← Book details Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 28

Sashe 26

Zurfin Ciki Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To sai ya ce tunda ke kin ki kwantar da
hankalinki ki kwantar da na mijinki to ya fasa
naki, mu harmun yi passport.

Bishira ta zaro ido,
da gaske Anty?

Anty ta ce, Allah da gaske.

To
yanzun shi ne ni ke son in ce muje mu ba shi
hakuri kila ya amince.

Bishira ta ce, Tashi muje
Anty don Allah, Anty ta ce kin tambayo zuwa can
ne?

Bishira ta ta6a baki, nifa ko nan din ban
wani tambaya ba, wallahi gidan ne bakikkirin
nake ganinshi.

Anty ta ce, "Ki dinga addu'a, kishi
yayi miki yawa.

Sannan ki daina fita ba tare da
izinin mijinki ba, duk in da ki ka je har ki dawo
Mala'iku suna tsine miki.

Don haka yanzun tashi
ki tafi gidanki, ni zan samu Hajiya da Dady yau
din nan kuma in sha Allah za amiki gyaran dakin,
sannan tafiyar za ta kasance tare da ke.

Bishira
ta ce, Na gode Anty, amma don Allah ki barni na
dan huta a nan gidan duhunsa nake gani, don ba
ki ji yanda ni ke ji ba ne Anty ko da dana Walid
ya rasu ban ji kunci irin wannan ba.

Ta sake
rushewa da sabon kuka wiwi, Anty kallonta kawai
take ta ma rasa me zata ce.

Wayarta ta ciro
daga chaji ta shiga kiran layin Abba, lokacin ya
kira kananan kannanshi su Kamal suna ta fito da
kayan dakin Bishira saboda ayi fenti har an gama
nashi dakin.

Wayarshi da ya ajiye a kan windown
dakinshi ta shiga ruri, ya duba, Anty ce.

Ya daga
tare da sallama, ta amsa ya gaida ta cikin
girmamawa da mutuntuwa, ta amsa da fara'a
sannan ta ce, "Abba ga Bishira nan tazo tana
kuka, kuma ta ce min ba ka san ta fito ba".

Ya
ce, "Eh haka ne, ta ce don Allah in baka wani abu
ina son ganinka.

Ya ce To zan zo Anty, amma
yanzu ina aiki ne kayan dakin ta muke fita da shi
za a yi mata fenti ne, ta ce To ko da dare ne
haka, ya ce to zan zo. * 68....

Ummi tana ta zuba
ido ganin Abba amma shiru har a ka yi Magriba
tayi wanka tayi sallah.

Tana zaune har Isha'i tayi
daga Masallaci shima ya nufo gidan su Ummi,
lokacin Ummi tana bakin gado tana 'yan shafe-
shafenta.Ta juyo Abba suna gaisawa da su
Umma, ta shirya cikin leshi mai ruwan lemun
tsami, da dan mayafinta fari haka takalminta.

Ta
fito tana zaune kan kujera, ta ce "Sannu da zuwa.

Za ka ci abinci?" ya ce, "Da sauri haka ba muko
gaisa ba?" Ta zauna ina yini?

Ya ce, lafiya lau.

To
na kawo abinci?

Ya ce, daga gida fa nake, ina da
kuma mata.

Ummi ta ta6a baki, oh, haka ne ashe
kana da mata, gani nayi da matar taka ka ke
zuwa cin abincin daga nan ta lafe a kujera tare da
hada rai.

Ya mike muje ko? itama ta mike, ya
kalle ta da wannan mayafin za ki?

Ta ce, eh, ya
ce a'a dauko hijabi ba zan lamunci yafa wannan
dan mayafin ba.

Ta kalle shi kamar ta ce ai
matarka tana yafa irin shi sai kuma tayi shiru ta
nufi uwar daki don dauko hijabi.

Shi kuma ya nufi
waje, ta yi wa su Umma sallama sannan ta fito.

Yana tsaye jikin mota ya ce, ina wayar nan?

