Sashe 56
Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****** Da asubahin ranar Hassana da Hussaina suka ci gaba da ruda gidan da kuka, wanda suka kwana suna yi suna hutawa. Tun daren jiya sun ki karbar nono. Daga Basma har Aalimah babu wacce ta runtsa, suna fama da yaran nan saboda mama na can dakinta kwance babu lafiya, ta ce kuma takamaimai ba ta san inda ke mata ciwo ba, amma ko hannunta ta kasa motsawa balle ta zo ta taimaka musu. Daga kwance ta ce su dinga yin addu’a suna tofa musu. Basma gefe ta koma ta zuba tagumi, nonuwa sun mata suntum suna ta sukarta suna kuma diga, duk sun jika gaban rigarta. Aalimah na so ta yi sallar asubah don har masallacin kusa da su sun idar, yaran duka biyu suna hannunta tana jijjaga su, ta san in ta ajiye su Basma ko taba su ba za ta yi ba. ta zama dumm! Kamar wadda ta samu ciwon kurumta na lokaci mai tsawo. Aalimah ta ajiye daya ta goya daya. Rabonta da goyo tun haihuwar Aunty Gumsu. Tunda aka sallamo Basma Mama ke goya su, ta zura hijabi ta tada sallah zuciyarta na harbawa da kukan da yarinyar ke zubawa a bayanta. Ga wadda ta ajiye ita ma ba ta fasa ba. Kawai ita ma sai ta soma kukan tausayin Basma, ta san tsananin damuwa ne ya sa ta daina tabuka komai a kansu. Allah-Allah ta ke ta idar su tafi asibiti, tukin motar da Aboulkhair ya nace ya koya mata duk da ba ta so yau zai yi mata amfani. Da safe ma ita ta kai su asibiti aka duba yarinyar aka ce mura ce kawai, suka sayo magani suka dawo. Nan Mama ke gaya musu tafiyar su Daddy a mota sakamakon rashin jirgi. Duka addu’ar sauka lafiya suka yi musu, suka ci gaba da hidimar yaran. Tun bayan maghriba kuma suka bude makogaro suke zunduma kuka. Wanda shi ne har yanzu suke fama. Tana idarwa ta fito goye da Husainar ta je dakin su Sabrina ta rufe su da duka suna barci. A tsorace duk suka tashi suna tambayarta me ya faru? Kuka ta hau yi a gabansu tana fadin, sai barcinsu na tsiya ya jawo musu masifa, uwarsu na kwance babu inda ta ke iya motsawa tun dare suna nan suna barcin asara, duk kukan da ‘yan biyu ke yi ba su san ana yi ba ko me? Rantsuwa suka hau yi mata suna dirgowa daga gado suna fadin, wallahi ba su sani ba, kuma su ba su ji kuka ba. Ta ce su je su kula da Mama ita da Basma za su je asibiti a duba yaran. Wata na ture wata haka suka fita a gigice, ta bi su da harara da idanunta da suka yi jawur. Lokaci-lokaci gabanta na tsinkewa ya fadi, har sai ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta ta ambaci sunan Allah. Dan cikinta sai wani irin juyi yake kamar ya wuce watanninsa. Ta dawo tana rarrashin Basma, ta canza riga su tafi asibiti, amma ta yi gumm! Kamar ba da ita ta ke ba, gani kawai ta ke rasa yaran za ta yi, don haka ba ta ga amfanin su je wani asibiti ba. ga Aboubacar tun kafin azahar rabonsa da kiranta, ita kuma in ta kira shi wayar ba ta shiga. Dalilin damuwarta kenan. Aalimah ta yi rarrashin duniyar nan, Basma ta ki tashi, kawai sai ta fashe da kuka mai karfi. Ta ce, “Basma, ya ki ke so in yi da raina? Kina so na zauce? Ga Mama can ba ta san wanda ke kanta ba, ni ma zuciyata tsinkewa ta ke yi, karfin hali kawai nake yi, su kuma da gani akwai abin da ke damunsu. Jarirai su kwana ba su sha nono ba ki ce haka za mu ci gaba da zama da su muna kallonsu?†Basma ko gezau! Sai ta rabu da ita ta sanya hijab din sallarta ta dauki mukullin motar Aboubacar da ya bar musu don irin hakan, kamar ya san za su bukace ta. Ta nade Hassanar a shawul mai kauri, ta dauki katinansu na asibiti ta tafi, Suhaima ta biyo ta da gudu ta karbi ta hannunta tana fadin, “Muje na raka ki in ji Mamaâ€. Da suka je asibitin a sashen sababbin haihuwa aka karbi jariran (Day old), likitoci suka hau bincikarsu. Suka samu wuri ita da Suhaima suka zauna. Sai a lokacin nutsuwa ta soma dawo mata jin ta daina jiyo kukansu. Tunanin Aboulkhair ya fado mata. Ta kira shi bayan sun dawo daga asibiti da safe ya ce mata suna Katsina, “in mun shiga Niger I will call you. Take care of yourself and my baby for me MON AMOUR!