← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 91

Sashe 35

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kamar yadda Mummy ta yi alkawari washegari ta shirya musu tafiya picnic zuwa ‘Miami’.
Ko a kwanaki uku da suka karar tare a Miami Resort, Mummy ba ta fahimci komai tsakanin Abulkhair da Aalimah ba. Suna zaune a gabanta suna chatting da juna da wayoyinsu bata san me suke yi ba. Sannan daki daya ta kama musu dukkansu ita da yaran, Abulkhair na dakinsa shi kadai, sai sun fito bakin beach suke haduwa. Watakila kuma don ba ta da kurillah ne da ta gano yadda suke magana da juna cikin halittar idanunsu. Da ta hango matsananciyar soyayyar da ke kwance cikin idanun kowannensu.Sun shakata yadda suke so. A jirgin Alaska Airlines suka je Miami daga Boston a cikinsa suka dawo.
Da suka sauka a filin jirgin saman Boston Logan, Mummy ta fiddo waya ta kira Joseph. Shi ya zo ya kwashe su zuwa gida.
Tun daga harabar gidan suka ga alamun an canza wa motar Daddy matsugunni. Motar da shi kadai yake hawanta, wato Chevrolet volt. Har suna hada baki yaran da Mamansu wajen tambayar Joseph, “
Daddy ya dawo ne?â€
A nan yake gaya musu ai tun washegarin tafiyarsu suka dawo shi da second madam dinsa.
Mummy ba ta wani fahimce shi ba. Cike ta ke da dokin ganin mijin nata abin kaunarta. Amma su sun gane me Joseph ke nufi da second madam, ban da Abulkhair. Jikinsu gabadaya ya yi sanyi, don haka ba su wani fita da sauri ba, Mummy ta riga su isa kofar shiga gidan da kanta ta danna kararrawa kafin su karaso.
Wata kyakkyawar ba’abziniya kamar balarabiya, ita ta bude kofar. Idanunta cikin na Zulaiha. Ba ta fice age mate (sa’ar) Abulkhair, wato ba za ta wuce shekarunsa ba. Mai yawan fara’a da hasken idanu da na hakora. Kallon-kallo suka shiga yi, sai dai kowacce nau’in kallon da ta ke yi wa ‘yar uwarta daban yake da na ‘yar uwarta. Zulaiha kallon ya tashi daga na mamaki ya koma na tsoro, da tunanin aljana ce ta shigo mata gida, don wannan ba ta yi kama da turawa ba. Yayin da Gumsu Moiram, ke kare wa uwargidan Ishaq kallo da son tantance rukunin matan da ta ke ciki don ta san da fuskar da za ta rayu da ita.
Daddy ne ya iso kofar ya katse kallon kudan matan nasa biyu. Shi ma kansa a darare yake, amma ya karfafi kansa ko don ya zama cikakken miji a gidansa ya ce, “Sun dawo ne? Gumsu shige ciki su shigo, ina zuwaâ€.
Ta wuce ta koma ciki.
Mummy Zulaiha ta kalli Daddy cikin ido, yawu ya kafe a cikin bakinta. Kin shiga ta yi kamar yadda yaran ma suka ja tunga a bayanta. Ta ce, “First, tell me who is she?â€
Da sassauci a kan fuskarsa ya ce, “A bakin kofa, a gaban yara ki ke so mu yi magana irin wannan? Ki shigo ciki tukunnaâ€.
“Magana irin wacce?†Ta tambaya cikin danne ko ma wane irin tunani ke son shiga zuciyarta a lokacin. Hannunta kawai ya kamo ya janyo ta cikin falon su Aalimah suka biyo bayansu.
Bai cika hannun Mummy ba (upstair) ya haye da ita don su kauce ma idanun yaransu. Yayin da amarya Gumsu ta wuce dakin da Daddy ya ba ta tun zuwansu, dakin Mu’az na da, kafin ya sama mata matsugunni.
