← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 91

Sashe 57

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ba zan barki a gida ba. Kuma yanzu zan yi wa Mummy waya har Niger din in gaya mata ga halin da ku ke ciki dukkanku, ni kadai ba zan iya ba, kwakwalwata kamar ta zauce. Yanzu haka ‘yan sanda ne a bakin gate sun zo tafiya da ni. Ba su je Niger ba, ina suka je? Na shiga uku ni Aalimah, ko dai ‘yan fashi ne suka tare su?†Dukkansu babu wanda ya kawo wani abu a zuciyarsa bayan wannan, Mama ta ce ba za ta iya fita zuwa mota ba. Aalimah na kuka ta ce, “Ko a goye ne sai na kai ki asibitiâ€. Ita da kannenta biyu suka ciccibi Mama, rabi kuma da kafarta suke janta a kasa zuwa mota. Suna fitowa harabar gidan Tabawa da Sabira suna shigowa (masu aikin Mama), wadanda ba aikin kwana suke yi ba. Wata ajiyar zuciya Aalimah ta yi, da hanzari suka taimaka mata ta sa Mama a mota, ta gaya musu saura Basma, Tabawa ita kadai ta ciccibo Basma sabida kakkarfa ce. Gabadayansu suka duru a motar har su Sabrina, su biyu a gaba, ta ja su zuwa asibitin da ta kai su Hassana da Hussaina. Dukkansu an karbe su ba bata lokaci, da yake asibitin na kudi ne, international. Ta gaya wa Mama za ta je ofishin ‘yan sandan ta dawo, Mama na daga kwance ta ce ba ta yarda ba. Ta kara gwada layin Aboulkhair, in har yanzu ba ta same shi ba, ta kira Uncle Oussama ta gaya masa, ko kofar asibitin ba ta yarda ta taka ba. Hakan kuwa ta yi, duk da cewa ta so Mama ta barta ta je, don idan reality bai kassara ta ba, fargaba da zullumi dake zuciyarta za su haifar mata da hauhawar jini, wanda shi ma ba’a sonsa ga mai ciki. Jiya-i-yau. Ba ta samu Aboubacar ko Aboulkhair ko Daddy ba. Don haka tana kuka ta kira Oncle Oussama wadanda ke can zugum-zugum sun kasa daura aure bayan sun tara jama’a makil daga birni da kauye, tunda babu labarin iyayen yaran bayan kowa ya tabbatar da tahowarsu tun jiya. Kukan da ta ke yi bai hana shi gane me ta ke cewa ba. Duk halin da suke ciki tun jiya ta warware masa. ta gaya amsa yanzu haka duk an ba su gado daga su har jariran kuma Mama ta hana ta zuwa police station din. “Za mu zo a yau, kada ki sake kije police station dinnanâ€. Abin da ya ce mata kawai kenan yana mai jin wani irin tsoro da tashin hankali na shigarsa. Ango Hamoud da ya yi zugum a gefe, da Mu’azzam da ya iso tun jiya ya ja gefe ya ce su je su nema musu ticket yanzu-yanzu mai zuwa Abuja, shi da Edrissa da Mu’azzam da angon da Malam kansa. Bayan wannan bai kara musu bayanin komai ba. Ya karbi sadaki daga hannun kaninsa babban dan Inna Bintou ya daura auren Khaleesat da Hamoud ba cikin dadin rai ba, sai don ba yadda za su yi da jama’ar da suka tara. Tun ba a gama watsewa ba ya ja Malam gefe ya gaya masa duk bayanin da Aalimah ta yi masa a waya, ya kara da cewa, yana tsammanin suna hannun ‘yan sandan da suka je neman wani nasun, ko dai sun yi wani laifin ne an kama su, ko ‘yan fashi ko hadari. Abin da yake zato kenan. “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’unâ€. Shi ne abin da Malam Ibraheem Raazee ke ambato, babu kakkautawa. Zufa na keto masa ta ko’ina a jikinsa a lokacin da ya daga kai ya hangi Mu’azzam na fitowa daga mota.
Chapter 57 · 0% Book details