← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 91

Sashe 34

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A haka satin ya kare musu, tana lissafe da kwanakin. Ranar juma’a wadda ta kama ranar zuwan Abulkhair kasa zaune ta yi ta kasa tsaye. Kwalliya ta yi ta har sau uku tana canzawa. Ba ta da lecture ranar, don haka ta makale a kicin da sunan taya Easther aiki. Nan kuwa masoyinta ta ke son yi wa girkin da zai yi farin ciki da shi. Waina (massa) ta soya masa wadda ta jika shinkafar tun daren jiya, ta markada da safe. Sai miyar ganye wadda ta ji tsokar naman talo-talo (Turkey). Ta dade da sanin Abulkhair na son chips wato soyayyan dankalin Turawa, ta zauna ta fere ta yi masa kyakkyawar suya. Mummy na office, Basma na school, Khaleesat da Yesmin suna Tahfiz dinsu. Gidan daga ita sai Easther, ta yi light make up kamar yadda ta saba, sannan ta zabo wani lallausan swiss lacelemon green mai stones da aka yi wa dinkin gown ta sanya.
Ita da Easther suna shirya abincin a diningaka danna kararrawar kofar gidan. Cewa Easther ta yi ta je ta bude, ita kuma da gaggawa ta gudu upstairs dakinsu. Ba ta san me ya sa ba, kunyarsa ta ke ji yau, kunya sosai, it has been long…har wata uku da rabi without them seeing each other (ba tareda sun ga juna ba)Ba ta san da fuskar da za ta kalle shi ba, ko wace tarba za ta yi masa. Fuskarta ta sanya cikin tafukanta ta zauna a bakin luntsumemen gadonsu.
“Yaa Allah! Grant me the courageâ€. Shi ne abin da ta furta a hankali.
Ya tambayi Easther da ta shigo masa da jakarsa, “Duk ina mutanen gidan?â€
Ta ce da shi babu kowa sai Aalimah. Cikin mamaki ya ce, “Sun dawo? Yaushe? Tana ina?â€
Bai kuma tsaya ta ba shi amsar ko guda daya ba, ya shiga hada steps biyu-uku, yana hawa sama.
Sai da ya murdo kofar dakin nasu ya shigo ya yi daidai da dago kanta da ta yi ta dubi saitin kofar. Kirjinta na harbawa.
Yana nan yadda yake, handsome Abulkhair. Well dressed in a Nordstromshirt and jeans trouser, masu kalar baki da fari, mai yawan gargasa a jiki, da sumar kai irin na buzayen usul. Ko bakar jakar da yake goye da ita a bayansa bai sauke ba. Sai dai kuma ya yi rama sosai. Kallo daya za ka yi masa ka san cewa ya rame din, duk da physique chest din yana nan ba abin da ya girgiza shi.
Idanunsa suka sauka cikin nata, sun dade suna kallon juna kowannensu yana sakin murmushi kafin ya saki jakar da ke bayansa kasa, ya bude mata hannayensa. Girgiza masa kai ta shiga yi alamar a’ah, ba ta san sanda ya iso gabanta ba har inda ta ke zaune ya zube gwiwoyinsa ya zauna a gabanta, ya zuba mata ido ba ya ko kiftawa. Daga bisani lumshe idanu kowannensu ya yi cikin jin wata irin nutsuwa na sauka a zuciya da gangar jikinsa.
“Kallon ya yi yawa. Babu aure a tsakaninkuâ€. Tunanin da ya shiga kan Aalimah kenan, ta mike tsaye da sauri. Shi ma mikewar ya yi ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallonta a tsanake, ta kara kyau ta cicciko sosai, wanda ke nuna ita kam cikin kwanciyar hankalinta ta ke. Duk wahalar nan da ya yi tsayin sati hudu bai ji ko da muryarta ba, ita ba haka ba ne a tare da ita ba.
Murmushi Aalimah ta yi, “Monsieur…â€
“... Don’t dare call me Monsieur againâ€.Yakatseta. “Na ga abubuwa sabanin yadda na zace su, ni kadai na yi kewarki. Ni kadai na damu da ke…!â€
Ya karasa maganar in subdued wato cikin muryar da ke nuna how dissappointed he was. Tare da juya mata baya.
Takowa ta yi a hankali har ta zo dab da shi, sannan ta tsaya. Cikin sanyin murya ta ce,
“Ba haka ba ne. tunda muka je ban…â€
“...Ba ki sake tunawa da ni ba, balle halin da rashin ji daga gare ki zai sanya ni. Quite four weeksâ€. Ya fada yana daga yatsun hannunsa guda hudu, akwai fushi sosai cikin muryarsa.
“Daddy bai ba mu layi ba…â€. Ta fada cikin son kare zarginsa na cewa ba ta damu da shi ba.
“In ba ku da layi ba za ki iya siya ba? Ko ba za ki iya roaming naki layin ki yi amfani da shi ba a ko’ina? In duk hakan ba mai yiwuwa ba ce, ba za ki iya aron wayar wani ki kira ni ba?†Wannan karon da fada sosai yake magana.
Abin da Aalimah ta ki jini kenan, tuni idonta ya cicciko da kwallah.
Hakan ya sa Abulkhair sassauta fushinsa, ya juyo yana kallonta. Fahimtar hakan ya ba ta damar iya yin magana cikin kwantaccen sauti.
“Na ji Basma na fada wa Malam Razee cewa jarrabawa ka ke yi, kuma ka yarda da ni ko su Mamanmu ban kira ba har muka je muka dawo. The house is always full and very busy… Mun kuma yi tafiye-tafiye na garuruwa masu nisa cikin sahara inda babu network har mutum sai ya manta ma yana da waya, amma ba don na manta da kai ba, ko ba ka zuciyata. Ina dawowa na yi niyyar kiranka na tuna ba weekend ba ne kada in ha’inci Daddy. Ina tabbatar maka tunaninka na tafiya ne tare da bugun zuciyata. Babu inda zan shiga, ko wani yanayi da zan shiga da zai sa in manta ka ko na kasa tunaka…â€
Ba karamin sanyi kalamanta suka yi masa a zuciya ba. Ya manta duk wani bacin rai da ya samu kansa a ciki.
“Then give me a hug… don in tabbatar ba dadin baki kika yimin don in yarda da ke baâ€. Ya fada yana cin magani.
Dariya ta yi, ta ce, “Not nowâ€.
Kwafa ya yi ya fice daga dakin jin shigowar motar Mummy, yana ce da ita,

“Jira ba ya kisa. Da yana kisa da ban kawo yau ba!â€.
******
Chapter 34 · 0% Book details