Duk wani bayani irin na nuna concern, wanke kai da kawo dalilai Ishaq Raazee ya yi ga Mummy Zulaiha don ta karbi kaddarar aurensa kamar yadda ya karbe ta, ta yarda bai yi da niyya ba, bai yi don ya tozartata ba, bai yi don ya daina sonta ba. Zulaiha ta ki fahimtar ko guda daya. Wani dan karamin hauka ne ya same ta a wannan lokacin. Ta gaya masa ta bar gidansa kenan, har abada ba zai burge ta ba sai ya auro matan Niger Republic bakidaya sannan za ta amince danginsa ba sa sonta. Ga gidansa nan, ga ‘ya’yansa nan, ya manta ya taba saninta a rayuwarsa.
Su dai su Aalimah suna zaune jigum-jigum kowacce da jakar matafiyanta a gabanta a falon kasa, tun bayan da suka shigo Abulkhair bai zauna gidan ba, ya shiga cikin gari ne tun bayan ya gaisa da amarya Gumsu da bai wan wace ce ba. Ya dai fahimci Daddy ya zo da ita ne daga Niger, sai ganin saukowar Mummy suka yi a sukwane tana hada steps biyu-uku, ta ja jakarta da suka dawo da ita ta yi waje, sai ga Daddy ya biyo bayanta da sauri shi ma. Yesmin ta bi ta da gudu, ya ce Khaleesat kada ta barta ta fita. Ta je ta riko ta tana kuka tana kiran Mummy. Wayarsa ya fiddo ya kira Abulkhair ya ce, “Kana ina?â€
Abulkhair ya amsa da cewa, ya dan fita ne amma ga shi nan ma ya shigo kwanar gidan.
Ya ce, “Ka kula da Mamanka, ga ta nan za ta dau mota ta fita. Kada ka barta ta yi tuki. Take care of herâ€.
Abulkhair ya amsa, “Don’t worry Daddyâ€.
A take kuma ya shiga hasashen abin da yake faruwa da matar da ya gani daga Nijar.
“This cannot be possibleâ€. Ya fada a fili.
Karawa motar gudu ya yi ya karaso gida, daidai Mummy na sanya jakarta a but din motarta tana rufewa. Ko daidaita parking bai yi ba ya kashe motar ya fito har da gudu ya hada ya bude mazaunin direba ya shige ya rufe. Kofar kusa da shi ta bude ta zauna tana fadin.
“Please go out, tafiya zan yiâ€.
“Ina so in raka ki ne Mummyâ€.
“Wannan karon tafiyar ba ta dawowa ba ce, please go to your Dadâ€. Sai a lokacin ne ta samu hawaye suka zubo mata.
Abulkhair ya ji wani iri a zuciyarsa, tissue din motar ya zara ya shiga tsane mata hawayen fuskarta.
“Mummy kun wuce wannan level din ke da Daddy, don Allah ki koma ku sulhunta kanku albarkacinmuâ€.
Girgiza kai ta shiga yi tare da fadin, “Ni da Babanku har abada! Kishiya ya yi min a shekarun girmana da furfurarsa da komai. Me zan yi da danginku? Tsakanina da su sai Allah ya isa!â€
“Hasashena ya tabbata gaskiya kenan?†Abulkhairi ya fadi a zuciyarsa, “Na fahimta Mummy. Amma yanzu komai zan gaya miki ba za ki fahimce ni ba. Kina bukatar nutsuwa. Yanzu ina zan kai ki?â€
Da sauri ta ce, “Las Vegasâ€.
Murmushi ya yi. A ransa yana fadin, “Wurin sanyin idaniyarta, mai share mata hawaye, mai fada mata ta ji kamar iyayenta. Kai ka ce shi ne uban ita ce ‘yarsaâ€.
A fili kuma ya ce, “Mummy, ni ma ki so ni yadda ki ke sonsa!â€.
Duk halin da Mummy Zulaiha ke ciki sai da maganar Abulkhair ta sa ta murmushi. Anya za ta so wani Da cikin ‘ya’yanta irin son da ta ke yi wa MU’AZZAM?
Chapter 35 · 0% Book details