Ta
ce, "Gata nan a hannuna ya yi dan murmushi
yace mayyar waya dama nasan sai kin dauko har
yanzun cikin haushin maganar shi ta dazun take
yi.

Don haka bata kula shi ba, ya shiga motar ya
bude mata gefen kusa da direba ta zauna cikin
fushi.

Lura ya yi da hakan, don haka sai ya ce ba
ni tamata ta ce so nake in loda mata kudi.

Ya
guntse baki don kada yayi dariya, ganin yanda
tamiko mishi wayar cikin hanzari gata Allah yasa
bacewa nayi a bani ba.

Ta juyar da kai tana
kallon titi, shima bai sake cewa kala ba har suka
shiga cikin gari.

Ya dube ta, wane shagon zamu?

Ta ce, duk wanda kaje, ni sanin wani saloon nayi?

Shagon wata mata ya kaita kusa da inda yake
aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar
Maiduguri.Shamsy belloRFIN CIKI novels / ZURFIN CIKI book 3 part 9
ZURFIN CIKI book 3 part 9
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 00:40
nayi?

Shagon wata mata ya kaita kusa da inda
yake aski, sun samu shagon Musulma ce 'yar
Maiduguri. 69....

Abba ya ce mata ga Amaryata a
gyara mata kai duk da ba wai gashi ne da ita ba
ya yi kyau sosai ko nawa ne zan biya.

Mai
shagon tayi 'yar dariya, zan mata yanda ka keso
ya dubi Ummi wadda ta samu kujera ta zauna
fuska daure.

Ya ce, "Kanwata zan tafi nayi aski
nima, daga nan sai na dauki matata daga unguwa
na kaita gida, sannan ta san in har ta bude baki
to kuka ne zai kwace mata, don haka sai ta yi
shiru.

Ya fita yana 'yar dariya, mai shagon
Yagana saloon ta ce, "Kai kanwata kun dace fa,
kuma da alamayana sonki sosai.Ta kalli mai
shagon hawayen da take makalewasuka zubo, ta
ce "Anty ina so a nan, dubi fa abinda yake
min.Komai sai ya ce min matarsa, matarsa, ko
inaruwana da matarsa?

Yagana ta ce, "Yana da
matane?

Sam bai yi kama da mai mata ba.Ummi
ta ta6a baki ta ce, "Yana da mata da yakeso ni
bana sonshi, baya sona, iyayenmu ne sukahada
mu.Yagana ta ce, in ma ke ba kya sonshi shi kam
yanadauke da tsantsar sonki a idanunshi n
fuskancihakan.

Ummi ta ce, "Anya kuwa?

Bana
zaton yanasona ne, in kin ce yabi iyayenmu ne
zan fi yardadon shi din mai biyayya ne.Yagana ta
tura mata kujera, zauna in soma miki,sai da ta
fara gyara mata kai sannan ta ce, "In mamijinki
ba ya sonki to kuwa ba za a yi wuyarshawo kai
ba.Ummi tayi murmushi tare da kallon fuskarta
tamadubin da suke fuskanta, ki ke gani Anty?

Ta
cesosai kuwa, ki tarairaye shi da kyau, kin san
shinamiji dai dan shauki ne da son nishadi.
(((KWARAI KUWWA!!!)))Ga kuma son tarairaya
kamar jaririn yaro, ummi tace, "To zan yi hakan in
har yin hakan zai sa ya soni.Yagana ta ce, "Zai
so ki, zan so kiyi gyaran jiki dafata, Umi ta ce,
kamar ya ya?

Yagana ta ce, kayanmata zuwa
gyaran fata, wanda za ki sha don 'karinni'ima.

Ummi tayi shiru, don bata son irin
wannanzantukan.Ta ce, "Kin yi shiru, Ummi ta ce
Ummana ta ce bata son in sha komai, tunda ni
budurwa ce, in je wamijina da ainihin halittata.In
yaso daga baya sanin saboda 'yan garinmu sunzo
da shi daga Zamfara.

