← Book details Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 91

Sashe 43

Aalimah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

tunawa shi musulmi ne a duk inda ya tsinci kansa, ya kiyaye martabar addininsa da koyarwarsa. Rayuwa cikinsu da cudanya da su (ahlil kitabi) ba laifi ba ne a musulunce, amma ‘ya’ya amana ne a hannun iyaye da ya zama dole a dora ido a kan mu’amalarsu da rayuwarsu, a tsawatar a inda yake bukatar tsawatarwa. Makauniyar soyayya ga ‘ya’ya ba gata ba ne a gare su, don haka za ki yi ta kuka fiye da Mu’azzam tunda ke uwa ce, kin fi shi son kansa da kansa, babbar banza kawai! Ashe matan ma Aalimah ce ta gyara su inji Balkissa amma ai da dan wando da ‘yar riga suke yawo, kai ba kallabi kamar akuyoyiâ€. Haka Uncle Oussama ya karewa Mummy tanadi tas ko dagowa ba ta yi ba. Malam dai ya kasa magana, tausayin Mu’az ya kashe bakinsa da zuciyarsa. Sai da Oussama ya yi shiru sannan Baban Aalimah Dr. Mansour ya yi gyaran murya, ya dubi Uncle Edrissa, ya ce, “Ban musanta batunka ba Yaya Oussama. Kuma ban hana a nema wa Mu’azzam magani namu na gida ba. Amma zancen ya bar treatment dinsa ya daina shan maganin likitocinsa bai taso ba. Da gaske wannan cuta ce mai zaman kanta na taba cin karo da ita a wani bincike da muka gudanarwa world health organization (WHO) a kan hanyoyin da za a bi a rage cututtukan kwakwalwa a cikin al’umma. Kuma ba bugun aljannu ba ne, sannan ba a America kadai ake samun masu fama da ita ba, wallahi har nan Nigeria inda nake, kawai dai Society dinmu ba su dauke shi mental health deficiency ba ne, sun fi daukarsa a DABI’A. Don haka ni shawara ta ita ce a jefi tsuntsu biyu da dutse daya, wato Mu’azzam ya ci gaba da shan maganin asibiti, sannan ku ma ku yi irin naku kokarin, a taru a roki Allah ya yaye masa bakidayaâ€. Kowa ya yi na’am da shawarar Dr. Mansour, ko da ma can duk ya fi kowa a gidan kaifin hikima. “Don haka mun ajiye batun Mu’azzam a gefe, za mu dawo kansa daga baya in mun samu nutsuwa. Yanzu muna kan na masu lafiyar. Ishaq, me kake ciki maganar auren ‘ya’yanka? Kai ma Mansour me ka ke ciki kan Aalimah da Aboubacar?†In ji Uncle Oussama. Daddy Ishaq ya muskuta ya ce, “Ba kin aurar da su na yi ba. In don ta ni ne da tuni na dade da aurar da su. Sun dade da hada kansu shekaru biyar a baya. Bana so ne in shiga gonar Mansour, ina so ya samu cikar burinsa shi da Aseeya a kan Aalimah, kada ya ga kamar na so kainaâ€. Ido sosai Dr. Mansour ya bude yana kallon Yayansa cikin rashin fahimta. Edrissa ya ce, “Kamar ya ya? Su waye suka hada kan nasu?†“Aboulkhair da Aalimahâ€. Fuskokinsu suka bayyana dadin da zancen ya yi a zukatansu. Malam ya ce, “Da ma aure yana hana wani buri cika ne, ko dai ya taimaka masa ya kai ga ci? Tukunna ma wane buri ne Mansour din da maidakinsa suke da shi a kan Aalimah? Da ma ana ci wa ‘ya mace alwashi a hana ta aure ne?†Nan Daddy Ishaq ya warware musu komai kan ba shi ya dauki nauyin karatun Aalimah ba. Ya gaya musu duk abin da ya wakana. Dr. Mansour Raazee ya dubi yayansa kamar zai yi kuka, “Ba ka kyauta min ba Yaya! Shekaru biyar Aboulkhair na dakon soyayyar Aalimah bayan kai kanka mai daura mata aure ne. Aseeya ke son karatun nan ba ni ba, kuma ita ma in ta san Aboulkhair ne zai auri Aalimah ba za ta hana ba. Shekara biyar Yaya? Ban ji dadi ba ko kadan. A kalla da ka gaya mini ko shawara ce mu yi,. Idan har yanzu Aboulkhair na son Aalimah bai canja shawara ba sabida nisan shekarun da aka sanya shi jira, na ba shi ita duniya da lahira, kuma ban da sadaki ban dora masa komai ba. Sadakin ma in an amince min, zan biya masaâ€. Uncle Oussama ya ce, “To ba a amince maka din ba. Shi zai biya ni daga aljihunsa. Aboubacar da Basma fa? Me suke ciki? Shin zancen da Inna Bintou ke fadi cewa sun hada kansu gaskiya ne?