â€. Kiran da har yanzu ko kyallinsa ba ta gani ba. Tsabar jiran kiran wuni ta yi rike da wayar a hannunta, in sallah za ta yi a cikinta ta ke soke ta. Da ta gaji da jiran ta yi ta gwadawa ita ya ki shiga. Ta yi tunanin sun shiga sahara sun rasa network, amma har twins suka fara jiniyarsu babu kiran Aboulkhair ko na Aboubacar. Mama ta ce, Daddy ma bai kira ba. A lokacin ya isa a ce ma sun shiga Niamey. To balle yanzu da za a iya cewa sun kwana sun hantse, tunda har ga shi alfijir ya keto. Ba ta kawo wani mummunan tunani a ranta ba, duk da ta san Aboulkhair yana da layin Niger. Ta sa a ranta bai samu sukunin kiran nata ba ne saboda gajiya duba da cewa, shi ya tuka motar tun daga Nigeria har Niger, har kuma babban birni Niamey. Sai dai wannan tsinkewar na zuciyarta shi yake damunta, saboda ba a son faduwar gaba ga mai ciki. A matsayinta na medical personnel ta san hatsarin hakan, don haka ta koma hailala da salatin Annabi cikin zuciyarta. Daidai lokacin likitan da ya karbi yaran ya fito. Tambayarta ya yi, ina uwarsu? Ta ce tana gida. Da mamaki ya dube ta, sai kuma ya basar ya ce ta je ta zo da ita za a debi nonon a ba su ta hancinsu, masassara ce ta cika musu makogaro. Ta ce da Suhaima ta zauna ta je ta zo da Basma, ba za ta jima ba. Har Mama za ta dauko. Tun daga nesa ta hangi bakar motar ‘yansanda fake a kofar gidansu. Tsinkewar da gabanta ke yi ya fadi da ta samu ya lafa sabida karfin hailala ne ya sake faruwa da ita. ‘Yansanda biyu na tsaye tare da maigadinsu Bilyaminu. A hankali ta ke rage gudun motar ta wuce su ta nufi gate tana danna wa Bilyaminu horn da nufin ya zo ya bude mata ta shige. Bilyaminu ya karaso da sauri, maimakon ya bude mata sai ya tsaya yi mata bayanin wai ‘yansandan gidan suka zo. Wani babba a gidan suke son gani. Ba halinta ba ne raina babba ko na kasa da ita, amma ba ta san sanda ta sakar wa Bilyaminu harara ba, “Amma dai ka san daga Daddy har Yaya Aboubacar ba sa nan ko? Don me ba za ka gaya musu ba da za ka tare ni kana gaya min? Ka san uzurin da ke gabana? Tunda ka ga na fita da asubah na dawo yanzu ba sai ka bude min kofa ba ka san ya zaka yi da su ba, tunda ba sata na yi ba?†Daya daga cikin ‘yan sandan ya karaso ganin ta ki kula su, kuma ta rufe dattijon da fada, “Excuse me Madam!†Ya fada da kyakkyawar siga. Dole ta yi shiru ta bi shi da ido. “Muna neman gidan Dr. Mansour Raazee, lecturer a jami’ar Bayero, tsangayar Mass Communication, da gidan Aboubacar Raazee, accounter GTBank Hotoro Branchâ€. Ya fada cikin harshen turanci. A sanyaye ta ce, “Nan ne!â€. “Ko za ki turo mana namiji ya bi mu ofishinmu? Akwai bayani a kansuâ€. Girgiza kai ta yi, abin gwanin ban tausayi ta ce, “Ni ce babba a gidan, babu namiji bayan su, uwata kuma ba ta da lafiyaâ€. Tsayawa ya yi yana tunani, bai kamata ya tafi da ita ba ya gaya mata al’amarin da ke tafe da shi, ga ciki yana gani tare da ita, kuma ga dukkan alamu dukkaninsu ‘yan uwanta ne. A hotunan da aka turo musu babu wanda bai yi kama da ita ba. “Madam, daure ki turo min namiji ko makocinku ne, zan fi son magana da shi a kankiâ€. “Ka yi hakuri Officer, ni ma bakuwa ce a unguwar ban san kowa ba. Ka yi hakuri ka bar ni in wuce in ba za ka hanzarta fadar uzurinka ba. Na baro jarirai a asibitiâ€. Kawai sai ta soma hawaye a gabansu, zuciyarta ce ta tsinke, jikinta ya gama ba ta wani tafiyayyen labari ne suke tafe da shi, wanda zai kawo karshen duk wani farin cikin rayuwarta. Wanda suke shakkar tattauna shi da ita, ganinta mace, kuma mai ciki. “Ok, since you insist (tunda kin dage), za ki iya biyo mu ofishinmu?†Ta zuki numfashi da kyar, amma ta kasa furzo shi waje. Yau ita ce a ofishin ‘yan sanda a kan laifin da ba ta sani ba! Kodayake sun ce abin da suke tafe da shi din ya shafi babanta da yayanta ne. To ko laifi suka yi? Ko kama su aka yi a hanyar Niger din? To su kuma sauran da ba’a ambata ba ina suke? Ba ta da amsa ko daya, don haka ta share hawayen da suka cika mata fuska ta ce su ba ta minti goma ta fada a gida, ta dauko ‘yar uwarta ta kai ta asibiti, sai ta same su a inda suka ce. Tana shiga gida ta tarar da wani tashin hankalin. Basma ce a sume, su Sabrina na ta sheka mata ruwa. Duk tsananin da Mama ke ciki ta sa sun tayar da ita sun jinginar a jikin filo. Sabrina ke gaya mata tunda aka yo mata waya daga Niger aka ce su Daddy ba su isa ba tun jiya kuma an kasa samun kowannensu a waya ta ke suma tana farfadowa. Ta dubi Mama a firgice sai Mama ta lumshe ido, ta ce, “Ku hada karfi ku sa ta a mota, ki kai ta asibitiâ€. Jikinta na rawa ta ce, “Mama har ke zan kai, wallahi