Yagana ta ce, Hakan
mayana da kyau, domin Amare da yawa suna
shanwahala sosai kasancewar ba su saba
ba.Sannan mazajen ba su bambance ainihin
yandamatan suke.

Ummi cikin gundira ta ce, Gara
ma nagyara fatar.Yagana ta ce, "Wancan ma za
ki neme shi, ko nangaba Ummi ta ta6a baki, ni
dai fada min na gayarnfatar.Ta ce, "Ina sai dawa
in kina so zan baki kije gida kihada kiyi zan hada
ma angon lissafi da shi Ummita ce, ba ni sai da
suka gama a ka gyara matagashi fes, sannan ta
dauko kayan ta shiga lissafamata kamar haka:-1.

Man Zaitun2.

Lalle3.

Kurkur4.

Madara ta ruwaZa
ki hada su guri daya ki kwa6a, sannan ki
shafejikinki da su kafin shiga wanka, in ya bushe
idan zaki shiga wankan sai ki murje shi tas,
dukwadannan 'yan kurajen na fuskarki za su
mutu,jikinki ya yi laushi da sheki.Ga kuma wani.1.

Sabulun Ghana2.

Dettol3.

Zogale4.

Farar
AlbasaZa ki hada Sabulun Ghanada da Dettol da
garinzogale, da farar albasa, ki hada su ki kir6a
kimurmule shima a jikin za ki ringa shafawa.Da
fuska kafin ki shiga wanka, zan bar ki da biyunin
sun amshe ki ma sun ishe ki.

Yanzun ko inwanke
miki kafa? 39. 70....

Ummita ce, "Ina tsoron kada
yazo kuma kudin shi ba su kai ba, Yagana tayi
'yar dariya, kina tausayinsa ne?

Ki daina tausayin
mijinki shi ne zai amfana da gyaran da duk za ki
yi.

Ummi ta ce, "To wanke mini".Ta hada kayan
wankin kafa ta ce yarana ke yi amma zan miki da
kaina.

Sai kuma taga zanen fulawa.

Ta ce, "Au,
an riga an yi zanen fulawa ma ba dama ayi,
Ummi ta ce, Ohi ni na manta ma, to ki fada min
yanda zan dinga gyara kafar, ta ce To bari in ba
ki mai sauki ma. 1.

Man kwaka 2.

Man shanu 3.

Man Zaitun Ki samu man kwakwa da man shanu
da man zaitun ki hada man kwakwa da man
shanu guri daya, ki shafa da dare da safe.

Ki dan
gasa kafar sannan ki wanke ki shafa man zaitun,
za ki ga yanda kafafunki za su yi tamkar ta jariri.

Ko ki yi na ruwan ko kumba, lalle ki hada su guri
daya ki shafa a kafafunki da dare.

Da safe ki
wanke ki shafa man ridi, wadan nan kurum in kin
rike su za ki ba wani labari, Ummi tace zan
kiyaye in sha Allah.

Shi kuma Abba yana fitowa
daga shagon aski kai tsaye gidan Anty ya nufa,
ya samu Bishira Anty ta matsa mata tayi wanka
ta bata kaya ta saka.

Ta kira mai kitso tazo tayi
mata ta sata ta shafa turaruka.

Tunda Abba ya
shigo yake kallon Bishira, sun gaisa da Anty,
sannan ta ce dama dai na ce kazo ne don Bishira
ta baka hakuri.

Sannan in maka tuni da yin adalci
a tsakanin matanka, kuma na yi wa Bishira fada
sosai.

Ta dubi Bishira, ki ba shi hakuri, Bishira ta
hada rai tare da turo baki, ta kalle shi cike da
tsananin jin haushin shi.

Kayi hakuri ya ce ba
komai dama ni ban yi fushi dake ba, a zuciyarta
ta ce, ba ka isa in baka hakuriba, albarkacin ina
son zuwa Makka ne da kuma canjin kayan dakin.

Ya yi wa Anty godiya ta ce ma Bishira gobe da
wuri kiyi parking din duk kayan ki a waje da mun
zo sai mu shirya miki.
Chapter 26 · 0% Book details