← Book details Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 28

Sashe 28

Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sannann kuma wane zumudi
na nuna na tarewa a gidanka, Ya Abba ka sani
yanda a ka tilasta maka aurena, to ni ma fa dole
tasa na hakura.

Amma ka rike a ranka bana wani
sonka bani kamarina ina sonka, kalaman nata na
karshe sun burgeshi har sun sa shi yin da ya
sanin tsokale zancen.

Sai kuma ya canza salo da
cewa, haka dai ki ka ce amma ina da ja mu dai
bar zancen, shin dazun kafin ki soma wannan
tunanin me ki ke yi?

Ta danyi shiru tana
tambayar kanta.

Dama mutumin nan haka ya ke?

Oh yanzun dabara zai min sai ya gano ko ina
sonshi dole, to kuwa bazai ji ba, ya katse ta da
cewa ban san ki da karya ba.

Ta ce, ina tunanin
irin ukubar da zan sha a gidanka ne ta
wulakancin da zaka min, ya yi shiru zuciyarshi
tana cewa yarinyar nan ba ta san irinson da ka ke
mata ba ai ta ma dauke ka mugu kenan.

A fili sai
ya ce, "Kuma fa kin yi tunani, Allah yabaki ikon
daukar ukubar da zaki sha tare kuma dajure
wulakancin da na tanadar miki goben Ummi.

"Ya
fadi, wai dama da gaske wulakancin zai mata.

Gyara kwanciya kawai tayi bata kara cewa komai
ba, kuma bata da nufin cewa wani abu, yasa taji
haushi sosai, don haka sai ya tausasa muryarshi.

"Ummi kina ji na?" Uhm" Kurum ta ce, don ya
gane tana jin shi.

Alkawari ta dauka ba zata sake
cewakala ba, tunda ya hanata kashe wayar.

"Ba
ni da nufin miki..." Sai layin ya yanke daga
gefanshi, ta ce, "Gara ma haka".

Tana kokarin
kashe wayar gaba daya kiranshi ya sake shigowa.

Tsaki taja kafin ta daga, kuma a ciki ta amsa
sallamarshi, sannan cikin murya mai kamar zata
rushe da kuka ta ce "Ya Abba ni fa bacci nake
son in yi".

Ya ce, "Sam ba wani bacci da za ki iya
yoa sai tunani".

Ta ce "To na ji, ina son yin
tunanin please".Ya ce, "Tunanin me za ki yi".

Cikin gundira ta ce,"Dole in yi tunanin yanda zan
kare kaina daga wulakancinka, don bana
tsammanin zan dauka" .Ya ce, "Wasa nake miki
fa." Ta ce, "Uhum, ban amince da cewa wasa ka
ke min ba, don na tabbata mu ba abokan wasa
ba ne".Ya ce, "To shi ke nan bari in bar ki kiyi
tunanin, amma tunanin yanda za ki faranta min
za ki yi".

Muryar Bishira ce ta katse shi.

"Oho!

Ai
tun da na farka ban ganka ba na san ana nan
ana cin amanata".

Ya kashe wayar da sauri, duk
da dai Ummi ta riga ta jiyo muryar Bishiran.

Sai
dai bata fahimci me Bishirar take cewa ba,
ringingine tayi tare da dora filo a kirjinta, tunani
take yi wane irin zama za su yi?

Koda bata da
amsa ta kudurce har abada ba za ta dauki
wulakanci ba, a shi ko a matar shi.

Sai dai
alkawari ta dauka ba za ta musu raini ba,
matsawar ba su suka 6ullo da hakan ba. *
************************************** Shi ko
Abba rigima suka dinga yi da Bishira cikin tsohon
daren wai ya cuce ta ya kwanta da ita yazo yana
hira da wata banza.

Kila ma ya saba kwanciya da
Ummin ne yau bai samu dama ba, Abba ya ce kin
so kanki in ki ka yimin wannan zaton, don ban
ta6a nemanki ba, kafinki shigo gidana, ko na
ta6a?"Ta ce, "Don ka san dai ni ba fuska".

Da ya
gaji da iya korata ya rufe kofar ya koma can
dakin. 40. 74...

Washegarin ranar, ga mamakin
Ummi tun misalin karfe goma jama'asuka cika
gidansu, a ka dora abinci.

Can kuma saiga yaran
shagon Abba da dinkunan zannuwan daAlhaji
Babba ya sai mata.Ranar Abba bai shigo gidan
ba a waya ya kiraUmma suka yi magana, zuwa
karfe uku angama yiwa Ummi jeren dakin da yake
yana da girma yacinye komai tsaf.Fitar 'yan jere
babu jimawa sai ga Anty Farida dakannasu motar
tana da kaya tana biye da su, gadoda kujeru a ka
canzo mata.Suka jera mata sannan suka lodawa
motar na dasuka dauki hanya suka koma, Abba
kam yana gurinaiki amma zuciyarshi tana
gida.Fatanshi Allah yasa yana zuwa ya tarar an
kaimishi Umminshi, kawayen Bishira da
makotansu'yan jam'iyyarta duk sun shigo gidan
sun hadu saizugata suke yi tare da nuna mata
koda wasa kadata sakar ma Ummi fuska, kuma in
ta mata takamata ta duki 'yan kayanta.Suna
gidan a ka kawo Ummi, 'yan kawo Amaeyakam
suna jiyo habaici da zagin da su Bishira ke yi,don
haka suka ce kada a kai musu yarinyar.Inna
Saratu da Inna Harira suka ce ai kuwa sai
ankaita.Ba ko kunya Bishira ta zabga musu
harara lokacinda suka fada mata cewa ga
kanwarta sun kawomata, don Allah su zauna
lafiya tare da Aminci.In yarinyar tayi ba daidai ba
ta sata a hanya... takatse su cikin tsawa da
mikewa tsaye.

"Don Allahku fice min daga daki
amanar kishiya?

Har wai muzauna da aminci ku
ke cewa?Tayi 'yar dariyar yake "Kun yi kuskure,
ai batacanza daga sunan ta na kishiya ba, kuma
kowa yasan kishiya abokiyar gaba ce."Inna
Saratu ta ce, "Baiwar Allah jahilan mata sunesuke
yin irin wannan tunanin, amma ga masu ilimisuna
koyi da gidan mai tsira da Aminci
(S.A.W)ne".Bishira ta ce, "To kawai dai ki ce min
jahila ki huta,bari ku ji ba za n ba ku a 6oye ba,
zama ne za muyi shi na rashin mutunci, na kowa
ya iya allonshi.

Don ina kishin mijina, kuma zan
nuna".

Tirkashi!

Lallai akwai daru kenan.

To
masu karatu ku biyo ni cikin littafi na 4, kumana
karshe domin jin yadda za ta kasance atsakanin
Bishira da Ummi da kuma Oga kwata-kwata wato
Chapter 28 · 0% Book details