara kan ita ba ta yarda Gumsu ta zauna mata a gida ba, shi kuma yana nuna mata tarin alfanun da zaman nata tare da su ke da shi, in kuma ba ta amince ba, to ta ba ta yaran bakidaya tunda ita da ma ba wani zaman gidan ta ke yi ba. Nan ma ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta yarda ba. Gumsu ta koma Nijar kawai ta yarda duk shekara ya je. Shi kuma ya ce, wannan rashin adalci ne.
Ya gaji da lallashinta, zai yi abin da ya ga dama. Zai kama wa Gumsu gida kusa da su, amma zai raba yaran biyu ya ba ta rabi, tunda ita ba ta san abin da zai taimake ta ba sabida kishin banza.
Ba tarbiyya ba ce iyaye na magana ‘ya’ya su sa musu baki ba tare da sun yi umarni a gare su da hakan ba, amma da ya ba wa Mummynsu shawarar ta kyale Gumsu ta zauna tare da su, amfani ne mai yawa a gare ta.
Chapter 36 · 0% Book details