← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 91

Sashe 40

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ta dago suka hada ido, ba shiri ta dauke idonta. “Ya Allah!†Basma ta ce a hankali idonta a kasa, “Believe me, I don’t have (ka yarda da ni, ba ni da shi)â€. Aboubacar wani irin sanyi ya ji a ransa, amma nan take zuciyarsa ta shiga cautioning din shi, tana gaya masa ya danne ko ma mene ne yake cin ransa a kan Basma, ta fi karfinshi. An haife ta a U.S, ta girma a can, rayuwarta gaba daya tana can. Shi ba kowa ba ne face karamin ma’aikacin banki. Gidan da suke ciki a yanzu ma Yayanta ne ya saya musu. Ya aure ta ya kai ta ina? Ban da giggiwa irin ta zuciya? A sanyaye ya tashi ya bar falon. Basma ta bi shi da kallon mamaki da wata irin ragaita cikin kwayar idanunta. Sosai ya janye jikinsa da zama cikin gidan. A ganinsa ganinta da yake yi ne yake jaza masa komai. Basma kuma rashin ganinsa a cikin gidan sai ya sabbaba mata rashin walwala, duk ta zama wata irin sukuku. Har Aalimah ta soma zargin ko zaman gidansu ne ba ta so. Ko ta kasa jure irin tasu rayuwar? Ko kuma tunanin gida ne ya addabe ta? Da ta ishe ta da tambaya ta ce kome ta ke tuhumarta ta je ta yi ta tuhuma, ta yi abin da za ta yi, amma ta daina damunta da magana. Haushi ya kama Aalimah ta ce, “To ko in dawo da booking dinki jibi ki koma ni na taho daga baya?†Saura kadan ta mare ta, Aalimah na iya ganin hakan cikin idanunta. Dariya ta yi, ta ce, “To Basma na kasa gane miki. Kin zo da walwala kwana biyu kin koma min hakaâ€. A fusace Basma ta ce, “Lokacin da ki ka fara son Monsieur Aboulkhair, na takura miki da tambaya? Ba idanu na sa miki har na gano da kaina ba? Amma ni kin sa ni gaba kin sa min ido, har da sharri da kazafi. Wai na gaji da Najeriya. To in gajiyar na yi kunyarki nake ji da zan kasa gaya miki?†Aalimah ta kama baki tana kallonta, “Me ya kawo wannan tambayar?†“You want to know?†Basma ta fada a raunane. “Yes, I doâ€. Aalimah ta amsa. Sunkuyar da kai ta yi. “Yaya Aboubacar ya daina shigowa gidan nan saboda ba ya son ganinaâ€. Sai hawaye. Aalimah ta karasa kusa da ita sosai, tuni ta fahimci matsalar ‘yar uwarta. Hannayenta biyu ta kama, “Kina nufin damuwarki kenan?†Basma ta daga kai, “Mu kuma kaddararmu kenan, son ‘yan uwanmu?†Da sauri Basma ta cira kai ta dube ta, “Sonsa nake yi?†Murmushi Aalimah ta yi, “Ask yourself, not me. It’s your heart, not mine (tambayi kanki ba ni ba, zuciyarki ce ba tawa ba)â€. A hankali Basma ta zare hannayenta daga na Aalimah ta juya mata baya, “Idan dai yadda na damu da lamarinsa din nan da rashin ganinsa shi ne so, Aalimah ina son Yayanki…â€. Kalaman da suka shiga kunnen Mama kenan, ta juya ta fasa shigowa kada Basma ta gane ta ji zancenta. Aalimah ta dafa kafadunta, ta ce, “Basma!†Ta juyo ta dube ta cikin damuwa, “Idan har za ki iya zaman Nigeria auren Yaya Aboubacar ya fi komai sauki a gare ki. In ba za ki iya ba ne da matsala. Amma kada ki bari ya gane kin damu haka. Ki dawo cikin walwalarki, tun zuwanmu ina lura da shi shi ma ya damu da lamarinki. Ki bi shi da duk ta inda ya billo, insha Allahu tsakaninku alheri neâ€. Da sauri Basma ta rungume Aalimah. “Ni ko a jeji ne zan iya zama da shi Aal. Ba Nigeria ba, ko cikin bukka neâ€.
Chapter 40 · 0% Book details