†Shiru Dr. Mansour ya yi, sannan a sanyaye ya ce, “Na san zancen, sai dai ban taba ba shi muhimmanci ba, a bisa hujjojina kwararaâ€. “Wane Aboubacar din da wace Basman?†Daddy Ishaq ya tambaya cikin mamaki da kuma dokantuwa da a fidda shi cikin duhu. Nan Malam ya gaya masa shi ya dade da sanin zancen a bakin iyayensu mata. Ya yi zaton ya sani shi ya sa ya yi ta zuba ido yana jira su zo masa da zancen. Da ya ga suna nufin sai bayan ransa shi ya sa yake so a yi ta ta kare a yau. Ko bai ga ‘ya’yansu ba, ya shaida aurensu ya gode wa Allah. Daddy ya dubi kaninsa zuciyarsa na ninkaya cikin farin cikin da ya gaza boyuwa a kan fuskarsa. “Ba ka bai wa zancen muhimmanci ba sabida wadanne hujjoji naka? Da ni da kai wa ya fi rashin kyauta wa dan uwansa?†Murmushi ya yi ya sunkuyar da kansa, “Ku fahimce ni bakidaya, dukkaninsu ba mai iya zama a kasar da dan uwansa ke zaune. Kowanne yana da tsararriyar rayuwa a inda yake. Sannan abu ne mai wahala Basma ta iya baro iyaye da ‘yan uwanta ta zauna da mu a Nigeria. Sannan ina tunanin kamar karfin samunsa bai isa ya rike ta ba in aka yi duba da irin rayuwar da ta taso a cikiâ€. Murmushi Daddy Ishaq ya yi, kanin nasa na kara shiga ransa. Idan zai yi abu sai ya duba shi (from every sphere, he leave no stone unturned), “To ai ni kaina na kusa barin Americarâ€. Ba Mummy Zulaiha kadai ba, kowa a falon sai da ya juyo ya dube shi. Gyada kai ya yi don tabbatar musu da furucinsa, sannan ya ci gaba da bayani yana kallon matarsa. “Saboda Mu’azzam na kai wannan lokacin a America, saboda yana karbar proper medical treatment, kuma bana so mu taho gabadaya mu barshi shi kadai, ga aikinsa ga yanayin da yake ciki, a ce ba shi da kowa a kasar da yake zaune. Amma ni tun farkon faruwar matsalolin nasa kasar Amurka ta fice min a rai. Ina ta dakon damuwar Mu’azzam. Yau da na fayyace muku sai na ji kamar an dauke min wani nannauyen dutse daga kirjina. A kalla nasan ba ni kadai nake jigilar damuwar ba, ina da masu taya ni ko da da addu’a ne. Target dina na yanzu shi ne, Aboulkhair ya kama aiki, ya yi aure ya zauna kusa da shi, ni kuma in nemi aiki a nan Niamey in dawoâ€. “Allah ya yi maka albarkaâ€. Inji Malam Raazee, “Shi kuma Allah ya ba shi lafiyaâ€. In ji Uncle Oussama da Uncle Edrissa. Ba su tashi daga wannan zaman ba sai da suka yanke lokacin auren yaran nasu hudu. Daddy ya gaya musu ita Khaleesat yana da buri a kanta, ya dade da gane shirin da ke tsakaninta da Hamoud kafin ya tafi Japan, inda yake kwas din aikin sojan ruwa, shekara mai zuwa zai kammala. Uncle Oussama rasa me zai ce ya yi, danshi yake wa tanadinta, amma ya gaya masa maganganu marasa dadi dazu. Matsar kwalla ya shiga yi yana cewa, “Pardonne-mon frereâ€. Wato (ka yafe min dan uwa da harshen faransanci). “Ni ba ka yi min komai ba Yaya. Kauna ce ta saka damuwa da lamarin Mu’azzamâ€. Addu’a mahaifin nasu ya daga hannu ya yi musu bakidayansu. Ya sa musu albarka, ya roki Allah ya sa su gama da duniya lafiya, ya kara musu kaunar junansu.
Chapter 43 · 0% Book details