← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 91

Sashe 79

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ta fara da shiga manhajar google inda ta binciki cikakken bayani a kan what the problem is all about? Sannan ta ke shiga library din Mu’azzam idan ya fita office, tana masa bincike, yana da manyan littattafai da suka shafi compulsive sexual disorder. Cikin manyan littattafan da ta debo daga library dinsa zuwa dakinta akwai ‘A Psychometric Investigation of the Hypersexual Disorder Screening Inventory’ (By J. Engel. 2019). ‘The Danger of Hypersexual Disorder’ (Dr. Martin Kafka), sai kuma ‘Compulsive Sexual Behaviour’ (A Review of the Literature) NCBI (By KL Derbyshire, 2015).

In takaice miki Aalimah sai da ta zama kamar wata ‘yar karamar Farfesa (Professor) a kan lalurar Mu’azzam sabida karatu da bincike, inda ta fahinci komai ta gane kan komai, ba tare da Mu’azzam din ya san tana yi ba.

Abu na gaba da ta ke son yi shi ne, ganawa da Dr. Nebrass Sheldon, ta kuma rasa hanyar yin hakan, tunda ba ta ganshi yana zuwa gidan su ba, ba ta kuma san a ina suke haduwa ba shi da Mu’azzam din. A lokacin da ta fahimci behaviour din, sai ta ga ba maraba da yadda Aboulkhair ya labarta mata. Ta dai samu faffadan bayani ne da cikakken ilmi akan lalurar.
Aalimah ta manta da wani abu wai shi ‘AURE’ dake tsakaninta da Mu’azzam, sai motive na ‘yan uwantaka. Sosai ta ke jin son ta tallafi rayuwar shi a haka, a hakan da yake da wannan lalurar, yadda Halima ta kasa. Ta ke ji a ranta cikin kowanne hali, za ta iya jimirin zama da Mu’azzam sabida biyayyar iyaye da kauna ta jini.
Ba abin da Uncle Ishaq bai yi mata a rayuwa ba! Ta tuno dauki ba dadin da ya dinga yi da matarsa a kanta. Ranar da ya gane Mummy ta hanata zuwa makaranta har na tsawon sati biyu ta maida ita boyi-boyin gidanta. In bata manta ba a ranar har hawaye yayi a kanta. Ya rungumeta a jikinsa kamar shi ya haife ta ya bata hakuri kamar zai ciro zuciyar sa ya bata don tayi hakuri ta cigaba da zama da su. Ya yi mata komai a rayuwa daga zamanta a gidansa har zuwa yau data auri Mu’azzam. Da yardar Allah jininsa bazai tozarta a hannunta ba.
Ta ji tana son shiga cikin rayuwar Mu’azzam ta kowanne bangare, ta fahimce shi yadda Aboulkhair ya fahimce shi, ta taimaka wa lafiyarsa yadda Aboulkhair ke taimakawa, ta kawo murmushi akan fatar bakinsa, ta kawo sauyin rayuwa mai tattare da nishadi. Duk da ba ta da shaidar ilimin da ya danganci wannan lalurar a yanzu, tana da fahimta a kai daidai gwargwado. Tana so ta shiga rayuwarsa ta ko ina yadda Aboulkhair ya shiga. Ta taimaka ta ko’ina, yadda Aboulkhair ke taimakawa. Har ake ganin murmushi a fatar bakinsa idan har suna tare, tana yiwa kanta kwadayin samun irin wannan matsayin a wurin Mu’azzam idan har zata samu dama! Tana rokon Allah Ubangiji ya dafa mata, ya agaza mata a bisa wannan niyya tata ta alkhairi akan mijinta.

******
Misalin karfe biyar na yamma Mu’azzam ya dawo office. Bai tsaya a ko’ina ba, kai tsaye cikin yanayin tafiyarsa mai kama data jinin sarauta ya soma taka matattakala ya haye upstairs don isa ga dakin barcinsa.
Bai dade da shiga ba ya ji Aalimah tana kwankwasawa. Wani abu da ba ta cika yi ba a tsayin watannin da suka kwashe tare, wato shigo masa daki in ba da kwakkwaran dalili ba, sai dai ta girka masa delicious ya ci ya more, in ba ta da lafiya ya kan kai ta asibiti, wanda sau biyu ne ma kawai tayi ciwon mara, ta fada masa abubuwan da ta ke bukata na cefane ya sa Harrison ya kawo mata. Ya lura bata komai yanzu sai karatu a library wanda bai san na menene ba. Ta dauki hankalinta da lokacinta kacokam ta mallakawa library, ko dakinta ya shiga zai ganta da glass tana karatu a ipad dinta, abinda ke gudana a tsakaninsu kenan a tsayin watannin su masu dan dama tare.
A tunaninsa tun wancan zuwan nata dakinsa da ya gaya mata maganar da ba ta taba zato ba, sanda tace ya maida ta makaranta ko aikin ta na pharmacy ba ta kara gigin zuwa dakin shi ba, don ta fahimci kamar ya gama karbar auren nasu, tana kuma tsoron abinda zai biyo bayan hakan, don haka tun daga lokacin ta janye jiki ta koma rufe jikinta a cikin hijabi yayin zirga-zirgar ta a gabansa, a falo ne ko a madafi. Duk wannan kwalliyar da ake cancadawa an daina. A wurin sa hakan ba karamin taimako ya zamo a gare shi ba, sabida ganin da yake yawan yi mata da dan kusancin da ya soma ginuwa a tsakaninsu ya soma birkita shi, ya gaya wa Nebrass yana so ya kara dose din magungunansa, kamar fa sun daina aiki a jikinsa kwanakin nan, don ya gaya masa yana kasa barci a yawancin lokuta da tunanin matar sa kuma ba ya son ya rabe ta. He is afraid of his new mood and the consequences.
Sun zauna sun yi magana heart-to-heart shi da likitocinsa, sun tabbatar masa zai iya rayuwar aure fa ya daina zancen a kara dose, amma ba lallai matar ta samu yadda ta ke so daga gare shi ba muddin yana cigaba da shan anti-androgens kamar yadda ya saba, bi ma’ana, ba lallai ya gamsar da ita a shimfida ba sabida karfin magungunan da suke bashi. Wadanda aikinsu shine kashe tasirin sex hormones a cikin jikinsa. Idan kuma aka dauke shansu shi ma matsala ne babba ga lafiyarsa, career dinsa da zaman lafiyarsa, don al’amarin zai zamo out of control. He will need nothing but sex. Mu’azzam ya gaya musu ya zabi ya zauna da ‘yar uwarsa a haka, cikin zabin da suka bayar duka babu mai sauki, babu wanda za’a ce gara shi. Tun dai ita ba ta nuna kosawa da zaman nasu a haka ba. Kuma da ma ba soyayya ce tsakaninsu ba.
Yana da tabbacin ta san lalurarsa, duk da ba su taba yin zance makamancin wannan da ita ba. Amma ai ta zauna da ABOULKHAIR.
Shi ya lura ma yanzu hankalinta ba ya kansa. Yana ga karance -karancen ta da rubuce-rubucen ta kamar mai rubutun thesis. A ganinsa zata fi kyau da zama malamar makaranta ba mai harhada magunguna ba.
Chapter 79 · 0% Book details