← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 91

Sashe 24

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Zuwa lokacin azahar ta yi, dakinsa ya koma ya yi sallah, ba ya bukatar abinci don haka ya je ya yi sabgoginsa a cikin gari zuwa lokacin da Aalimah ta gaya masa tana da sarari. Yana yin parking kuwa ya gansu suna fitowa, daga dakin laccar tana rungume da folder.
Tsura mata ido ya yi tana nufo motarshi. A zuciyarsa tambayar kansa yake yi, me ya fi so a Aalimah? A gaggauce amsar ta halarto zuciyarsa… Yana son komai nata… komai ta yi abin burgewa ne a idonsa. He loves her dearly.
Har ta shigo ta zauna a gefensa bai sani ba. Sai da ta hada yatsunta biyu suka yi kas! A kunnensa. Kallonta ya yi, sannan ya dauko wayarta daga inda ya ajiye ta ya lalubo lamba ya danna kira. Ba ta ankara ba ta ji muryar Mahmoud na amsawa da sallamarsa, yana tambayar ina ta shiga kwana biyu? Kafin ta kwace wayar ya bada amsa,
“Ba ita ba ce, mijinta ne, kuma Yayanta, wanda ya bada sadakinta ga iyayenta. This is for your information not to call or text my wife againâ€. Ya datse kiran.
Aalimah ta ji ba dadi har fuskarta ta nuna.Mahmoud yana da mutunci a idonta ko don Yaya Aboubacar. Ko rabuwa za ta yi da shi ba za ta so su yi irin wannan rabuwar ba.
Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta don ganin reaction dinta, amma ya kasa fahimtar komai ban da rashin jin dadin da idanunta suka nuna. Magana ta yi a hankali cikin rarrashi don fahimtar cewa so yake su yi rigima.
“Haba Yayan Basma? Abokin Yaya Aboubacar ne kuma…..†Ta yi shiru ta kasa ci gaba.
“…... Kuma saurayin kiâ€, yayi maza ya karasa mata. “Kawai ki fashe da kuka na raba ki da saurayinki…â€.
Turo baki ta yi cikin shagwaba, “…Ni ba saurayina ba ne, cewa zan yi muna mutunci ni da shi fa… Ni ba ni da saurayi…â€.
Ganin yadda yake kallon bakin nata admiringly ya sanya ta maida bakin nata ta kintse, ta kuma sunkuyar da kanta. Murmushi ta shiga saki kasa-kasa a sanda ya sanyaya murya ya ce da ita,
“Har NI?â€
Tafukanta ta kai ta rufe fuskarta tana murmushi,
“Kai ma Yayana neâ€.
“Ko?†Ya tambaye ta.
Bai jira amsarta ba ya ci gaba, “Za mu bambance hakan ranar da aka daura mana aureâ€.
Ta kara tusa fuskar tata cikin tafukan nata, cikin matsananciyar jin kunya.
Wayarta ya jefa mata kan cinyarta ya tada motar, “Na bude miki Whatsapp, Daddy ya amince min in dinga magana da ke ta waya, daga yau har zuwa ranar da zai karbi sadakinki. Idan ki ka yi chatting da wannan mutumin Allah ya isaâ€.
Dariya ta soma yi tana fita daga motar. Ganin yadda yake maganar with confidence kamar ta furta masa tana sonshi ita ma. Tana son mutum mai courage, wanda ya iya yarda da kansa.
Ko da ta koma class ta bude littafin da ta ke rubutu, samun hannunta ta yi da rubuta haruffan guda tara, ‘A…B…U…L…K…H…A…I…R, ta zagaye su da zanen zuciya (heart). Kafin ta ankara cewa a cikin littafin daukar laccarta ta ke yi. Hannu ta kai ta dafe goshinta tana ambaton sunan Allah, me ke damuna ni Aalimah? Me ya shiga kaina? Me zuciyata ke nufi da ni a kan Yayan Basma? Ina zan kai Mahmoud wanda ke can wata duniya yana jirana? To amma me? The feelings are entirely not equal! Ko kusa da juna ba su zo ba, infact, abin da ta ke ji a kan Aboulkhair ba ta taba jin irinsa a kan kowa a duniya ba.
Chapter 24 · 0% Book details